11
Sep
Daga BELLO A. BABAJI Wata ambaliya da akayi a Kafanchan da wasu ƙauyuka da ke kusa da garin a ƙaramar hukumar Jema'a ta jihar Kaduna, ta yi sanadiyar rasa rayukan yara biyu tare da ɗaiɗaita mutane sama da 1,000. Mataimakiyar kantoman Jema'a, Christy Usman ta bayyana hakan wa kwamitin kula da ɓarnar ambaliya a kudancin jihar a lokacin da ya kai ziyarar gani-da-ido a ranar Litinin. Ta ruwaito cewa ambaliyar ta shafi cikin garin Kafanchan da gundumomin Jagindi, Atuku, Aso da Bade wacce ta kuma ɓarnata gonaki inda amfanin gona na miliyoyin kuɗi suka salwanta. Ta ƙara da cewa, gwamnan…
