Babaji

5715 Posts

DSS ta miƙa wuya ta saki Shugaban NLC bayan ta ƙwace masa fasfo

Daga BELLO A. BABAJI Hukumar DSS amsa buƙatar NLC ta sako shugabanta, Joe Ajaero. Ajaero, wanda aka sako shi wajen ƙarfe 12 na daren ranar Talata ya ce an sako shi ne kafin tsakiyar dare na ranar Litinin. Shugaban na NLC ya ce, jami'an sun sako shi bayan sun ƙwace masa fasfo ɗinsa. An kama Ajaero ne a jiya Litinin a lokacin da ya ke kan hanyar ficewa daga Nijeriya zuwa Landan a filin jiragen sama na Nnamdi Azikwe da ke Abuja. Hakan na zuwa ne bayan wani zama na gaggawa na rassan ƙungiyar ciki har da ma'aikatan wutar lantarki…
Read More

PDP ta soki Tinubu kan kama shugaban NLC

Daga BELLO A. BABAJI Jam'iyyar PDP ta soki Shugaba Bola Ahmed Tinubu saboda kama ƴan Nijeriya da jami'an tsaro suke yi. A yau Litinin ne jami'an hukumar ƴan sandan farin kaya, DSS suka kama shugaban Ƙungiyar Ƙwadago ta Ƙasa (NLC), Joe Ajaero a Filin jiragen sama na Nnamdi Azikwe da ke Abuja.. Sakataren yaɗa labarai na ƙasa a jam'iyyar, Debo Olugunagba ya ɗora wa Tinubu laifin kakkama mutane da aka yi, musamman la'akari da kama shugaban ƙwadago da aka yi a yau, ya na mai bada tabbacin cewa za su jira su ga abin da zai biyo bayan haka. A…
Read More

Joe Ajaero: Bayan zama na gaggawa, NLC ta bai wa gwamnati sharuɗa huɗu

Daga BELLO A. BABAJI Ƙungiyar Ƙwadago ta Ƙasa, NLC ta gudanar da wani zama na gaggawa sakamakon kama shugabanta, Joe Ajaero da jami'an hukumar DSS suka yi a yau Litinin, a filin jiragen sama na Nnamdi Azikwe da ke Abuja. Jami'an sun kama Ajaero ne akan hanyarsa ta ficewa daga Nijeriya zuwa Burtaniya don halartar taron Ƙungiyar Kasuwanci (TUC). A yayin zaman ne shugabannin NLC suka cimma ababe kamar haka; na farko, a gaggauta sako shugaban nata a yau da aka kama shi kafin karfe 12 na dare. Na biyu, a dawo da farashin litar man fetur zuwa N617 kamar…
Read More

Da Ɗumi-Ɗumi: Bayan rashin nasara a harin makaranta, ƴan bindiga sun yi garkuwa da malaman asibiti da marasa lafiya a Kaduna

Daga BELLO A. BABAJI Wasu da ake zargin ƴan bindiga ne sun kai hari a wani ƙaramin asibitin gwamnati (PHC) da ke Kuyallo a ƙaramar hukumar Birnin Gwari da ke jihar Kaduna inda suka yi garkuwa da malaman asibiti biyu da marasa lafiya da ba a tantance adadinsu ba. A lokacin haɗa rahoton, ba a samu wani jawabi daga rundunar ƴan sandan jihar ko jami'an gwamnati ba duk da ƙoƙarin neman Kakakin ƴan sanda, ASP Mansir Hassan da aka yi da sakonni da aka aika masa. Da misalin ƙarfe 9 na safiyar ranar Litinin ne suka kai hari a makarantar…
Read More

DSS ta kama shugaban NLC akan hanyarsa ta zuwa Burtaniya

Daga BELLO A. BABAJI Jami'an tsaro na hukumar ƴan sandan farin kaya ta DSS sun kama shugaban Ƙungiyar Ƙwadago ta Ƙasa, Joe Ajaero akan hanyarsa ta tafiya Burtaniya a ranar Litinin. Jaridar 'WikkiTimes' ta ruwaito cewa, jami'an sun kama shi ne a lokacin da ya nufi ficewa daga Nijeriya don halartar taron Ƙungiyar Kasuwanci (TUC) a filin jiragen sama na Nnamdi Azikwe da ke Abuja. A kwanakin baya ne rundunar ƴan sanda ta gayyaci Ajaero kan laifukan da ke da alaƙa da zanga-zangar tsadar rayuwa da aka yi a watan Agusta, inda gwamnatin tarayya ta zarge shi da hannu a…
Read More

Ba a yi adalci ba wajen raba kayan tallafi a Kano – Barau

Daga BELLO A. BABAJI Mataimakin shugaban Majalisar Dattijai, Sanata Barau Jibrin, ya ce Shugaba Tinubu bai gamsu da yadda aka bi ba a baya wajen rabon kayan tallafin ga mabuƙata a Nijeriya don rage raɗaɗin halin matsi da al'umma suka tsinci kansu a ƙasar. Ya ce, kasancewar haka ne ya sanya shugaban yanke shawarar samar da kwamitin kula da raba kayan tallafin don a tabbatar da cewa ya kai mabuƙatan. A lokacin da ya ke ƙaddamar da buɗe aikin raba tallafin gwamnatin tarayya na shiyyar Arewa-maso-Yamma a Kano ran Lahadi, Barau ya yi kira ga al'ummar Nijeriya su bai wa…
Read More

Zagon ƙasa: Kwamitin horarwa na PDP ya karɓi rahoto kan Wike, Ortom da Makinde

Daga BELLO A. BABAJI Kwamitin ladabdtarwa na Jam'iyyar PDP ya karɓi rahoton kwamitin aikace-aikace na ƙasa (NWC) game da zargin ayyukan zagon-ƙasa na Ministan Abuja, Nyesom Wike da wasu ƴan jam'iyyar. Kwamitin, wanda tsohon Ministan Ma'aikatar harkokin wajen, Tom Ikimi ke jagoranta, ya gayyaci Wike da wasu jiga-jigan jam'iyyar ne zuwa gaban jagororinsa kan zarginsu da yi wa PDP zagon-ƙasa a lokacin zaɓen 2023. Zargin ya mayar da hankali ne kan wasu gwamnonin PDP guda biyar waɗanda ake tuhumar su da yin zagon-ƙasa ga ɗan ƙarar shugaban ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar a jam'iyyar. Gwamnonin na wancan lokacin sune; Wike -…
Read More

SERAP ta bai wa Shugaba Tinubu kwana biyu ya sauya tashin farashin fetur

Daga BELLO A. BABAJI Ofishin tabbatar da ƴanci da adalci, SERAP ya yi kira ga Shugaba Bola Tinubu ya tsoma baki kan ƙara kuɗin man fetur da kamfanin man fetur na Ƙasa (NNPCL) ya yi, ya na mai nuna haramcin yin hakan da kuma bayyana shi a matsayin abu da aka yi ba bisa doka ba. Cikin wata buɗaɗɗiyar wasiƙa da ya fitar a ranar Asabar, SERAP ya nemi shugaban ƙasa ya umarci NNPCL ya gaggauta cire ƙarin da ya yi akan farashin da ya ke a baya, kuma ya ɗauki matakin binciken rashawa a kamfanin. SERAP ya nemi Antoni…
Read More

Gwamnan Kano ya dakatar da buɗe makarantun jihar

Daga BELLO A. BABAJI Gwamnatin jihar Kano ta dakatar da komawa makaranta ga daliban makarantun firamare da sekandire na zangon 2024/2025 bisa wasu dalilai da ba ta bayyana ba. Daraktan wayar da kan al'umma na ma'aikatar Ilimi ta jihar, Balarabe Ƙiru ya faɗi hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar. Ya ce, Kwamishinan Ma'aikatar, Umar Doguwa ya bayyana cewa hukuncin ya biyo bayan matsaloli ne da ake ƙoƙarin warware su da za su taimaka wajen inganta harkar ilimi a jihar. A ranakun 8 da 9 ga watan Satumba ne aka shirya komawa makarantu don cigaba da karatu…
Read More

Tinubu ya martaba ɗalibai 462 da aka yaye a makarantar kwalejin horo ta ƴan sanda

Daga BELLO A. BABAJI Shugaban ƙasa kuma Kwamandan rundunar tsaro, Bola Ahmed Tinubu GCFR ya tabbatar da yaye ɗalibai 462 daga makarantar kwalejin horo ta ƴan sanda da ke Wudil a Jihar Kano zuwa sahun rundunar ƴan sandan Nijeriya. Bayan kammala shekaru biyar a makarantar su na karɓar horon karatu da na aikin ƴan sanda, an bai wa kowannen su muƙamin Mataimakin Sufuritandan ƴan sanda (ASPs). Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar ƴan sanda, Olumuyiwa Adejobi ya ce an gudanar da bikin yaye ɗaliban ne a filin fareti na makarantar inda masu alfarma daga ɓangarori daban-daban a Nijeriya suka halarta.…
Read More