Babaji

5715 Posts

Karɓar horon NYSC: JAMB ta buƙaci ɗaliban HND su kai kokensu ga hukumomin da suka dace

Daga BELLO A. BABAJI Hukumar Haɗaka ta bada Gurbin Karatu ga ɗalibai, JAMB ta shawarci ƙungiyar ɗaliban makarantun Polytechnics (NAPS), cewa ɗaliban HND da ba a tantace su ba ga tafiya hidimar ƙasa ta NYSC, su kai kokensu ga hukumomin da suka dace. A lokacin da ya ke ganawa da shugaban NAPS a hedikwatar hukumar da ke Abuja, Rijistiran JAMB, Farfesa Ishaq Oloyede ya bayyana cewa, kamar yadda JAMB ba ita ke da alhakin bai wa ɗaliban HND gurbin karatu ba, haka kuma ba ita ce mai tantance su ba. Farfesan ya yi mamakin yadda ƙungiyar ta tunkare su da…
Read More

Ayyukan ƴan ta’adda na da alaƙa da watsi da aka yi da su – Sheikh Gumi

Daga BELLO A. BABAJI Malamin addinin Islama, Sheikh Ahmad Gumi ya ƙaryata iƙirarin da ake yi na cewa ƴan siyasa ke ɗaukar nauyin ayyukan ta'addanci a Arewacin Nijeriya. Gumi wanda sananne ne akan sharhin ayyukan ta'addanci da ke cigaba da ta'azzara a shiyyar, ya ce tashin-tashinar yankin ta na da alaƙa da watsi da aka yi da waɗansu mutane na tsawon lokaci a madadin siyasantar da al'amarin. Sanannen abu ne a ƴan shekarun nan, yankin Arewa-maso-Gabashin Nijeriya na fama da matsalolin ta'addancin kashe-kashe da yin garkuwa da mutane ciki har da kisan Sarkin Gobir na jihar Sakkwato da aka yi…
Read More

Majalisar Shari’a ta amince ta bai wa masu zanga-zangar da aka tsare kariya

Daga BELLO A. BABAJI Darakta-Janar na Majalisar Shari'a ta Ƙasa, Aliyu Abubakar, ya tabbatar ta ƙoƙarin da su ke yi wajen bada wakilci na Shari'a ga masu zanga-zangar tsadar rayuwa da aka tsare ba tare da wani ɗauki a hukumance ba. Cikin wata hira da ƴan jarida, Abubakar ya ce kawo yanzu majalisar ba ta tuntuɓi wasu mutane ko wata kotu ba game da wakiltar ɗaya daga cikin waɗanda aka tsaren yayin da ake cigaba da gudanar da shari'ar. A ranar 1 zuwa 10 ga watan Agusta ne aka gudanar da zanga-zangar kan halin matsin rayuwa da al'umma ke ciki…
Read More

Zamfara: Bello Turji ya rage harajin da ya sanya wa Moriki zuwa miliyan N30

Daga BELLO A. BABAJI Shahararren ɗan jaridar nan, Bulama Bukarti ya wallafa a shafinsa na X cewa an ƙulla yarjejeniya tsakanin sanannen shugaban ƴan ta'addar nan, Bello Turji da al'ummar yankin Moriki da ke jihar Zamfara. An shirya yarjejeniyar ce wadda ta ƙunshi kuɗi da za a biya kan dabbobin Turji da aka kashe. Acikin jawabin, Turji ya buƙaci Naira miliyan 50 ne da farko wanda daga baya ya rage adadin kuɗin zuwan miliyan N30. A ƙarƙashin haka, kowane magidanci zai biya N10,000 yayin da samarin da basu da aure za su biya Naira dubu biyu-biyu. Ya ce, mutanen Moriki…
Read More

Gwamnan Zamfara ya ƙaddamar da aikin babban asibiti mai ɗaukar gadoji 200 a Talata Mafara

Daga BELLO A. BABAJI Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya jaddada aniyar gwamnatinsa na zuba ayyuka a harkokin kiwon lafiya a jihar ganin yadda manyan asibitoci ke taka rawar gani a ɓangaren. A ranar Asabar ne gwamanan ya ƙaddamar da sake ginawa da kuma zuba kayan aiki na babban asibiti a ƙaramar hukumar Talata Mafara wanda zai ɗauki aƙalla gadojin marasa lafiya 200. Wata takarda da Kakakin gwamanan, Sulaiman Bala Idris ya fitar ta ce, tsohon gwamnan tsohuwar Jihar Sakkwato, Malam Yahaya Abdulkarim shi ne babban baƙo na musamman a taron. A lokacin da ya ke jawabi, gwamana Lawal ya…
Read More

Ainihin dalilan da suka sanya Ngelale yin murabus daga muƙamin kakakin Tinubu

Daga BELLO A. BABAJI Wasu sabbin bayanai sun bayyana game da dalilan da suka sanya mai taimaka wa shugaba Tinubu na musamman kan harkokin yaɗa labarai, Ajuri Ngelale ya yi murabus daga aikinsa. A ranar Asabar ne Ngelale ya sanar cewa, ya ɗauki hutu mara iyaka don matsalolin kiwon lafiya da ya shafi ahalinsa. Ya bayyana haka ne kwana ɗaya bayan miƙa wata takarda ga ofishin shugaban ma'aikata na Fadar shugaban ƙasa kan cewa ya sanar da shugaban ƙasa batun ajiye aikin nasa. Bayan fakewa da matsalolin kiwon lafiya a matsayin dalilinsa na tafiya hutu mara iyaka, wata majiya ta…
Read More

Ina maka fatan alkhairi kan ajiye aikinka – Shugaba Tinubu ga Ngelale

Daga BELLO A. BABAJI Ofishin shugaban ƙasa ya ce ya samu saƙo daga mai magana da yawun Shugaba Bola Tinubu, Ajuri Ngelale cewa zai ajiye aikinsa saboda dalilai na kai-da-kai da kuma matsala ta kiwon lafiya. An samu sanarwar ne ta shafin ofishin na X inda ta ce an karɓi uzurin Ngelale na tafiya hutu daga aikinsa. "Shugaban ƙasa ya amince da dalilansa na tafiya hutu, ya fahimce su kuma ya tausaya game da matsin da suka kai ga yanke wannan hukunci mai tsauri", inji sanarwar. Ofishin, ya kuma yaba wa ƙoƙarinsa na sadaukarwa wajen hidimta wa ƙasa da kuma…
Read More

Yadda mahaifiyar Yar’Adua ta mayar da ni abin da na zama a yau – Jonathan

Daga BELLO A. BABAJI Tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Ebele Jonathan ya bayyana takaicinsa game da rasuwar Hajiya Dada Yar'Adua, Mahaifiyar Tsohon shugaban ƙasa, Umaru Musa Yar'Adua inda ya ce ta yi tasiri sosai ga nasarorin da ya samu a rayuwarsa. Jonathan ya faɗi haka ne a lokacin da ya kai ziyarar ta'aziyyar rasuwar Hajiyar ga iyalanta a Katsina, a ranar Asabar da ta gabata. Ya ce, "mutuwarta ta matuƙar sosa mun rai. Ɗanta ne ya ɗakko ni a matsayin abokin tafiyarsa wanda ba don ita ba, da yau ba ku san sunana ba." Tsohon shugaban ƙasar ya bayyana cewa, ta…
Read More

An kama ɗan shekara 60 kan satar wayar lantarki a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Rundunar tsaro ta al'umma (Civil Defence), ta yi nasarar kama tsoho ɗan shekara 60 kan satar wayar wutar lantarki a ƙaramar hukumar Funtua da ke jihar Katsina. Jami'in yaɗa labarai na rundunar, DSC Buhari Hamisu ya bayyana sunan ɓarawon mai sun Hassan Abubakar da ke zaune a ƙauyen Lasanawa a garin Maska da ke ƙaramar hukumar. DSC Buhari ya ce, Hassan ya zo hannun jami'an tsaro ne bayan an kama shi da tsinkakkun wayoyin lantarki ya na ƙoƙarin kai wa masu cinikin kayan nauyi a garin Funtua. "Cikin dare ya hau sandar wayar wutar lantarkin…
Read More

Gina famfunan tuƙa-tuƙa a Sakkwato kan Naira biliyan 1.2: Tsakanin sani da rashin sani

Daga ALƘALAMIN MARUBUCIYA - BILKISU YUSUF ALI KANO A kwanakin baya, gwamnan Jihar Sakkwato, Alhaji Dakta Ahmad Aliyu ya yi wata magana kan haƙa rijiyar 'borehole' wanda akan adadin kuɗin da ya faɗa, sai aka yi masa ca, aka fara yaɗa farfaganda har abin ya zama abin zolaya ga waɗanda suka jahilci mai gwamna yake nufi da abin da gwamna zai yi. Faɗin za a yi borehole ya sa masu ƙaramin sani suka ɗauka borehole ce irin wanda aka saba yi a gidana da gidanka. Injiniyoyin kirki da yake sana’arsu ce haƙa borehole, ka ji sun yi magana? To ba…
Read More