Babaji

5715 Posts

Jonathan ya je ziyarar ta’aziyyar mahaifiyar tsohon shugaban ƙasa Yar’adua

Daga Umar Garba a Katsina Tsohon shugaban Najeriya, Dakta Goodluck Ebele Jonathan, ya kai ziyarar ta'aziyyar rasuwar Hajiya Dada Musa Yar'adua. Gwamnan jihar Katsina, Mallam Dikko Umar Raɗɗa ne ya tarbi Jonathan a filin sauka da tashin jiragen sama na Mallam Umaru Musa Yar'adua da ke Katsina, a ranar Asabar. Jonathan ya kasance mataimakin marigayi shugaba Yar'adua daga shekarar 2007 zuwa 2010. Daga bisani ya zama shugaban ƙasa a Najeriya na goma 14, a ranar 5 ga watan Mayu na shekarar 2010 bayan rasuwar Umaru Musa Yar'adua.
Read More

NNPCL ya mayar da martani bisa kalaman MURIC kan farashin fetur

Daga BELLO A BABAJI Kamfanin man fetur na Ƙasa, NNPCL ya yi tsokaci game da takardar da Ƙungiyar kare Ƴancin al'ummar Musulmi (MURIC) ta fitar inda ta ce matatar man fetur ta Ɗangote na fuskantar barazana game da burinta na samar da mai a farashi mai sauƙi ga al'umma. MURIC ta tabbatar da cewa, ƙarin farashin mai da NNPCL ya yi a kwanan nan zai hana Matatar Kamfanin Ɗangote (DRL) bada man fetur a farashi mai sauƙi ga ƴan Nijeriya wanda an gina shi ne domin su amfana, wanda ta ce NNPCL ya mamaye baki ɗaya hajojin matatar. Sai dai,…
Read More

An ƙaddamar da kwamitin zakka da waƙafi a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Gwamna Dikko Raɗɗa ya ƙaddamar da kwamitin Zakka da waƙafi na gundumomi da na ƙananan hukumomi 34 da ke jihar. Ya ce, aikin kwamitin shine tattarawa da raba Zakka da waƙafi kaɗai da ya bayyana ga masu biya a matsayin hanya tabbatacciya ta samun rahamar Allah da shawo kan matsalolin rayuwa. Acewarsa, ƴan kwamitin sun haɗa da hakimin gunduma da daraktan ilimi da walwalan jama'a a matsayin shugaba da sakatare na kwamitin. Sauran mambobin sun haɗa da wakilai daga majalisar dokoki, ƴan kasuwa, manoma da ƙungiyoyin Izala da Ɗariƙa a kowacce gunduma. Gwamnan ya jaddada…
Read More

Gwamnatin Katsina za ta kafa kwamitin ci gaban al’umma

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Gwamnatin jihar Katsina za ta kafa kwamitin ci gaban al'umma a kowacce ƙaramar hukumar da ke jihar. Gwamna Dikko Raɗɗa ya sanar da haka a wajen taron tattaunawa da alummomin shiyyar Katsina ya ce, nan bada jimawa ba za a aika da ƙudirin wa majalisar dokoki ta jihar domin ta amince ya zama doka. Ya ce, manufar kafa wannan kwamiti shine bai wa al'umma dama su yanke wa kansu abinda suke buƙata gwamnati ta yi masu. Haka kuma, kwamitin zai sa ido akan aikace-aikace na gwamnatin jihar a yankunansu domin tabbatar da ingancin aikin. Malam…
Read More

Tsadar man fetur ya tsananta ayyukanmu – Ƙungiyar Masana’antu

Daga BELLO A. BABAJI Shugaban Ƙungiyar Masana'antu ta Nijeriya (MAN) reshen Kudu-maso-Yamma, Mista Lanre Popoola ya ce ayyukan masana'antu sun tsananta sakamakon ƙarin kuɗin man fetur da aka yi kwanan nan. Ya faɗi hakan ne a yayin zantawa da jaridar 'News Agency Nigeria' a Ibadan, babban birnin jihar Oyo inda ya bayyana yadda tsananin da aka shiga a matsayin dalili na rashin gudanar da ayyukan masana'antun yadda aka saba sakamakon koma baya da hakan ya haifar. Ya ce, tun kafin ƙarin farashin man fetur a Nijeriya, MAN ke fuskantar tsanani wajen amsa buƙatun kwastomominsu. Ya kuma ce, a halin tsaka-mai-wuya…
Read More

Akwai buƙatar ƙarfafa haɗin-gwiwa tsakanin sarakuna da gwamnati wajen daƙile matsalolin ƙasa – Shettima

Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya yi kira da a ƙara ƙarfafa dangantaka tsakanin gwamnatin tarayya da Masarautun gargajiya. Shettima ya yaba da rawar da suke takawa wajen wanzar da haɗin-kan ƙasa da zaman lafiyar al’umma. Mataimakin ya bayyana hakan ne a wajen ta'aziyyar da ya kai masarautar Ningi da ke jihar Bauchi, bisa rasuwar marigayi Sarkin Ningi, Alhaji Yunusa Ɗanyaya. Ya kuma taya sabon sarkin da aka naɗa murna tare da yi masa alƙawarin ba shi goyon bayan gwamnatin tarayya. Ya ƙara da jaddada muhimmancin cigaba da shugabancin sarakunan gargajiya ga haɗin-kan ƙasa.
Read More

Gwamnati ta karya farashin shinkafa sama da buhu miliyan uku akan N40,000 kowane kg50

Gwamnatin tarayya ta ƙaddamar da sayar da tan 30,000 na shinkafa akan farashin kuɗi Naira 40,000 babban buhu domin rage matsalar hauhawar farashin abinci a Najeriya. Shirin, wanda shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ke jagoranta na da nufin samar da abinci mai sauƙi ga ƴan ƙasa. Za a sayar da shinkafar kan karyayyen farashin a duk faɗin ƙasar ƙarƙashin tsauraran matakan da za su tabbatar da an bi dokokin da suka dace wajen hana Shinkafar shiga hannayen ƴan kasuwa masu tsauwala farashi da gangan.
Read More

Tsadar fetur: Sai an yi haƙuri an jure matakan da muke ɗauka – Tinubu

Daga BELLO A. BABAJI Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya magantu kan ƙarin farashin man fetur inda ya gabatar da jawabi wa ƴan Nijeriya alhali ya na ƙasar Chana. Tinubu ya ce hakan da ma wasu gyare-gyare da gwamnatinsa ke yi na daga cikin salon haɓaka tattalin arziƙin Nijeriya, ya na mai cewa su na bin hanyoyin da suka dace wajen cimma hakan. Mai magana da yawunsa, Ajuri Ngelale ya hakaito inda shugaban ƙasar ya ke cewa, "mene ne ɓangaren ƙamarin da zai kai mu wajen, idan ba za mu iya jure wa tsauraran matakan da za su buɗe hanya wa…
Read More

Masu katin ɗan ƙasa kaɗai za a sayar wa buhun shinkafa N40,000 – Gwamnatin Tarayya

Daga BELLO A. BABAJI Gwamnatin Tarayya ta ce Ma'aikata masu katin shaidar ɗan ƙasa ne kaɗai za su amfana yayin da ta shirya fara sayar da ton 30,000 na shinkafa. Ministan Albarkatun Noma, Abubakar Kyari a lokacin ƙaddamar da tsarin ya ce an yi haka ne don a toshe ƙofar yin ha'inci ga masu saya da kuma taimakawa wajen rage farashin kayan abinci a Nijeriya. Kyari, wanda ya wakilci Shugaba Tinubu, ya ce kowane ma'aikaci damar sayan buhu ɗaya kadai aka ba shi. Sannan, za a sayer da kowane buhu ɗaya mai nauyin 50kg akan N40,000 kamar yadda aka sanar…
Read More