19
Jul
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Hukumar gyaran hali ta ƙasa (NCoS), ta fitar da hotuna da sunaye da sauran bayanan waɗansu mutane da su ka tsere daga kurkukun Suleja, reshen Abuja, sakamakon ruftawar ginin da su ke ciki bayan wani mamakon ruwan sama da aka yi a ranar Laraba, 24 ga watan Afrilu, 2024. Wata sanarwa da jami'in hulɗa da jama'a na hukumar, Abubakar Umar ya fitar a ranar Alhamis, ta ce matakin yana da muhimmanci wajen sake kamo su tare da mayar da su komar hukumar. Ya ce, sun miƙa bayanan waɗanda suka tseren ga sauran hukumomin tsaro da kuma…
