21
Jul
Daga SANI AHMAD GIWA Shugaban gamayyar ƙungiyoyin Arewa (CNG), Kwamared Jamilu Aliyu Charanci, ya yi kira ga gwamnatin Nijeriya da Shugaba Bola Ahmed Tinubu da su tashi tsaye su yi duk mai yiwuwa domin hana abin da ke shirin faruwa a ƙasar. Kwamared Aliyu ya bayyana hakan ne yayin wani taron manema labarai da ƙungiyar ta kira a cikin makon nan, a lokacin da ake tsaka da batun gudanar da zanga-zanga a faɗin ƙasar kan tsadar rayuwa da taɓarɓarewar harkar tsaro da ake fama da su musamman a Arewacin ƙasar. Shugaban ƙungiyar ya ce, sanin kowa ne al'umma tana cikin…
