Babaji

5681 Posts

Da ƊUMI-ƊUMI: DSS ta sako matasan da ta kama kan shirin zanga-zanga

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Ƴan sandan farin kaya ta DSS, ta sako Injiniya Khalid Aminu da Sanusi Aliyu waɗanda ta kama su a kwanakin baya kan zargin zanga-zangar tsadar rayuwa da aka yi wa laƙabi da 'EndBadGovernance'. Sanarwar haka ta fito daga Omoyele Sowere, ɗan takarar shugaban ƙasa na Jam'iyyar AAC a zaɓen 2023 a wani rubutu da ya yi a kafar sadarwa. An kama Khalid ne a safiyar ranar Alhamis don zargin gayyato mutane shiga zanga-zangar gama-garin a jihar Kaduna, yayin da a irin haka aka kama Sanusi a ranar Talata a jihar Sakkwato, 23 ga watan Yuli. Rahotanni…
Read More

Zanga-zanga: Masu amfani da wayoyi da motoci ake hari, DHQ ta gargaɗi al’umma

Daga BALA MUHAMMAD Hedkwatar tsaro ta ƙasa (DHQ), ta ce ta gano wani shiri da wasu ɓata-gari ke yi na kai hari wa masu motoci da masu amfani da manyan wayoyi da kuma mallakar wasu kadarori a cigaba da shirye-shiryen gudanar da zanga-zangar 'EndBadGovernance' a za a yi wata mai zuwa. A ranar Alhamis ne, Daraktan ofishin kan harkokin yaɗa labarai, Manjo Janar Edwerd Buba ya faɗi haka a yayin ganawa da manema labarai a Abuja inda ya ce sun gano akwai maƙarƙashiya da ka iya haifar da tarzoma a lokacin zanga-zangar, yana mai cewa mutane da dama na goyon…
Read More

Ajaero ya bayyana matsayar NLC kan zanga-zangar tsadar rayuwa

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa (NLC), ta musanta batun cewa ta janye daga zanga-zangar tsadar rayuwa da ake shirin yi faɗin Nijeriya, ta na mai cewa ba ta ɗaya daga cikin waɗanda su ka shirya ta. Shugaban ƙungiyar, Joe Ajaero ya bayyana haka cikin wata takarda da ƙungiyar ta fitar a ranar Talata, inda ya ce ba za su janye daga zanga-zangar da ba su suka tada batunta ba. Ya ce ƙungiyar tana da tsarinta na cikin gida game da yin hukunci kan ababan da su ka shafi al'umma cikin har da zanga-zanga. Ya ƙara da cewa…
Read More

Shugaban ƙasar Gabon ya gayyaci Ɗangote don sanya hannun jari a siminti da taki

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Shugaba Brice Oligui Nguema na ƙasar Gabon ya gayyato shugaban kamfanin Ɗangote, Alhaji Aliko Ɗangote zuwa ƙasarsa domin ƙulla harkar kasuwanci a ɓangarorin siminti da taki musamman domin haɓaka harkar noma. A lokacin ziyarar, Ɗangote ya gana da Shugaba Nguema da wasu manyan jami'an gwamnati inda su ka tattauna kan batutuwan sanya hannun-jari. A zaman, an mayar da hankali ne kan yadda masana'antun Ɗangote zasu taimaka wajen haɓaka tattalin arziƙin Gabon ta hanyar samar da masana'antun siminti da taki musamman a ɓangaren samar da albarkatun noma. Nguema ya bayyana jin daɗinsa game da haɗa hannu da…
Read More

An samu tsaiko a shari’ar Kwankwaso kan EFCC

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Sakamakon rashin cike ƙa'idojin babbar kotun jihar Kano da hukumar hana yi wa tattalin arziƙi zagon ƙasa, EFCC ta yi, an samu tsaiko kan sauraron ƙarar da aka shigar kan kare ƴancin shugaban jam'iyyar NNPP, Rabi'u Musa Kwankwaso da wasu mutum bakwai. Jaridar 'Daily Trust' ta ruwaito cewa, waɗanda su ka shigar da ƙarar sun haɗa da; NNPP, Dakta Ajuji Ahmed, Dipo Olayanku, Ahmed Balewa, Cif Clement Anele, Ledi Folshade Aliu, Buba Galadima da kuma Rabi'u Musa Kwankwaso kan hukumar EFCC. A yayin da aka tada batun, lauyan da ya karɓi shigar da ƙarar, Robert Hon,…
Read More

DSS ta sake kama wani matashi kan shirya zanga-zanga a Sakkwato

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Rundunar Ƴan sandan farin kaya ta DSS, ta yi nasarar kama wani matashin Nijeriya mai suna Aliyu Sanusi kan shirya zanga-zangar da ke ƙalubalantar raunin shugabanci a faɗin ƙasar. An kama matashin ne a yammacin ranar Litinin, a hanyar Sama da ke Sakkwato, babban birnin jihar. Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar AAC, Omoyele Sowere ya bayyana hakan a shafinsa na X, a ranar Talata inda ya buƙaci hukumar ta gaggauta sako matashin, yana mai cewa hakan ya saɓa wa doka. Lamarin ya auku ne bayan da DSS ta sako wani matashin mai suna Bashir…
Read More

Rundunar ‘Yan sanda ta roƙi mazauna Abuja kar su shiga zanga-zanga kan tsadar rayuwa

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Kwamishinan 'Yan sandan birnin tarayya, Abuja, Bennet Igweh ya roƙi al'ummar jihar kar su shiga zanga-zangar da aka shirya za a yi a watan Agusta kan tsadar rayuwa a faɗin Nijeriya. Igweh ya nuna damuwarsa kasancewar ɓata gari ka iya amfani da zanga-zangar wajen tarwatsa sabbin ayyukan cigaba da a ka yi a faɗin jihar. Kwamishinan, ya bayyana hakan ne a yayin hira da manema labarai a ranar Litinin a lokacin da rundunar ta gurfanar da mutane da dama kan zargin fashi a hedkwatar ofisoshinta da ke birnin. Ya ce, suna aiki tuƙuru wajen kamo ƴan…
Read More

‘Yan sandan Kano sun kama fursunan da ya tsere daga kurkukun Kuje, wanda ya kitsa kashe janar na soja

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Rundunar 'Yan sanda ta yi nasarar kama wanda aka zarge shi da kitsa kisan marigayi Burgediya Janar Harold Udokwere, mai suna Hashiru Baku wanda yana ɗaya daga cikin waɗanda suka tsere daga kurkukun Kuje a kwanakin baya. Jaridar 'News Point Nigeria' ta ruwaito yadda ƴan bindiga suka shiga gidan janar Harold tare da kashe shi a unguwar rukunin gidajen Sunshine da ke Abuja a ranar 21 ga watan Yuni, inda Ƴan sanda ƙarƙashin kwamishinan rundunar Abuja, Bennet Igweh su ka kama waɗanda ake zargi kwana biyu bayan aukuwar lamarin. A lokacin da aka gurfanar da ƴan…
Read More

ASUU ta janye yajin aikin Jami’ar Abuja da aka ɗauki kwanaki 82 ana yi

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Jami'ar Abuja ɓangaren ƙungiyar malaman jami'o'i ta sanar da dakatar da yajin aikin da aka ɗauki tsawon kwanaki 82 ana yi inda ta ce nan da nan za a dawo bakin aiki. Shugaban ƙungiyar, Dakta Sylvanus Ugo ya faɗi haka a yayin ganawa da manema labarai bayan kammala wani zama na ƙungiyar a Abuja inda ASUU tare da majalisar zartarwar Jami'ar su ka tattauna yayin da majalisar ta yi alƙawarin yin duba ga buƙatunsu tare da samar musu da mafita a kan su. A ranar biyu ga watan Mayu, 2024 ne aka shiga yajin aikin sakamakon…
Read More

Gwamnatin Tarayya ta jagoranci ganawa kan taƙaddamar matatar Ɗangote da NMDPRA

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Gwamnatin Tarayya ta shiga tattaunawa kan taƙaddamar da ke tsakanin hukumar man fetur ta NMDPRA da sabon matatar Ɗangote wanda ƙaramin ministan albarkatun man fetur, Heineken Lokpobiri ya jagoranta wanda Alhaji Aliko Ɗangote da shugabannin NMDPRA suka halarta. An shirya zaman ne da nufin wanzar da haɗin kan ɓangarorin biyu da kuma warware ɓoyayyun matsalolin da ka iya shafar ayyukan matatar wanda ake tsammanin hakan zai taimaka wajen kawo ƙarshen dogaro da dangogin mai daga ƙasashen waje da Nijeriya ke yi. Wata takarda da mai bai wa ƙaramin ministan shawara kan yaɗa labaru, Nneamaka Okafor, ya…
Read More