07
Jul
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal ya aika saƙon fatan alkhairi ga al'ummar Musulmin jihar bayan shiga shekarar Hijira ta fiyayyen halitta, Annabi Muhammad (SAW), 1446. Gwamnan, ya yi kira ga al'ummar Musulmi a jihar da ma Nijeriya baki ɗaya da su cigaba da yi wa ƙasa addu'a domin samun zaman lafiya a dukkan sassan da ake fama da matsalolin tsaro. Wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Sulaiman Bala Idris ya fitar, ta ce sabuwar shekarar Musuluncin lokaci ne na yin nazari ga abubuwan da suka faru a shekarar da ta gabata. Yau Lahadi ce ranar…
