Babaji

5684 Posts

‘Ofishin Made in Nigeria halastacce ne’, inji Nwabueze yayin musanta zargin haramcinsa, ya fitar da shaidar bada aiki

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Kodineta na Ƙasa kuma Babban Daraktan 'Ofishin National Brands Development and Made in Nigeria Special Project' da ake taƙaddama a kai, George Nwabueze, ya musanta zargin cewa yana gudanar da "hukumar bogi" a Nijeriya. Nwabueze ya bayyana haka ne ga manema labarai a ranar Asabar, inda ya ce ya jagoranci wani ofishi da ke gudana a ƙarƙashin sanya idon Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya (OSGF). Ya ce, ofishin yana aiki tun sawon shekaru 16 baya. A ranar Juma'a ne Hukumar Yaƙi da Rashawa (ICPC) ta ce Shugaba Bola Tinubu ya umarci a kama Nwabueze bisa…
Read More

Ƙungiyar kansilolin APC ta taya Yari da Ganduje murnar samun shugabanci a kwamitin yaƙin neman zaɓen Tinubu na 2027

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ƙungiyar Kansilolin Jam'iyyar APC ta Ƙasa (NPSCF) ta fitar da saƙonta na taya murnar ga Sanata Abdulaziz Yari Abubakar kuma Gwamnan Jihar Zamfara bisa naɗa shi a matsayin darakta-janar na kwamitin yaƙin neman zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaɓen 2027 ƙarƙashin jam'iyyar APC. A wata sanarwa da ke ɗauke da sanya hannun Shugabanta na ƙasa, Hon. Muslihu Yusuf Ali da ya fita a Abuja, ranar Asabar, NPSCF ta kuma taya wanda ta naɗa a matsayin Uban Ƙungiya, tsohon shugaban APC na ƙasa kuma tsohon gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje murna bisa…
Read More

Wike zai wallafa ayyukan da ya gada daga gwamnatocin baya

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ministan Abuja Nyesom Wike, ya sanar da shirinsa na wallafa bayanan ayyukan da ya gada daga gwamnatocin da aka yi a baya da kuma na ayyukan da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta bai wa gwamnatinsa. Wike ya bayyana haka ne a ranar Asabar bayan kai ziyarar sanya ido a wasu titina biyu a Abuja, inda ya bayyana gamsuwarsa a kai da kuma ƙwarin aikin da 'yan kwangilar suke yi. Ya ce, takardun bayanan za su ƙunshi ayyukan da gwamnatinsu ta gada daga na tsofaffin shugabannin ƙasa da suka haɗa da, Olusegun Obasanjo, Umaru Musa…
Read More

Abin da ya sa ba zan zama daraktan yaƙin neman zaɓen APC ba – Wike

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ministan Abuja Nyesom Wike, ya bayyana dalilin da ya sa ba zai karɓi muƙamin Darakta-Janar na kwamitin yaƙin neman zaɓen jam'iyyar APC ba domin zaɓen 2027 duk da goyon bayansa ga Shugaba Tinubu. Wike ya bayyana haka ne a ranar Asabar bayan wata ziyarar sanya ido da ya kai a wuraren wasu ayyukan titi guda biyu a Abuja, inda ya bayyana gamsuwa da salo da ƙwarin aikin 'yan kwangilar. Ya ce, matakin nasa na da alaƙa da darussa da ya samu daga zaɓukan baya, inda ya ce da dama daga cikin waɗanda suka riƙe…
Read More

Matafiya sun shiga mawuyacin hali yayin da manyan motoci da aikin titi suka haifar da cinkoso a hanyar Kaduna zuwa Abuja

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A safiyar ranar Asabar ne matafiya akan hanyar Abuja zuwa Kaduna suka haɗu da tsaiko a sakamakon wani cinkoson ababen hawa a yankin Kateri, lamarin da ya jefa su cikin halin rashin tabbas game da makomar zirga-zirgarsu. Wakilin Blueprint.ng da ke wajen ya ruwaito cewa, cinkoson ya shafi masu zirga-zirga na ɓangarorin titin guda biyu, inda aka ga wani dogon layi na jerin gwanon motoci a yankunan babbar hanyar. Ya bayyana cewa, halin ya fi zama matsi ga masu zuwa Jere da Abuja inda haɗakar aikin gina titi da yawaitar manyan motoci suka haifar…
Read More

2027: Yari ya yi jawabi karon farko a matsayin darakta-janar na yaƙin neman zaɓen Tinubu

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Bayan da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kafa kwamitin yaƙin neman zaɓensa a babban zaɓen 2027, Darakta-Janar na tafiyarsa a jam'iyyar APC, Sanata Abdulaziz Yari Abubakar, ya karɓi muƙamin a hukumance inda ya ci alwashin sauke nauyin da aka ɗora bisa jajircewa da ladabi wajen kai su ga nasara a 2027. An zaɓi Yari, wanda shi ke wakiltar Zamfara ta Yamma a Majalisar Dattawan Nijeriya kuma tsohon Gwamnan Jihar Zamfara ne a matsayin Darakta Janar na yaƙin neman zaɓen Tinubu a ranar Asabar, 22 ga Agusta. A wata sanarwa da sanatan ya fitar a…
Read More

Yadda hukumar bogi ta gina tsarin gudanarwa a jihohi 20 da ofisoshi a Amurka da Chana

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja 'National Brands Development and Made in Special Project Offic', wadda aka zarga da "hukumar bogi", ta kasance ta faɗaɗa tsarin gudanarwarta a jihohin Nijeriya 20 da wasu manyan ƙasashe guda biyu gami da samar da kodineta ja ƙasa, daraktocin shiyyoyi, kodentocin jihohi da wakilai a Amurka da Chana, kamar yadda binciken jaridar NewsPointNigeria ya nuna. A wani bincike da aka gudanar a shafinta na intanet a ranar Asabar, 22 ga Agusta, 2026, an gano cewa Hon. Nwabueze George shi ne shugabanta kuma kodineta na ƙasa tare da daraktan gudanarwa na ƙasa, daraktocin shiyyoyi uku,…
Read More

Babban Limamin masallacin Anas Bin Malik Islamic Centre ta Abuja ya rasu

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A safiyar yau Asabar ne Dakta Ibrahim Mohammed Fadul da aka fi sani da Imam Abuya ya rasu. Marigayin, wanda shi ne babban Limamin Masallacin Cibiyar Anas Bin Malik Islamic da ke yankin rukunin gidajen AMSSCO Platinum City a Galadimawa, ya rasu ne a Abuja bayan fama da wani rashin lafiya. An kuma shirya gudanar da jana'izarsa da misalin ƙarfe 1:30 na rana a Babban Masallacin Ƙasa da ke yankin Central Area a babban birnin. Allah SWT ya jiƙansa ya kuma gafarta masa kurakuransa tare da bai wa makusantansa haƙurin juriya ga rashinsa.
Read More

‘Yan bindiga sun sace masu ibada bayan sallar Juma’a a ƙauyukan Neja

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja 'Yan bindiga sun yi awon-gaba da mutane a wasu ƙauyuka da ke Ƙaramar Hukumar Borgo ta Jihar Neja, ciki har da waɗanda suke kan hanyar koma wa gidajensu bayan kammala sallar Juma’a. Al'amarin ya auku ne a ranar Juma’a a jim-kaɗan bayan kammala Sallar Juma’a a babban masallacin ƙauyen Dekara, inda wasu 'yan bindiga suka far wa jama'a tare da yin awon-gaba da masu ibada daga ƙauyukan Gidan Zana, Masaka da Sabon Gida. Daga cikin waɗanda aka sace akwai wani dattijo mai shekara 90 wanda mahaifi ne ga Dagacin Dekara, lamarin da ya jefe…
Read More

Da Ɗumi-Ɗumi: Tinubu ya naɗa kansa shugaban kwamitin yaƙin neman zaɓensa na 2027

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya fitar da sunayen mambobin kwamitin yaƙin neman zaɓensa a ƙarƙashin Jam'iyyar APC yayin tunkarar babban zaɓen 2027. Kakakinsa Bayo Onanuga ne ya fitar da jaddawalin mambobin a wata takarda da ya fitar a yau Asabar. Kwamitin ya ƙunshi; Abdulaziz Yari a matsayin darakta-janar, Hope Uzodimma a matsayin sakatare sai Shugaba Tinubu da mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima a muƙaman shugaba da mataimaki. Sakataren APC na Ƙasa, Ajibola Bashiru da Hadiza Bala-Usman sune mataimakan sakatare na ɗaya da ta biyu. A cewar sanarwar, shugaban kwamitin, Shugaba Tinubu zai yi aiki…
Read More