Babaji

5684 Posts

Dawo da tallafin fetur zai maida hannun agogo baya ga nasarorin da Nijeriya ta samu a tattali – Idris

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Al'umma, Mohammed Idris Malagi, ya ƙalubalanci kira akan a dawo da tallafin fetur da aka cire a baya, yana mai gargaɗin koma wa tsarin na da ka iya haifar da cikas ga bunƙasar da aka samu a ɓangaren wadatar kuɗi, karya ƙwarin-gwiwar masu zuba jari da rushe nasarorin da aka samu sakamakon gyare-gyaren fannin tattali a ƙarƙashin gwamnatin Tinubu. Shugaba Bola Tinubu dai ya cire tallafin fetur ne yayin da ya kama aiki a matsayin shugaban Nijeriya a watan Mayun 2023, matakin da ya zama ɗaya daga…
Read More

Gobara ta ƙone ɗaruruwan shaguna a shahararriyar kasuwar Oranyan ta Ibadan

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ɗaruruwan shaguna ne suka ƙone ƙurmus a wata gobara da tsakar dare a ranar Litinin a sananniyar kasuwar Oranyan da ke Ƙaramar Hukumar Ibadan ta Arewa maso Gabas a Jihar Oyo. Rahotanni sun bayyana cewa, gobarar, wadda ta fara ci tun tsakiyar dare, ta shafi shaguna da dama na sassa daban-daban na kasuwar. Sannan, ta shafi ƙananan 'yan kasuwa da suka haɗa da 'yan harkar gwala-gwalai, kafintancin zamani, 'yan gwanjo da wasu kayayyaki. Shaidu sun ce, wutar da fara ci ne tun da tsakar dare, saidai ba su san ainihin lokacin ba. Wasu rahotanni…
Read More

NiMet ta yi hasashen mamakon ruwan sama a Abuja, Nasarawa, Benuwai da wasu jihohi shida

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Yayin da ake tsaka da lokacin damina, Hukumar Kula da Yanayi ta Ƙasa (NiMet), ta yi hasashen samun hadari da tsawa a yankunan Nijeriya a ranar Litinin, 24 ga Agusta, 2026 tare da matsakaicin ruwan sama a sassa da dama na ƙasar. Blueprint ta ruwaito cewa, hasashen ya ƙunshi shiyyoyin arewaci, arewa ta tsakiya da kudanci ƙasar, inda za a yi tsawa da matsakaicin ruwan sama a jihohi da dama a yinin. A jihohin arewa, NiMet ta ce ana sa ran hadari a safiya, yayin da tsawa za ta biyo baya tare da matsakaicin…
Read More

2027: Tinubu ya janye jaddawalin kwamitin yaƙin neman zaɓensa

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Shugaba Bola Tinubu ya umarci a janye tare da sake tsara jaddawalin 'yan kwamitin yaƙin neman zaɓensa a ƙarƙashin Jam'iyyar APC domin babban zaɓen 2027. Umarnin ya biyo bayan cece-kuce akan jaddawalin da aka fitar da fari a ranar Asabar. A cewar jaridar TheWill, Tinubu ya ɗauki matakin ne bayan ƙorafi daga wasu jiga-jigan 'ya'yan APC da suka ce jaddawalin bai ƙunshi wasu muhimman masu ruwa da tsaki na jam'iyyar ba kuma bai yi daidai da tsarin shugabanci da rarrabawa da kuma tsarin jam'iyyar ba. Majiyoyi sun bayyana cewa, Tinubu ya umarci Fadar Shugaban…
Read More

Tinubu ya sabunta wa’adin jagororin NAN da NTA

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Shugaba Bola Tinubu ya sabunta wa'adin Malam Ali Muhammed Ali, wato Darakta Manaja na Kamfanin Dillancin Labarai (NAN), na tsawon wasu shekaru uku. Kakakin Shugaban ƙasa Bayo Onanuga ne ya sanar da haka a wata sanarwa da ya fitar a Abuja, ranar Lahadi. Ya ce, shugaban ƙasar ya kuma sabunta na jagorancin Darakta Janar na Gidan Talabijin na Ƙasa (NTA), Malam Abdulhamid Dembos. A cewar Onanuga, shugaban ya naɗa Dembos na NTA da Ali na NAN a ranar 20 ga watan Oktoba, 2023, inda ya ƙara da cewa, zangon nasu na biyu zai fara…
Read More

Shahararren jarumin Nollywood, Taiwo Hassan Ogogo ya rasu

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Sanannen jarumin Masana'antar Nollywood, Taiwo Hassan, wanda aka fi sani da Ogogo ya rasu. 'Yarsa Kira Taiwo ce ta tabbatar da rasuwarsa a wani faifan bidiyo da aka yi kai-tsaye yayin tattaunawa a shafinta na Instagram. A ranar Litinin, 17 ga Agusta ne 'ya'yan Ogogo biyu, wato Kira Taiwo da Lima Taiwo suka fitar da wani faifan bidiyo, inda suke roƙon jama'a shawarwarin lafiya da agaji ga mahaifin nasu da ya kasance yana fama da cutar daji ta mataki na huɗu. A cewar Kira, likitoci sun ce ba za su yi masa aikin kashe…
Read More

Malaman addini sun goyi bayan sake zaɓen Tinubu a 2027

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Yayin da aka sake kaɗa gangar siyasa a Nijeriya, wata tawagar Malaman Addinin Islama a Jihar Jigawa, ta bayyana goyon bayanta ga sake zaɓar Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaɓen 2027 da ke tafe. A wani taro da aka gudanar a Dutse, Babban Birnin Jihar Jigawa, an manyan malamai daga jihohin Arewa goma 19 da adadinsu ya kai kusan 500, inda suka bayyana amincewarsu ga takarar Shugaba Tinubu. Haka kuma, sun amince kan lallai shi za su yi wa yaƙin neman zaɓe kuma za su zaɓe a yayin zaɓukan, waɗanda za a gudanar a…
Read More

Tsohon Gwamnan Adamawa, Bindow ya koma APC bayan ganawa da Tinubu

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Tsohon Gwamnan Jihar Adamawa, Sanata Muhammad Umar Jibrilla Bindow, ya koma Jam'iyyar APC a hukumance gabanin shirye-shiryen babban zaɓen 2027. Hakan na zuwa ne bayan shawarwari da abokan hulɗar siyasa da kuma tattaunawa da Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima. Bindow ya sake rajistar zama mamban jam'iyyar ne a mazaɓarsa da ke Mubi, wato cibiyar kasuwanci ta jihar Adamawa a ranar Lahadi, a gaban Shugaban APC na mazaɓar, Alhaji Ahmadu Guruja. A yayin haka ne aka samu halartar tsofaffin magoya bayansa, abokai, 'yan dangi, abokan harkokin siyasa da masu fatan…
Read More

2027: SERAP ta buƙaci INEC ta bayyana adadin kuɗaɗen da doka ta ƙayyade wa jam’iyyu su kashe yayin yaƙin neman zaɓe

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja. Cibiyar kula da 'yancin zamantakewa da tabbatar da gaskiya da adalci a Nijeriya (SERAP), ta yi kira ga Shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), Farfesa Joash Amupitan, da ya yi amfani da ikon da dokar ƙasa ta bayar wajen bayyana ainihin adadin gudunmawar da ta halasta a bayar a harkokin siyasa ƙarƙashin Sashe na 91 na Dokar Zaɓe ta 2026. Haka kuma, SERAP ta roƙi hukumar da ta wallafa ainihin adadin da aka ƙayyade da kuma sanar da su ga jam'iyyun siyasa, 'yan takara, masu taimakawa da kuma al'ummar ƙasa domin tabbatar da biyayya…
Read More

Yaƙin neman zaɓen APC: Ƙungiyar Arewa ta jinjina wa Tinubu kan saka Yerima Shettima

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ƙungiyar Arewa Community APC a jihohin kudanci 17, ta taya Alhaji Kwamared Yerima Shettima kan samun muƙamin Darakta na Hulɗar Ƙwadago na II a kwamitin yaƙin neman zaɓen Jam'iyyar APC a zaɓukan 2027. Da yake magana a Gusau, Jihar Zamfara a ranar Lahadi Frins Alhaji Aliyu Bambado na II, wanda shi ne Galadiman Legas na I kuma mai bayar da shawara ga ƙungiyar Community APC a Legas da jihohin kudu 17, ya bayyana naɗin Shettima a matsayin ajiye ƙwarya a gurbinta duba da yadda yake da ƙwarewa da jajircewa a harkar shugabanci. Ya bayyana…
Read More