Babaji

5684 Posts

Tinubu ya umarci hukumomin tsaro su ceto masallatan Neja da aka sace

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Shugaba Bola Tinubu ya umarci rundunonin soji, 'yan sanda, hukumar tsaro ta farin kaya DSS da sauran hukumomin tsaro da na leƙen asiri, da su gaggauta ƙaddamar da atisayen ceto mutanen nan masu yawa da aka sace a Jihar Neja. Wannan umarni na zuwa ne bayan garkuwa da halaka wasu fararen hula daga ɓangaren 'yan ta'adda a jihar, inda shugaban ƙasar ya koka akan aukuwar iftila'in. A wata sanarwa da Kakakin Shugaban ƙasa Bayo Onanuga ya fitar a ranar Talata, Shugaban ya bayyana masu hannu a mummunan harin a matsayin maƙiya zaman lafiya da…
Read More

Sojoji sun ceto mutum 14 bayan daƙile yunƙurin garkuwa a Zamfara

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Dakarun tsaron Shiyya ta 2 na Atisayen FANSAR YAMMA, sun yi nasarar daƙile wani yunƙuri da yin garkuwa da mutane, sannan sun ceto mutum 14 yayin atisayen a Ƙaramar Hukumar Tsafe da ke Jihar Zamfara a ranar Talata. Wata majiyar tsaro ta shaida wa wakilinmu cewa, an gudanar da atisayen ne a ranar Talata, 25 ga Agusta bayan samun wani bayani na sirri kan lamuran ababen zargi a yankin ƙauyen Magazu. Akan haka ne rundunar ta tura jami'an tsaro yankin, inda suka yi arangama da maharan da ke ƙoƙarin sace wasu fararen hula ciki…
Read More

Ka daina tsoma baki a idan ‘yan siyasa na magana – Amaechi ga Sowore

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Wani fagen tattaunawar harkar siyasa a babban taron Ƙungiyar Lauyoyi ta Ƙasa (NBA) karo na 66 a Fatakwal, Jihar Ribas ya koma cacar baki bayan ɗan takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar AAC, Omoyele Sowore ya ƙalubalanci tarihin siyasar 'yan siyasar da suka riƙe muƙaman gwamnati a baya. Ana haka ne tsohon Gwamnan Jihar Ribas kuma tsohon Ministan Sufuri Rotimi Amaechi, wanda ya wakilci ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar a taron, ya mayar da martani kan sukar. Ya ƙalubalanci Sowore da ya bayyana ƙwarewarsa a fagen shugabanci. An fara musayar kalaman…
Read More

Kano: ‘Yan unguwa sun ƙi karɓar cin hancin N10m don rufa-rufa ga zargin safarar miyagun ƙwayoyi

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Mazauna Unguwar Bajallabe da ke yankin FCE Gate na 1 a garin Kano, sun ƙi amincewa su karɓi wani tayin cin hanci da aka yi zargin ya kai Naira miliyan 10 domin su yi rufa-rufa ga wata mota da ake zargin ta da jigilar miyagun ƙwayoyi. Al'amarin ya faru ne a safiyar ranar Talata bayan 'yan yankin sun gano wata mota ƙirar Golf da ake zargin tana maƙare da haramtattun ƙwayoyi, wadda aka ajiye a gefen wani babur kusa da wani gida da ke unguwar. Kakakin hukumar jami'an yaƙi da sha da fataucin miyagun…
Read More

2027: Abin da ya sa Tinubu ya jirkita jaddawalin yaƙin neman zaɓensa

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja An buƙaci Fadar Shugaban Ƙasa ta sake nazari akan haɗin mamban kwamitin yaƙin neman zaɓen APC a 2027 ne saboda waɗansu dalilai da ka iya tozarta yaƙin neman zaɓen, kamar yadda rahotanni suka bayyana. An yi ta cece-kuce daga ciki da wajen jam'iyyar tun bayan fitar da jaddawalin a ranar Asabar, inda da dama suka riƙa ankararwa kan cire wasu sunaye da sanya wasu da ake da alamar tambaya akansu. A jaddawalin, an naɗa Shugaba Tinubu a matsayin shugaba da Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima a matsayin maitaimaki. Haka kuma, an naɗa Shugaban APC…
Read More

Gwamna Buni da mashawarcin Tinubu sun bada tallafin miliyan N600 don gina jami’ar JIBWIS

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Gwamna Mai Mala Buni na Jihar Yobe da Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara akan Harkar Siyasa, Kabiru Ibrahim Masari, sun bayar da tallafin jimillar Naira miliyan 600 domin gina jami'ar Fortune University. Ƙungiyar Jama'atu Izalatul Bid'ah Wa'iƙamatus Sunnah (JIBWIS), reshen Jos ce ta samar da jami'ar a yankin Magama Gumau da ke Ƙaramar Hukumar Toron Jihar Bauchi, wadda ake aikinta tun a baya. Masari da Gwamna Buni sun sanar da tallafin ne a ranar Lahadi yayin wani taron wayar da kan al'umma kan shiga harkar siyasa na kwana ɗaya mai taken "Enhanced Political Participation…
Read More

Ƙungiyar AVRS ta yi jimamin rasuwar Jarumi Taiwo Hassan Ogogo

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ƙungiyar kare 'yancin kafafen yaɗa labarai (AVRS), ta shiga sahun masana'antar finafinai wajen jimamin rasuwar ɗaya daga cikin mambobinta, jarumi Taiwo Hassan da aka fi sani da Ogogo. A wata sanarwa da ta fitar ta hannun Shugaban kwamitin yaɗa labaranta, Sani Mu'azu a ranar Talata, AVRS ta ce jarumin ginshiƙi ne daga cikin ginshiƙan masana'antar finafinan Nijeriya kuma jarumin da ƙwarewarsa ta bayar da gagarumar gudunmawa wajen ciyar da harkar gaba a tsawon shekaru da dama. Ta bayyana cewa, bisa baiwar da yake da ita, ya kasance mai nishaɗantarwa da ilimantar da masu kallo,…
Read More

2027: Zan cire tallafin fetur, daga bisani na dawo da shi, inji Atiku

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar zai dawo da tallafin fetur idan aka zaɓe shi a 2027, amma daga baya zai cire na wucin-gadi don daidaita lamuran tattali, inji Kakakinsa Paul Ibe. Ibe ya bayyana haka ne yayin hira da gidan talabijin na AIT, inda ya ce shirin Atiku akan tallafi yana da bambanci da na gwamnatocin baya kuma zai fifita samar da ɗanyen mai da tacewa a cikin gida Nijeriya. A cewarsa, dawo da shi na wucin-gadi zai bai wa 'yan Nijeriya da kasuwanci damar numfasawa da farfaɗowa daga matsin tattali da ake…
Read More

Adadin ‘yan ta’adda da ke tuba ya ƙaru da kaso 202 – Sojoji

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Dakarun haɗaka a Arewa maso Gabas, ƙarƙashin Atisayen HAƊIN KAI, sun samu ƙarin adadi mai yawa cikin ƙanƙanin lokaci na kwamandoji, mayaƙa da masu taimaka wa 'yan ta'adda da ke miƙa wuya ga rundunar sojoji. Rahotanni sun bayyana cewa, sama da 'yan ta'adda guda 150 ne suka miƙa wuya acikin wannan makon, wanda idan aka kwatanta da 50 da aka samu a makon da ya gabata, hakan na wakiltar ƙarin kashi 202. Kafin Mohammed Goni, jami'in yaɗa labarai na rundunar kuma na riƙo, shi ne ya bayyana haka a wata takarda da ya fitar…
Read More

Yanzu-yanzu: APC ta musanta janye jaddawalin kwamitin yaƙin neman zaɓen Tinubu na 2027

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Jam'iyyar APC ta yi watsi da rahotannin da ke cewa ta janye jaddawalin sunayen 'yan kwamitin yaƙin neman zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaɓen 2027. Sakataren yaɗa labaran jam'iyyar, Felix Morka, ya bayyana rahotannin da ke yaɗa hakan a matsayin jita-jita, inda ya ce dukkan wani hukuncin da aka yanke kan kwamitin, za a ji shi ne daga bakin jam'iyyar a hukumance. Da yake magana da 'yan jaridar a safiyar yau Talata a Abuja, Morka ya ce APC ba ta janye jaddawalin ba kuma ra rahotannin da ake yaɗawa akan haka ba gaskiya…
Read More