27
Aug
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Gwamnatin Jihar Neja ba ta samu wani kira daga 'yan ta'addan da suka sace masallata ba a wani masallaci da ke Ƙaramar Hukumar Borgu a ranar Juma'a, inji Kwamishinan Yaɗa Labaran Jihar Neja, Obed Nuhu. Nuhu ya bayyana haka ne a ranar Alhamis yayin wata hira da gidan talabijin na Channels, inda ya ce harin ya faru ne a wurare guda uku da ke yankin, wanda ake zargin ƙungiyoyin Lakurawa da Boko Haram da alhakin ƙaddamarwa. Rahotanni sun bayyana cewa, kwamishinan ya ce har yanzu gwamnatin ba ta samu damar tattaunawa ba da masu…
