Babaji

5684 Posts

WAEC na fuskantar sabon ƙalubale kan sakamakon jarrabawar 2026 yayin zargin saɓa wa dokoki

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Hukumar Shirya Jarrabawar Yammacin Afirka (WAEC), ta fara fuskantar bincike kan sakamakon da ta fitar a kwanan nan na jarrabawar kammala sakandare ta WASSCE ta 2026 yayin da jagororin makarantu da masu kira ga neman ilimi suka yi zargin saɓa wa ƙa'idoji da matsalolin sadarwa sanadiyyar amfani da cibiyoyin kwamfuta (CBT). Hakan na zuwa ne bayan da jagororin makarantu da dama suka yi ƙorafi da iƙirarin da masu kira ga neman ilimi suka gabatar cewa wasu zaƙaƙuran ɗalibai sun samu maki ƙasa da yadda ake tsammani, bisa la'akari da ƙoƙari da kuma abin da…
Read More

Mu na nazarin sakamakon zaɓen Osun – APC

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Jam’iyyar APC a Jihar Osun, ta ce tana nazari kan sakamakon zaɓen gwamnan jihar na 2026 da aka kammala a kwanan nan, domin tantance matakin da za ta ɗauka na gaba. Daraktan yaɗa labaranta, Kola Olabisi ne ya bayyana haka a wata takarda da ya fitar a ranar Lahadi a Osogbo. A cewarta: "Babu yadda za a yi a ce an kammala zaɓe ba tare da aiwatar da dukkan damar da doka ta bayar ba na gyara ababen da suka saɓa wa tsari da aka gano yayin haka, kamar yadda Dokar Zaɓe ta 2026…
Read More

NFF ta sallami tawagar jagorancin Super Falcons ta Koci Madugu

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Kwamitin Zartarwa na Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Ƙasa (NFF), ya tsige tawagar gudanar da harkokin 'yan wasan Super Falcons ƙarƙashin jagorancin Justine Madugu, hukuncin da ya fara aiki a nan take. NFF ta sanar da haka ne a wata sanarwa da ta wallafa a sahihin shafinta na X a ranar Litinin. Super Falcons ta shiga mawuyacin hali yayin buga wasannin gasar Kofin Ƙasashen Afirka na Mata WAFCON, wanda aka gudanar a ƙasar Moroko. Nijeriya ta shiga gasar ne a matsayin wadda take riƙe da kofin kuma ta lashe har sau goma a tarihinta. Saidai…
Read More

Sama da farfesoshi da lakcarori 200 na Jami’ar Kaduna sun yi murabus yayin da ASUU ta yi barazanar shiga yajin aiki

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Malaman jami'a da suka haɗa da masu muƙamin farfesa da wasu sama da guda 200 ne suka bar Jami'ar Kaduna KASU, bisa rashin ingancin lamuran gudanarwa da rashin aiwatar da yarjejeniyar Gwamnatin Tarayya da Ƙungiyar Malaman Jami'o'i ta Ƙasa (ASUU) ta 2025, inji reshen ƙungiyar na KASU. Rahotanni sun bayyana cewa ASUU reshen KASU ta bayar da wa'adin sati biyu ga hukumomin jami’o’i da sauran masu ruwa da tsaki da su fara aiwatar da yarjejeniyar yadda aka tsara ta, tana mai gargaɗin cewa rashin yin hakan ka iya haifar da yajiin aikin sai baba-ta-gani…
Read More

Dakarun tsaro sun ceto mutum tara bayan daƙile harin ‘yan bindiga a hanyar Zamfara

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Dakarun Sashe ne 2 na Atisayen FANSAR YAMMA, sun yi nasarar daƙile wani harin 'yan ta'adda na garkuwa da mutane da dama a Unguwar Rogo da ke Ƙaramar Hukumar Ƙauran Namoda ta Jihar Zamfara, inda suka yi nasarar ceto wasu mutane guda tara, saidai maharan sun tsere da uku a yayin haka. Rahotanni sun bayyana cewa, ana zargin maharan yaran jagoran 'yan ta'adda mai suna Malam Shu'aibu ne, waɗanda suka ƙaddamar da harin da nufin ramuwa akan atisayen sojoji na kwanan nan kan dabar da masu taimaka mata ciki har da kama masu tsegumi…
Read More

‘Yan sanda sun tabbatar da harin ‘yan ta’adda a Sakkwato

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Rundunar 'Yan sanda a Jihar Sakkwato ta tabbatar da cewa wasu da ake zargin 'yan ta'addan Lakurawa ne sun kai wani hari a garin Kebbe a ranar Juma'a, inda ta ce jami'an tsaro sun mayar da martani kuma an tura ƙarin wasu a yankin. Haka kuma, rundunar ta ce babu wani farar hula da aka halaka ko jikkata harin saɓanin wasu rahotanni da ke nuna 'yan ta'addar sun halaka mutane da dama. Wasu rahotanni da aka wallafa bayan aukuwar lamarin sun bayyana cewa an halaka soja guda huɗu a yayin arangamar, amma Rundunar Soji…
Read More

An kama budurwa a Kebbi kan zargin satar jariri da juna biyun bogi

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Rundunar 'Yan Sanda a Jihar Kebbi, ta ce ta kama wata mata mai shekaru 19 a Ƙaramar Hukumar Zuru da ke jihar bisa zargin ta da sace wani sabon jariri da gabatar da shi ga mijinta a matsayin nata. Al'amarin ya auku ne a ranar 23 ga Yuli, 2025, a lokacin da wadda ake zargin ta ziyarci wata mai suna Fatima Muhammad jim-kaɗan bayan ta haihu, inda ta taimaka mata da wasu ayyuka ciki har da ɗebo ruwa. A cewar 'yan sanda, wadda ake zargin ta yi amfani da damar hakan ne wajen tserewa…
Read More

Kakakin majalisar dokokin Edo, Blessing Agbebaku ya yi murabus yayin yunƙurin tsige shi

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Kakakin Majalisar Dokoki na Jihar Edo, Blessing Agbebaku ya sauka daga muƙaminsa yayin da ake tsaka da zargin wasu mambobin majalisar na shirin tsige shi. Rahotanni sun bayyana cewa, ɗan majalisa mai wakiltar mazaɓar Akoko Edo ta II, Yekini Idaiyi ne aka rantsar a matsayin sabon kakakin bayan matakin na Agebakun. Mai taimaka wa Agbebaku kan harkokin yaɗa labarai, Ivy Ebojele ne ya tabbatar da murabus ɗin mai gidan nasa a wani rubutu da ya ɗora a kafar Facebook a ranar Litinin, inda ya ce za a fitar da ƙarin bayani kan al'amarin a…
Read More

Cardoso, Ojulari da Tantita za su halarci taron Karramawa na Blueprint gobe

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Mista Olayemi Cardoso; Shugaban Babban Kamfanin Man Fetur na Ƙasa (NNPCL), Injiniya Bashir Bayo Ojulari da Kamfanin Tantita Security Services suna daga cikin sanannun mutane da ƙungiyoyin da za a karrama a babban taron shekara-shekara na bayar da lambobin yabo da Kamfanin Jaridun Blueprint Newspapers Limited zai jagoranta a gobe Talata, 18 ga Agusta, 2026. Taron, wanda za a gudanar a ɗakin taro na Bola Ahmed Tinubu International Conference Centre, Abuja, zai haɗa manyan jami’an gwamnati, jagororin siyasa, jagororin kamfanoni, masana harkar tsaro, 'yan difulomasiyya, malamai, wakilan ƙungiyoyin al'umma,…
Read More

Adeleke ya janye ƙarar EFCC bayan nasara a zaɓen Osun

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Wanda aka sake zaɓa a matsayin Gwamnan Jihar Osun, Ademola Adeleke, ya ce ya umarci Antoni Janar na jihar da ya janye ƙarar da suka shigar akan Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta'annati EFCC, bisa rufe asusun bankin gwamnatin jihar gabanin zaɓen da aka gudanar a ranar Asabar. Adeleke ya bayyana haka ne a wata hira da gidan talabijin na Channels a ranar Lahadi, sa'o'i bayan ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar da Hukumar Zaɓe (INEC) ta yi. Yayin da aka masa tambaya kan halin batun rikicin siyasa…
Read More