Babaji

5684 Posts

Tinubu zai yi jawabi a taron Majalisar Ɗinkin Duniya ranar 23 ga Satumba

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Shugaba Bola Tinubu zai haɗu da jagororin ƙasashen duniya a taron Majalisar Ɗinkin Duniya (MƊD) karo na 81 (UNGA 81), inda aka tsara zai gabatar da jawabi a New York, a ranar Laraba, 23 ga Satumba, 2026. Manhaja ta ruwaito cewa, an zaɓi Tinubu ne matsayin mai jawabi na 10 yayin zangon safe a rana ta biyu ta babban taron tafka muhawara (high-level General Debate), wanda za a gudanar a tsakanin ranakun 22 da 28 ga Satumba a hedikwatar Amurkan. A yadda aka tsara, Shugaban Nijeriyar zai yi jawabin nasa ne yayin zangon safe,…
Read More

‘Yan bindiga sun halaka sufeton ‘yan sanda da wasu huɗu a sabon harin Adamawa

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Wasu 'yan bindiga sun halaka sufeton hukumar 'yan sanda da wasu mutane huɗu a yayin wani hari da suka ƙaddamar a ƙauyen Gaya Dlang da ke Gundumar Kuva Gaya a Ƙaramar Hukumar Hong ta Jihar Adamawa. Al'amarin ya auku ne da misalin ƙarfe 5 na yammacin ranar Litinin, wanda kuma shi ne mummunan hari na biyu da aka samu cikin wata guda, kuma a haifar da fargaba acikin al'umma bisa hare-haren 'yan bindiga. Kakakin Runndunar 'yan sandan jihar, SP Suleiman Yahya-Nguroje ne ya sanar da haka yayin ganawa da wakilin gidan talabijin na Channels…
Read More

Iƙirarin ASUU cewa sama da lakcarori 200 sun yi murabus a KASU ba gaskiya ba ne, inji VC Farfesa Musa

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Mataimakin Shugaban Jami'ar Jihar Kaduna (KASU), Farfesa Abdullahi Musa, ya yi watsi da iƙirarin Ƙungiyar Malaman Jami'o'i rushen jami'ar (ASUU-KASU) na cewa sama da malamai 200 sun ajiye aikinsu kan rashin kyawun yanayin aiki, yana mai bayyana zargin a matsayin abin ruɗarwa da bai yi kama da haƙiƙanin al'amari ba. Rahotanni sun bayyana cewa, wannan faɗi-in-faɗa ta samo asli ne bayan wani taron manema labarai da ASUU-KASU ta kira, inda ta yi zargin sama da farfesoshi da lakcarori 200 sun bar aiki da jami'ar bisa rashin kyawun yanayin aiki da gazawar cika alƙawarin aiwatar…
Read More

Tinubu ya gana da shugaban EFCC da ministan gine-gine kan kadarorin da aka ƙwace

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A ranar Talata Shugaba Bola Tinubu ya karɓi ba'asi daga Shugaban Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta'annati EFCC, Ola Olukoyede da Ministan Gine-gine da Raya Birane, Muttaqa Rabe Darma a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja. Rahotanni sun bayyana cewa, ganawar ta mayar da hankali ne kan gudanarwa da soke amfanin gidaje da EFCC ta ƙwace a faɗin Nijeriya, kuma ita ce ta farko tsakanin Tinubu da Olukoyede tun bayan da shugaban ya soke hukuncin hukumar na sanya wa asusun gwamnatin Jihar Osun takunkumi. Ofishin yaɗa labaran fadar ne ya fitar da…
Read More

‘Tsaro ba wajen taro ba ne’, Ministan Tsaro ya gargaɗi tura dakarun tsaro ana gab da zaɓe

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa (mai ritaya) ya yi gargaɗi ga hukumomin tsaro kan dogaro da aikin tura jami'an tsaro bayar da kariya wuraren zaɓuka yayin da ake gab da farawa, yana mai cewa samun hakan ya inganta na buƙatar a ɗauki tsawon watanni ana kimtsawa. Janar Musa ya bayyana haka ne a ranar Talata yayin gabatar da jawabin babban baƙo a taron Karramawa na jaridar Blueprint kan tsaro. Ya ce, wajibi ne a mu'amalanci al'amarin tsaron zaɓe wajen ɗaukar tsawon lokaci ana nazari a kai musamman don kimtsawar wuri da ƙoƙarin neman hanyoyin…
Read More

Daga ƙarshe, ɗan takarar APC Oyebamiji ya magantu bayan kaye a zaɓen Osun

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ɗan takarar gwamnan jihar Osun a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar APC, Bola Oyebamiji, ya magantu a karon fari bayan shan kaye a hannun gwamna mai ci, Ademola Adeleke a zaɓen da aka gudanar a ranar Asabar. Oyebamiji ya karɓi sakamakon da Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta fitar yayin da ya koka kan zargin hare-haren da aka kai wa wasu mambobin APC da magoya baya bayan zaɓen. An sanar da Adeleke na jam'iyyar Accord Party a matsayin wanda ya lashe zaɓen bayan samun ƙuri'a 511,067, yayin da Oyebamiji ya samu ƙuri’a 444,815 a matsayi na…
Read More

Wike ya umarci a rushe gidaje masu tare magudanan ruwa a Abuja

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ministan Abuja Nyesom Wike, ya umarci a gaggauta rusa gidaje da wasu gine-gine da suke haifar da tsaiko ga a hanyoyin da ruwa ke wucewa a unguwar Maitama da wasu wurare masu fuskantar barazanar ambaliya a Babban Birnin. Wike ya bayar da wannan umarni ne bayan aukuwar wata ambaliya a kwanan nan da ta haifar da tsaiko ga harkokin yau da kullum na al'umma a sassan birnin. Ministan ya bayar da umarnin ne a yau Talata bayan ziyarar sanya ido a yankunan da ambaliyar ta shafa a Maitama, inda wani mamakon ruwan sama ya…
Read More

CP Bakori ya yaba wa wata mace kan gyara ofishin shiyya na rundunar a Kano

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Kwamishinan 'Yan sandan Jihar Kano, Ibrahim Adamu Bakori ya gabatar da wasiƙar godiya ga Hajiya Hajara Abdullahi ta Diso Quarters da ke Ƙaramar Hukumar Gwale a jihar, yayin yaba wa ƙoƙarinta na taimaka wa al'umma musamman kan gyara ofishin 'yan sanda na Shiyyar Gwale da ta gudanar. Ya ce, wannan hoɓɓasa da Hajiya Hajara ta yi na wakiltar gagarumar gudumawa ga harkar tsaro a yankin. A cewarsa, tana bayar da tallafi ga ayyukan shiyyoyin 'yan sanda a sassan jihar da nufin inganta wuraren ayyukan jami'ai da bunƙasa lamuran hidimta wa al'umma. Da yake damƙa…
Read More

Shugaban sojoji ya je ta’aziyya bayan harin ‘yan bindiga ya yi ajalin babban limami da wasu 27 a Sakkwato

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Kimanin mutane 28 ciki har da limamin Masallacin Izala na Ungushi, Imam Aliyu ne aka halaka a lokacin da wasu 'yan bindiga suka farmaki jama'a a ƙauyen Ungushi da ke Ƙaramar Hukumar Kebbe ta Jihar Sakkwato a daren Litinin. Da yake tabbatar da labarin, Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Sakkwato, DSP Ahmed Rufa'i, ya ce yana da wuya a iya gano ainihin adadin waɗanda iftila'in ya shafa. Saidai, ya ce an gano gawarwaki guda 28 bayan aukuwar lamarin. Mazauna sun ce maharan sun afka wa ƙauyen ne da dare, inda suka buɗe wa jama'a…
Read More