Babaji

5684 Posts

Yanzu-yanzu: Tinubu ya maye gurbin Didi Walson-Jack da Abel Enitan a matsayin sabon Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Shugaba Bola Tinubu ya naɗa Abel Enita a matsayin sabon Shugaban Ma'aikatan Gwamnatin Tarayya, wanda zai fara a ranar 27 ga Agusta, 2026. Hakan na nufin Enitan zai maye gurbin Misis Didi Walson-Jack a muƙamin, wadda a kwanan nan za ta yi ritaya bayan cika shekaru 60, kamar yadda doka ta tsara. Enitan, wanda ɗan ainihin Jihar Osun ne, shi ne mafi girma kuma Babban Sakatare da Ma'aikatar Ma'aikatan Tarayya, wanda yake da ƙwarewa a harkar gudanarwa da kuma fahimtarsa ga ayyukan sabon nauyin da aka ɗora masa. Ya kasance a matsayin babban sakatare…
Read More

Da Ɗumi-Ɗumi: ‘Yan bindiga sun farmaki ayarin motocin Gwamnan Osun yayin da jami’an tsaro suka daƙile harin

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A ranar Laraba wasu 'yan bindiga suka farmaki tawagar motocin da ke yi wa Gwamna Ademola Adeleke na Jihar Osun rakiya, jim-kaɗan bayan kai ziyara a fadar Ataoja na Osogbo, Oba Jimoh Oyetunji, lamarin da ya haifar da musayar wuta tsakaninsu da jami'an tsaron gwamnan. Rahotanni sun bayyana cewa, ba-takashin, wanda aka shafe tsawon mintina 12 zuwa 15, ya faru ne bayan gwamnan ya fice daga fadar basaraken, lamarin da ya jefa al'ummar yankin cikin firgici. Gwamnan ya isa fadar mai martaban ne da misalin ƙarfe 3:15 na rana a wani ayarin motoci guda…
Read More

Rundunar ‘yan sanda ta bada umarnin bincike kan bidiyon zargin jami’anta suna karɓar na goro a Kaduna

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Rundunar 'Yan sanda a Jihar Kaduna, ta umarci a fara gudanar da cikakken bincike kan wani faifan bidiyo da ya karaɗe kafafen sada zumunta, wanda yake zargin jami'an 'yan sanda suna tilasta wa masu motoci da babura ba su na goro yayin aiki a shingen bincike. Kwamishinan rundunar, Rabi'u Muhammad ne ya bayar da umarnin inda ya buƙaci a gano su waye ne daga cikin 'yan sandan aka gani a bidiyon kuma a gayyato su yayin binciken. A wata sanarwa da Kakakin rundunar, DSP Mansir Hassan ya fitar a ranar Talata, rundunar ta ce…
Read More

2027: Tsohon Sufeto Janar ne zai lashe zaɓen gwamnan Nasarawa, inji Ali Bagio

Daga JOHN D. WADA a Lafiya Jibrin Ali, wanda akafi sani da Bagio babban mai goyon baya kuma mai tara kuri’u ne na musamman ga qan takarar kujerar gwamnan jihar Nasarawa a karkashin jam’iyyar Social Democratic Party SDP wato tsohon sufeton ‘yan sandan Najeriya alhaji Abubakar Muhammed Adamu inda ya bayyana cewa qan takarar nasa kadai ne zai iya lashe zaben gwamnan dake tafe a jihar. Bagio ya bayyana haka ne a Lafiya babban birnin jihar yayin tattaunawa na musamman da manema labarai kwanan nan. Ya musanta zargin cewa babban qan takarar SDP din wanda aka zaba kafin zuwan Abubakar…
Read More

Filato: ‘Yan sanda sun cafke wanda ake zargi da kitsa harin ƙauyen Mangu

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Rundunar 'yan sanda a Jihar Filato, ta ce ta kama wanda ke zargi da kitsa mummunan harin ranar Talata da aka ƙaddamar a ƙauyen Bimper da ke Gundumar Kombun ta Ƙaramar Hukumar Mangu. Rahotanni sun ce, harin ya yi ajalin kimanin mutane 25 yayin da jikkata wasu huɗu sakamakon raunuka a farmakin safiyar. Wannan shi ne karo na uku da aka ƙaddamar da harin 'yan ta'adda acikin mako guda a Mangu. Kakakin 'yan sandan jihar, SP Alfred Alabo ne ya tabbatar da kamen ga gidan talabijin na Channels, inda ya ce a yanzu haka…
Read More

Gwamnatin Tinubu ta faɗi yadda aka sarrafa kuɗaɗe bayan tara tiriliyan N15.8 daga tallafin fetur da sauye-sauyen canjin kuɗi

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Gwamnatin Tarayya ta ce cire tallafin fetur da samar da tsari guda na kasuwar canjin kuɗaɗen ƙasashen waje sun tara mata jimillar Naira tiriliyan 15.8 da ƙarin albarkatu ga ƙasa daga watan Yunin 2023 zuwa Disambar 2025, inda jihohi da ƙananan hukumomi suka samu kaso mafi tsoka. Rahotanni sun bayyana cewa, Gwamnatin Tarayya ta ce kuɗaɗen da aka samu daga cire tallafi bai shiga sahun asusun tarayya ba a ware, wato "subsidy savings", saidai an bayyana tasirinsa ta kuɗaɗen shiga da aka karɓa sakamakon sauye-sauye a canjin kuɗi da waɗanda aka samu sanadiyyar tasirin…
Read More

Sabon harin Sakkwato ya yi ajalin mutane bakwai da sace 17 a ƙauyuka uku

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Wasu 'yan bindiga sun kai wa ƙauyuka guda uku farmaki a Ƙaramar Hukumar Wurno da ke Jihar Sakkwato, inda suka halaka mutum bakwai da kuma sace wasu guda 17 da suka haɗa da mata 15. Ƙauyukan da aka afka wa sune Dinawa, Munƙi da Gidan Dare, inda maharan suka ɗauki tsawon sa'o'i suna atisaye a daren Litinin, bayan amfani da damar mamakon ruwan sama da aka zabga a yankin. Da yake tabbatar da aukuwar lamarin, Shugaban 'yan bijilante na yankin Dinawa, Aliyu Falke, ya ce an yi jigilar maharan ne a wata tirela da…
Read More

Abuja: Diloli sun shiga tsaka mai wuya bayan Wike ya haramta amfani da guraren shaƙatawa a matsayin wuraren siyasar da motoci

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Akwai yiwuwar dilolin harkar motoci a Abuja su fuskanci ƙalubale yayin da Ministan Abuja, Nyesom Wike ya umarci a gaggauta dakatar da amfani da filayen shaƙatawa a faɗin babban birnin a matsayin wuraren dillanci ko siyasar da motoci. Rahotanni sun bayyana cewa, umarnin na Wike wani ɓangare ne na ƙoƙarin Hukumar Gudanarwar Birnin (FCTA), na warware matsalolin barazanar ambaliya da ke fuskanta a sassan birnin a wannan daminar. A wata sanarwa da Jami'in Hulɗa da Jama’ar ministan, Lere Olayinka ya fitar wa manema labarai, Wike ya koka kan yadda aka mayar da filayen da…
Read More

Gwamnatin Tarayya, jihohi da ƙananan hukumomi sun raba kuɗi mafi yawa a ƙarƙashin Tinubu na watan Yuli

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Kimanin Naira tiriliyan 3 ne Gwamnatin Tarayya, jihohi da ƙananan hukumomi suka raba a tsakaninsu daga kuɗaɗen asusun tarayya a watan Yuli, 2026, wanda ya zama mafi girma da aka taɓa rabawa a ƙarƙashin gwamnatin Tinubu. An sanar da haka ne a taron Agusta, 2026 na Kwamitin Asusun Kasafta Kuɗaɗen Tarayya (FAAC) da aka gudanar a Owerri, Babban Birnin Jihar Imo, wanda kuma Ministan Kuɗi da kula da Harkokin Tattali, Taiwo Oyedele ya jagoranta. Kasafin na watan Yuli ya samu gagarumin ƙari daga tiriliyan N2.551 da aka raba a tsakanin ɓangarorin gwamnatin uku a…
Read More

Gwamnan Zamfara ya lashe kyautar gwarzon gwamna na Blueprint yayin da manyan jami’an gwamnati suka tafka muhawara kan tsaro da zaɓen 2027

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Gwamna Dauda na Jihar Zamfara ya samu kyautar lambar yabo ta Jaridar Blueprint ta 2026 kuma ta Gwarzon Gwamna mafi Ƙwarewa wajen Gudanar da Kuɗaɗen Al'umma da Tsare Gaskiya da Adalci, inda yake ƙoƙarin ganin gwamnatinsa ta ceto tare da sake gina Zamfara domin amfanin al'umma. Dauda Lawal ya karɓi wannan kyauta ne a ranar Talata, 18 ga Agusta yayin taron Karramawa na Kamfanin Jaridun Blueprint na Shekara-Shekara, wanda aka gudanar a ɗakin taro na Bola Ahmed Tinubu International Conference Centre da ke Abuja, inda jagororin siyasa, 'yan difulomasiyya, ƙungiyoyin al'umma, masana da sauran…
Read More