13
Jul
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Gwamnatin Tarayya ta dakatar da shirinta na sauya kuɗin rajistar jarrabawar WAEC da ta NECO na 2027, har zuwa lokacin da za ta kammala shawarwari da masu ruwa da tsaki. Rahotanni sun bayyana cewa, Ma'aikatar Ilimi ta Tarayya ta sanar da matakin a wata sanarwa, inda ta ce ta janye ƙudirin wanda ke ƙunshe a wata takarda da aka fitar a ranar 18 ga Yuni da ke neman yi wa farashin rajistar jarrabawar garambawul. A cewar ma'aikatar, an ɗauki matakin janyewar ne sakamakon samun ƙorafe-ƙorafen al'umma akan matsin da ƙarin kuɗin jarrabawar ka iya…
