ukarofi

12485 Posts
Gwamnatin Tarayya ta saki biliyan N11.58 ga shirin tallafa wa mutane 178,342 a Jigawa

Gwamnatin Tarayya ta saki biliyan N11.58 ga shirin tallafa wa mutane 178,342 a Jigawa

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Gwamnatin Tarayya ta fitar da sama da Naira biliyan 11.58 domin aiwatar da shirin Tallafin Tsaron Rayuwar Jama’a na Sabunta Fata, wato Renewed Hope Social Security Grant, a Jihar Jigawa, inda ake sa ran mutane 178,342 za su amfana da tallafin a faɗin ƙananan hukumomin jihar 27. Kwamishinan Ayyuka na Musamman da Harkokin Agaji na Jihar Jigawa, Hon. Auwal Sankara, ne ya bayyana hakan yayin da yake yi wa ’yan jarida bayani kan yadda shirin ke gudana. Ya ce, an tsara shirin ne domin tallafa wa iyalai masu ƙaramin ƙarfi ta fuskar kuɗi tare da haɓaka…
Read More
2027: Jam’iyyun adawa na yunƙurin haɗaka don neman ɗan takarar da zai ƙalubalanci Tinubu

2027: Jam’iyyun adawa na yunƙurin haɗaka don neman ɗan takarar da zai ƙalubalanci Tinubu

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Manyan jam’iyyun adawa a Nijeriya sun fara sabunta ƙoƙarin haɗa kai domin kafa wata babbar ƙawance da za ta samar da dandali guda na siyasa da zai kalubalanci Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da Jam’iyyar APC a zaɓen Shugaban ƙasa na 2027. Sabon yunƙurin, wanda ƙungiyar G-100 ke jagoranta, na da nufin haɗa jam’iyyun African Democratic Congress (ADC), Peoples Democratic Party (PDP), Nigeria Democratic Congress (NDC), Peoples Redemption Party (PRP), Social Democratic Party (SDP) da Allied Peoples Moɓement (APM). Daga cikin ’yan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyun da aka ambata akwai Atiku Abubakar na…
Read More
Al’ummar Kano ba su tare da kalaman Sheikh Jingir – Kwankwaso

Al’ummar Kano ba su tare da kalaman Sheikh Jingir – Kwankwaso

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce kalaman da malamin addinin musulunci Sheikh Sani Yahaya Jingir ya yi na iya haifar da rarrabuwar kawuna a tsakanin al'ummar Nijeriya. A wata sanarwa da Kwankwaso ya wallafa a shafinsa na ɗ, ya jaddada cewa al'ummar Kano ba su tare da irin waɗannan kalamai na yunƙurin rarraba kawuna ba Ya ce ya damu matuƙa da kalaman da Sheikh Jingir ya yi a wani taro a Kano a ƙarshen mako. A ƙarshen makon nan ne kafar sada zumunta da ma kafafen yada labarai suka ɗauki ɗimi…
Read More
Yadda aka yi maulidin Sheikh Ahmadu Tijjani na 2026 ƙarƙashin Khalifa Ibrahim Dahiru Bauchi a Kano

Yadda aka yi maulidin Sheikh Ahmadu Tijjani na 2026 ƙarƙashin Khalifa Ibrahim Dahiru Bauchi a Kano

Daga BILKISU YUSUF ALI a Kano An gudanar da babban taron maulidin Sheikh Ahmad Tijjani a birnin Kano, wanda gidauniyar Sheikh Dahiru Usman Bauchi Foundation ta saba shiryawa duk shekara don tunawa da ranar haihuwar Shehi Ahmadu Tijjani da irin gudummawar da ya bayar wajen yaɗa addinin Musulunci da ɗariƙar Tijjaniyya a duniya. Taron ya kasance babban taro na addini mai ɗauke da tarihi da muhimmanci ga al’ummar Musulmi, musamman mabiya ɗariƙar Tijjaniyya.  Taron, wata muhimmiyar dama ta tunatarwa da ilimintarwa da ƙarfafa zumunci tsakanin al’ummar Musulmi. Haka kuma, ya sake tabbatar da matsayi da muhimmancin birnin Kano a matsayin…
Read More
’Yan jarida na iya gina ko rushe dimokuraɗiyya — Sarkin Dutse

’Yan jarida na iya gina ko rushe dimokuraɗiyya — Sarkin Dutse

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Sarkin Dutse na Jihar Jigawa, Dr Hameem Nuhu Sanusi, ya nuna damuwa kan yadda wasu mutanen da ba su da cikakken horo ko ƙwarewar aikin jarida ke kutsawa cikin sana’ar, yana mai cewa ayyukansu na lalata martabar aikin jarida. Sarkin ya bayyana hakan ne yayin da ya karɓi baƙuncin Shugaban ƙungiyar ’Yan Jarida ta Nijeriya (NUJ), Kwamared Alhassan Yahaya, tare da mambobin Majalisar Zartarwa ta ƙasa (NEC) ta ƙungiyar, waɗanda suka kai masa ziyarar ban girma a fadarsa da ke Dutse. Tawagar NUJ ta je Dutse ne domin halartar taron NEC na ƙungiyar da ake gudanarwa…
Read More
Tsohon ɗan dambe Prichard Colón ya rasu yana da shekaru 33

Tsohon ɗan dambe Prichard Colón ya rasu yana da shekaru 33

Tsohon dan damben Puerto Rico, Prichard Colón, ya rasu yana da shekaru 33, kusan shekaru 11 bayan wani mummunan faɗa da ya janyo masa zubar jini a kwakwalwa. Colón ya rasu ne ranar Alhamis, 13 ga Agusta, 2026, bayan ya shafe tsawon lokaci cikin wani yanayi na rashin cikakken sanin abin da ke faruwa a jikinsa sakamakon raunin da ya samu. Mahaifinsa kuma tsohon mai horar da shi, Richard Colón, ne ya sanar da rasuwarsa a wani saƙo da ya wallafa a Facebook. Kafin hatsarin da ya sauya rayuwarsa, Colón na daga cikin fitattun ‘yan damben da ake sa ran…
Read More
An naɗa tsohon jakadan Najeriya a Majalisar Ɗinkin Duniya uban ƙasar Besse

An naɗa tsohon jakadan Najeriya a Majalisar Ɗinkin Duniya uban ƙasar Besse

Daga MUHAMMAD SADISU ABUBAKAR Birnin Kebbi Mai martaba sarkin Gwandu Alhaji Muhammadu Iliyasu Bashar ya naɗa tsohon jakadan Najeriya a Majalisar Ɗinkin Duniya Farfesa Tijjani Muhammad Bande a matsayin Baraden Besse, uban ƙasar Besse, da ke Jihar Kebbi. Gwamnan Kebbi mai ci yanzu , Nasir Idris, tare da tsohon gwamnan jihar, Atiku Bagudu, wanda a yanzu shine ministan kasafin kuɗi da tsarin tattalin arziki, da kuma tsohon gwamnan jihar, Jakada Sa'idu Dakingari da kuma tsohon gwamnan jihar, yanzu kuma ɗan majalisar dattijai mai wakiltar Kebbi ta tsakiya, Muhammadu Adamu Alieru, sun halarci wurin bikin naɗin sarautar, wanda aka yi a…
Read More
Gidauniyar Mangal ta fara tantance masu lalurar fitsari domin yi masu magani kyauta a Katsina

Gidauniyar Mangal ta fara tantance masu lalurar fitsari domin yi masu magani kyauta a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Gidauniyar Dahiru Bara'u Mangal ta fara aikin tantance marasa lafiyar da suka samu wannan dama, inda ake gudanar da gwaje-gwaje domin gano irin matsalar da kowanne mara lafiya ke fama da ita da kuma tantance waɗanda suke buƙatar aikin tiyata ko magani. Sama da mutane 120 ne ake sa ran za su amfana da aikin, wanda za a gudanar da shi kyauta ba tare da marasa lafiyar sun biya kuɗin magani ko aikin tiyata ba. Da yake bayyana yadda shirin yake, ɗaya daga cikin ’yan Kwamitin Amintattu na Gidauniyar Hussaini Kabir, ya bayyana cewa tun…
Read More
Gamayyar jam’iyyun siyasa takwas a Zamfara sun yi Allah wadai da taron IPAC

Gamayyar jam’iyyun siyasa takwas a Zamfara sun yi Allah wadai da taron IPAC

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Gamayyar jam'iyyun siyasa takwas a Jihar Zamfara ta nisanta kanta daga wani taron manema labarai da wasu mambobin gammayyar jam'iyyun siyasa IPAC reshen Jihar da ke ayyana kan su a matsayin shugabannin IPAC a jihar su ka yi. Da yake jawabi ga manema labarai a yau Asabar a Gusau, Ambasada Adamu Haruna Tsafe, ya ce ƙungiyar ta damu da wannan bayanin, wanda suka lura an yi shi ne da nufin cin zarafi ga manufofi da shirye-shiryen gwamnatin jihar. Gamayyar ta ƙunshi wakilan jam'iyyun siyasa na AA, NNPP, SDP, ZLP, AAC, LP, YPP da APP. A…
Read More
Zamfara: Jigo a APC ya fice daga jam’iyyar sakamakon rashin kawo ƙarshen ‘yan bindiga

Zamfara: Jigo a APC ya fice daga jam’iyyar sakamakon rashin kawo ƙarshen ‘yan bindiga

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Wani fitaccen ɗan jam'iyyar APC a ƙaramar hukumar Maradun, Hon. Muhammad Bello Yakubu Bakyasuwa, ya yi murabus daga jam'iyyar nan take, yana zargin gwamnatin tarayya da sakaci da rashin tsaro a jihar Zamfara. A cikin wata wasiƙar murabus da ya aike wa shugaban APC a Dosara/Birnin Kaya Ward, Bakyasuwa ya ce shawarar da ya yanke na ƙashin kansa ne da kuma rashin gamsuwa da gwamnatin APC ta Shugaba Bola Ahmed Tinubu. Bakyasuwa ya yi nuni da ci gaba da kai hare-hare a Zamfara, yana mai cewa ya yi murabus ne saboda gazawar gwamnatin tarayya da…
Read More