ukarofi

11213 Posts
Yan bindiga sun hallaka mutane 9, sun ƙone motoci 9 da wasu gidaje a Katsina

Yan bindiga sun hallaka mutane 9, sun ƙone motoci 9 da wasu gidaje a Katsina

'Daga Umar Garba a Katsina 'Yan bindiga ɗauke da muggan makamai sun yi dirar mikiya a garin Mai Dabino dake ƙaramar hukumar Ɗanmusa ta jihar Katsina inda suka kashe mutane tara(9) suka ƙone gidaje huɗu (4) da motocin 'yan kasuwa tara (9) tare da yin garkuwa da mata da ƙananan yara fiye da hamsin a yayin harin da suka kai a garin na Mai Dabino. Wani mazaunin garin ya shaidawa Blueprint Manhaja cewa 'yan ta'addar sun kutsa kai da misalin ƙarfe goma na dare, inda suka shafe kimanin sa'o'i bakwai suna ta'addanci a garin sun kashe mutane tare da ƙone…
Read More
Shekara 52 da kafuwa: ‘Yan Tifa a Gombe sun buƙaci tallafi daga gwamnati

Shekara 52 da kafuwa: ‘Yan Tifa a Gombe sun buƙaci tallafi daga gwamnati

Daga MOHAMMED ALI a Gombe Ƙungiyoyin hadin Kan Leburorin Motocin Tifa na Awala sama da mutum dubu goma da ke Jihar Gombe suna roƙon Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya da ya kawo musu tallafin gaggawa don ciyar da dubban dattawan ƙungiyar da ƙarfinsu ya ƙare. Har ila yau, suna kuma tunatar da Gwamna akan alƙawuran da ya yi na tafiya tare da su wajen ƙara musu ƙarfin gwiwa kamar sauran ƙungiyoyin jihar. Waxannan koke-koke sun fito ne daga bakin sabon zaɓaɓɓen shugaban ƙungiyar Alhaji Abubakar Bose lokacin da yake hira da ’yan jaridu, jim kaxan bayan an rantsar da shi a…
Read More
IPAC ta zaɓi sabbin shugabanni a Kaduna

IPAC ta zaɓi sabbin shugabanni a Kaduna

Daga MAHDI M. MUHAMMAD An zaɓi sabbin shugabannin Gamayyar Jam'iyyu ta 'Inter Party Advisory Council' (IPAC), reshen Jihar Kaduna. An zaɓi Ahmad Tijani Mustapha ne a matsayin shugaba ba tare da hamayya ba, tare da wasu mutane takwas yayin zaɓen da aka gudanar a hedikwatar hukumar INEC ta Kaduna da yammacin ranar Litinin. Sabon Shugaban IPACɗin, Honarabul Tijani Mustapha, shi ne shugaban jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) na jihar Kaduna. A jawabin godiya bayan zaɓen, sabon shugaban, ya gode wa kwamitin zaɓe na IPAC, sakataren gudanarwa na INEC, ma’aikata da mambobin IPAC bisa gagarumin goyon baya da amincewar da suka…
Read More
Kasuwancin aya da dabino ke samar mana da rufin asiri – Alhaji Auwalu

Kasuwancin aya da dabino ke samar mana da rufin asiri – Alhaji Auwalu

Daga DAUDA USMAN a Legas Shugaban Ƙungiyar Masu Sana'ar Kasuwancin Aya da Dabino a Kasuwar Mile12 da ke Jihar Legasa, Alhaji Auwalu Mai Dabino ya bi sahun 'yan uwansa 'yan kasuwa masu wannan sana'ar wajen ƙorafin cewa rufe shingogin tsakanin iyakar Nijeriya da Jamhuriyar Nijar ya ƙara taɓarɓara kasuwar aya da dabino a Legas. Alhaji Auwalu ya cigaba da shaida wa Jaridar Manhaja a Legas halin da 'yan kasuwar aya da dabino su ke ciki a Legas dangane da wannan al'amari. Shugaban ƙungiyar ya ce, tun daga lokacin da Nijeriya ta rufe iyakokin tsakaninta da ƙasar Nijar harkokin kasuwancinsu na…
Read More
Sirrin kyauta da illar rowa ga ruhi da rayuwa!

Sirrin kyauta da illar rowa ga ruhi da rayuwa!

Tare da ALI ABUBAKAR SADEEQ Halifan Musulunci mafi shahara cikin jerin halifofin gidan Abbas (wato Abbasid ko muce Abasiyawa da hausa), wato Harun Al Rashid, ba'a taba samun mai kyauta irinsa ba. Shine halifan da kusan duk dare sai ya yi bad-da-kama ya shiga lungunan garin Bagadaza domin ganewa idonsa yadda talakawa ke rayuwa da zakulo mabukata domin tallafa musu. Rayuwarsa ce ta zama shahararren labarin nan na "Dare dubu da daya". Wata rana wani wazirinsa ya ce ya Amirul Muminun, ya aka yi kake da kyauta da karimci haka, sai ya dube shi ya ce "Kyauta ta zamto a…
Read More
Yaƙi da cutar Kwalara

Yaƙi da cutar Kwalara

A Nijeriya, an sake samun ɓullar cutar Kwalara da ta yi sanadin mutuwar mutane da dama tare da jikkata wasu sama da dubu a faɗin jihohin ƙasar. Alƙaluman baya-bayan nan da Hukumar Yaƙi da Cututtuka Masu Yaɗuwa ta Nijeriya NCDC ta fitar, sun bada wani rahoto mai muni na kamuwar mutum 1,141 da cutar, sannan 30 sun mutu a ƙananan hukumomi 96 a cikin jihohi 30. Wannan lamari da ya shafi lafiyar jama'a gabaɗaya, akwai gazawar tsarin samar da tsaftataccen ruwa da tsaftar muhalli. Jihohin da suka fi fama da wannan annoba – Bayelsa, Zamfara, Abia, Kuros Ribas, Bauchi, Delta,…
Read More
Ya kamata Rabi’u Musa Kwankwaso ya iya bakinsa – APC

Ya kamata Rabi’u Musa Kwankwaso ya iya bakinsa – APC

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Jamiyyar APC mai mulki a Nijeriya ta ce bai kamata tsohon gwamnan jihar Kano kuma ɗan takarar shugabancin ƙasar na jam'iyyar NNPP a zaɓen 2023 Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya riƙa yin kalamai sakaka, ba tare da kame baki da lura da abin da zai iya haifarwa a kan lamarin jihar Kano ba. Jam'iyyar ta ce a matsayin Kwankwaso na dattijo a ƙasa kamata ya yi ya mayar da hankalinsa kan lalubo duk wata hanya ta siyasa da lumana don magance rikicin masarautar jihar maimakon rura wutar dambarwar. Kiran na kunshe ne a martanin…
Read More
’Yan PDP 4,400 sun sauya sheƙa zuwa APC a Binuwai

’Yan PDP 4,400 sun sauya sheƙa zuwa APC a Binuwai

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Mambobin Jam’iyyar adawa ta PDP kimanin 4,450 sun sauya sheƙa zuwa APC mai mulki a Jihar Binuwai. Masu sauya sheƙar da suka fito ne daga ƙananan hukumomin Katsina-Ala, Ukum, Logo, Kwande da kuma Ushongo sun koma APC ne a ranar Talata. Gwamnan jihar, Hyacinth Alia, ne ya karɓe su a wani biki a yayin da yake gudanar da rangadin godiya ga al’ummar jihar. Gwamnan yana yin zagaye a ɗaukacin ƙananan hukumomin jihar ne domin nuna godiyarsa bisa goyon bayan da ya samu har ya lashe zaɓen 2023. A jawabinsa a wurin karɓar masu sauya…
Read More
Ya kamata Tinubu ya yi taka-tsan-tsan da tsoma baki a siyasar Kano -Buba Galadima

Ya kamata Tinubu ya yi taka-tsan-tsan da tsoma baki a siyasar Kano -Buba Galadima

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Wani jigo a Jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP), Buba Galadima, ya buƙaci Shugaba Bola Tinubu da ya yi taka-tsan-tsan wajen tsoma baki a siyasar jihar Kano. Galadima ya bayyana haka ne a wata hira da ya yi da gidan talabijin na Arise a ranar Litinin. Ya ce, “Ya kamata gwamnatin tarayya da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu su yi taka-tsan-tsan da shiga siyasar Kano. Zai lalata shugabancinsa.” Ya yi Allah wadai da goyon bayan da gwamnatin tarayya ke baiwa wata ƙungiya a siyasar Kano, yana mai cewa bai kamata hukumomin tarayya su karkata kan…
Read More
Tarihin hawan Sallah a Ƙasar Hausa

Tarihin hawan Sallah a Ƙasar Hausa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Hawan Sallah wata al'ada ce da ta daɗe a tarihin Masarautun Ƙasar Hausa. Masarautar Kano: A wannan masarauta, akwai hawan sallah da ake yi duk shekara a lokacin ƙarama da kuma babbar sallah. Bayanai na cewa Muhammadu Rumfa ne ya assasa tsarin hawan sallah a Kano. Daga cikinsu akwai Hawan ranar sallah da Hawan Nasarawa da Hawan Ɗorayi da Hawan Daushe da Hawan Fanisau. Sai dai daga cikin waɗannan haye-haye da ake yi a Masarautar Kano, guda biyu ne suka fi jan hankali. Hawan Nassarawa: Yayin wannan hawan, sarki na zuwa gidansa da ke Nassarawa daga…
Read More