ukarofi

11455 Posts
Shugaba Ruto na Kenya ya sallami ministocinsa

Shugaba Ruto na Kenya ya sallami ministocinsa

Shugaban ƙasar Kenya, Ruto ya sallami sukkan ministocinsa. Wannan na zuwa ne bayan shafe satuka da akai ana ta zanga zanga a ƙasar. Amma wannan sauyin bai shafi ofishin mataimakin shugaban ƙasa ba da sakataren ministocin. Ya cigaba da cewa, za suyi gana sosai da mutane da dama domin samun shawarwari ta yadda za a kafa gwamnati mai inganci. Wadda zasu shawo kan bashin da ke damun ƙasar, samar da ayyukan yi da yaƙi da cin hanci
Read More
An karɓe ikon Sarkin Musulmi kan hakimansa

An karɓe ikon Sarkin Musulmi kan hakimansa

Majalisar Sarkin Musulmi sun cire masa ikon naɗa hakimai a jihar, yayin da Gwamna Aliyu Ahmed ya sanya hannu a dokar da ta ba da ikon haka. Wannan dokar, ta cire wa sarkin Musulmin duk wani iko na naɗa hakimai da dagatai a faɗin Jihar Sokoto. Yayin bikin ƙaddamar da dokar, gwaman yace ba anyi dokar bane don muzantawa wani, sai dai domin ƙarfafa mulkin dimukraɗiya a faɗin Jihar. Ya cigaba da cewa, malamai da sarakunan gargajiya su daina bari yan siyasa suna amfani dasu wajen cin ma manufofinso na siyasa. A ranar dai ya sanya hannu ga dokar da…
Read More
Matsayin gara a mahangar magabata 

Matsayin gara a mahangar magabata 

(Ci gaba daga makon jiya) Daga AISHA ASAS  Mai karatu barkanmu da sake ganin zagayowar sati lafiya. Idan ba mu manta ba, kuma kuna biye da jaridar Manhaja, a makon da ya gabata, mun ɗauko bayani kan kayan da ake kai gidan miji da ke da suna gara a al'adance. Mun faro bayanin kan irin kallon da ma'anar da take da shi a tsakanin al'ummarmu, musamman ma a Ƙasar Hausa. Inda muka yi bayanin yadda muhimmancin ta ke rasiri a zamantakewar aure a wasu lokuta.  Mun yi bayanin yadda barin ta yafi zama alheri da wasu hujjojin da muka kawo,…
Read More
Shugaba Tinubu ya yi maraba da hukuncin Kotun Ƙoli kan cin gashin ƙananan hukumomi

Shugaba Tinubu ya yi maraba da hukuncin Kotun Ƙoli kan cin gashin ƙananan hukumomi

Shugaba Tinubu yayi maraba da hukuncin kotun ƙolin a kan cin gashin kan ƙananan hukumomi Shugaba Tinubu ya nuna murna ƙwarai dagaske a kan hukuncin da kotun ta yanke na ba ƙananan hukumomi damar cin gashin kansu. Wannan ya fito ne a wata sanarwa daga mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkar sadarwa, Ajuri Ngelale. Ya bayyana cewa wannan hukuncin ya bayyana irin ƙudurin da gwamnatin sa ke da shi wajen ganin mun bi doka a tsarin gyaran da muka zo dashi" Ya cigaba da cewa wannan ya zama dole saboda ƙananan ayyuka irin su saka fitilar titi, gyaran wasu…
Read More
An dakatar da shari’ar tsohon ministan Buhari bayan ya yanke jiki ya faɗi a harabar kotu

An dakatar da shari’ar tsohon ministan Buhari bayan ya yanke jiki ya faɗi a harabar kotu

An dakatar da shari'ar tsohon ministan wuta, Saleh Mamman a babbar koto dake Abuja saboda bashi da cikakkiyar lafiya. Tsohon ministan zai gurfana ne yau domin cigaba da shari'ar sa, amma ya yanke jiki ya faɗi. Wanda lauya mai kare shi, ya sanar Alƙalin halin da ake ciki lokacin da aka kira shari'ar. Tsohon ministan ya bayyana a gaban kotun ne, da kayan sa a jiƙe, wanda ya sanya alƙalin ya tambaye ko ruwa ake a waje. Mai shari'a Okong,ya tambayi tsohon ministan ko zai iya cigaba da tsayuwa, wanda yace zai iya. Ya faɗi ne saboda maganin da ya…
Read More
Sanata Kawu Sumaila ya gabatar da ƙudirin ƙirƙirar sabuwar Jiha daga Kano

Sanata Kawu Sumaila ya gabatar da ƙudirin ƙirƙirar sabuwar Jiha daga Kano

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Akwai yiwuwar samar da sabuwar jiha nan ba da jimawa ba, sakamakon yadda aka gabatar da ƙudirin kafa jihar Tiga daga Kano a majalisar dattawan Najeriya. Ƙudurin dokar wanda Sanatan Kano ta kudu Suleiman Abdurrahman Kawu Sumaila ya gabatar, wanda aka yi masa karatu na farko a ranar 10 ga Yuli, 2024. Ƙudirin doka mai taken “Constitution of the Federal Republic of Nigeria, 1999 (Alteration) Creation of Tiga State Bill, 2024 (SB.523)” na da nufin raba jihar Kano zuwa jihohi biyu, inda Tiga za ta zama sabuwar jihar da za a ƙirƙireta daga Jihar kano…
Read More
Majalisa na zargin Ministar Mata da kashe miliyan N75 wajen sayen ƙunzugun mata

Majalisa na zargin Ministar Mata da kashe miliyan N75 wajen sayen ƙunzugun mata

Ana zargin ministar harkokin mata ta Tinubu Uju Kennedy, da almundahana kuɗi kimanin naira miliyan 20 wajen sayen ƙunzugu na mata da kuma naira miliyan 45 wajen bikin sabuwar shekara. Wannan ya fito ne lokacin da aka gayyaceta majalisa domin tuhumar rashin biyan yan kwangila kuɗinsu, kimanin biliyan 1.5 bayan gwamnati ta biya wannan kuɗin. Amma minstar ta musanta zargin hakan, tace ya faru ne lokacin tsohuwar gwamnati. Tuhumar ta samo asali ne lokacin da ɗan kwangilar ya shigar da koke gaban majalisa. Akan ayyukan da yayi kuma an kasa biyanshi haƙƙinshi.
Read More
Gwamnatin Dauda za ta gina tashar mota ta zamani a Gusau

Gwamnatin Dauda za ta gina tashar mota ta zamani a Gusau

Gwamnan Jihar Zamfara ya amince da fara ginin sabuwar tashar mota na zamani a cikin Gusau, wanda takai kimanin N4,854,135,954.53. Aikin kwangilar a bada shi ga Fieldmark Construction ltd. Wannan na ɗaya daga cikin ayyukan raya birni wanda gwamnatin sa ke aiwatar wa. Wannan ya faru ne, a ranar Talata yayin zaman majalisar gudanarwa na gwamnatin, kamar yadda mai magana da yawun Gwamnan,Sulaiman Bala Idris ya shaida. Yace majalisar ta zanta akan abubuwa da dama wanda suka shafi cigaban mutanen Jihar Zamfara. Ma'aikatar ayyuka tare da Ma'aikatar Ƙananan Hukumomi su zasu ɗauki nauyin biyan wannan aiki. Sabuwar tashar za ta…
Read More
An kama ɗan shekara 80 da yin lalata da ‘yar shekara 10 a Bayelsa

An kama ɗan shekara 80 da yin lalata da ‘yar shekara 10 a Bayelsa

'Ƴan sanda a Jihar Bayelsa sun yi nasarar cafke wani dattijo mai shekaru 80 da zargin yin lalata da yar shekara 10. Lamarin ya faru a Otuakpoti dake ƙaramar hukumar Ogbia a Jihar Bayelsa. Mai magana da yawun yan sanda na Jihar, ASP Musa Muhammad ya tabbatar da faruwar lamarin, inda yace tuni an miƙa lamarin sashen binciken manyan laifuka domin cigaba da bincike. Bayanai sun nuna cewa, dattijon ya jima yana lalata da yarinyar har tsawon wata 12 kafin dubun shi ta cika. An sami nasarar cafke tsohon ne da taimakon wata ƙungiya mai rajin kare haƙƙin mata.
Read More