22
Jun
Daga MAHDI M. MUHAMMAD Yayin da kasuwanni da buƙatuwar kayayyakin amfanin gona ke cigaba da ƙaruwa, kwararrun Nijeriya a fannin noma sun yi kira da a samar da ƙa'idoji na ayyukan noma a Nijeriya. Da yake magana a ranar Litinin yayin wani taron masu ruwa da tsaki, Manajan Shirin Abinci da Noma na ActionAid Nigeria, Azubike Nwokoye, ya bayyana cewa ƙasar na yin asarar kusan dala miliyan 362.5 a duk shekara a kuɗaɗen musaya na ƙasashen waje sakamakon hana fitar da wake. A cewar Azubike, ilimin aikin gona na iya rage tarzoma a nan gaba na wadatar abinci a ƙasar…
