ukarofi

11213 Posts
Gwamnatin Tarayya ta sanar da 12 ga Yuni a matsayin hutun Ranar Dimukraɗiyya

Gwamnatin Tarayya ta sanar da 12 ga Yuni a matsayin hutun Ranar Dimukraɗiyya

Gwamnatin Tarayya ta sanar da 12 ga Yuni a matsayin hutun Ranar DimukraɗiyyaMinistan harkokin cikin gida, Hon.Dr Olubunmi Tunji Ojo ya fitar da sanarwa yana mai cewa " yayin da muke murnar zagoyowar ranar dimukraɗiya a tarihin ƙasar mu. Yana da kyau muyi waiwaye domin ganin yadda magabatan mu suka jajirce don ganin Najeriya ta zama tsintsiya maɗaurinki ɗaya.Ministan ya ƙara da cewa, Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu yana iya bakin ƙoƙarinsa don ganin kawo canji ga tattalin arziki da tsaron kasa.Ministan yayi kira ga yan Najeriya da abokan ta da su yi alfahari da ita ganin yadda ta cigaba…
Read More
Yan Ta’adda sun kai hari a sansanin sojoji da ke jihar Niger

Yan Ta’adda sun kai hari a sansanin sojoji da ke jihar Niger

Aƙalla sojoji biyu ne suka samu raunuka lokacin da wasu yan ta'adda suka kai wani hari a sansanin sojoji da ke Tegina, karamar hukumar Rafi jihar Niger An kashe dan ta'adda ɗaya yayin musayar wuta da sojojin. Wasu majiya sun bayyana cewa yan ta'addan na shirin tsallakawa ne daga ƙaramar hukumar Wushishi zuwa Mashegu lokacin da suka kai harin. Alhaji Ayyuba Usman Katako, shugaban ƙaramar hukumar Rafi, ya tabbatar da faruwar al'amarin in da yace sojojin da suka samu raunuka na Asibitin IBB da ke Minna domin samun kulawa.
Read More
Shekara Guda: Wacce rawa Shettima ke takawa a Gwamnatin Tinubu?

Shekara Guda: Wacce rawa Shettima ke takawa a Gwamnatin Tinubu?

Daga STANLEY NKWOCHA Shekara  guda kenan da rantsar da Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu (GCFR), wato a ranar 29 ga Mayu, 2023, kuma nan take ya ɗauki alwashin samar da sauye-sauyen da za su bayar da sakamakon da zai sauya akalar harkokin mulki a Najeriya baki ɗaya. Kuma mun gani a ƙasa, domin a shekara guda na mulkinsa ya qaddamar da ƙudurorinsa ƙarƙashin taken ajandodi 8 na Sabunta-Fata, wanda suka tafi kafaɗa-da-kafaɗa da alƙawuran da ya ɗauka a lokutan yaƙin neman zaɓensa. Wato abin nan da ake kira aiki da cikawa. Duk da abu ne mawuyaci a yi wa gwamnatin…
Read More
Ina son labaran abin da ya shafi aljanu da almara – Ameera Adam

Ina son labaran abin da ya shafi aljanu da almara – Ameera Adam

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Aisha Adam Hussaini wacce a fagen rubutu aka fi sani da Ameera Adam, ita ce Gwarzuwar Gasar Hikayata ta BBC Hausa ta shekarar 2023. Marubuciyar labaran hikayoyi da almara, wacce Allah Ya yi wa baiwar sarƙafa labari cikin hikima da basira, kai ka ce a zamanin Barbushe take ko cikin Daular Ifiritai. Ƴar baiwa ce ta nunawa a fadar Sarki, domin kuwa babu wata gasar marubuta adabi da ake shiryawa wacce in Aisha ta shiga ba ta samun nasara, don haka ne ma nasarar ta a Gasar Hikayata ba ta zo wa mutane da dama a…
Read More
Sabbin hare-haren Isra’ila a Rafah sun sake fusata duniya – Shawesh

Sabbin hare-haren Isra’ila a Rafah sun sake fusata duniya – Shawesh

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Jakadan Falasɗinu a Nijeriya, Abdullah Abu Shawesh ya bayyana cewa a rana ta 237 da aka fara kisan ƙare dangi a kan al'ummar Falasɗinu, a bayyana yake ƙarara cewa ana amfani da dokokin ƙasa da ƙasa ne kawai a ƙasashen kudanci.Abu Shawesh ya bayyana hakan ne a wata sanarwar manema labarai da ya fitar, ranar Alhamis.Ya ce, "ya zuwa ranar Talata 29 ga watan Mayu, an samu Falastinawa shahidai 36,096 da kuma 81,136 da suka jikkata, inda kusan dubu 10 suka ɓace a qarqashin ɓaraguzan ginin da ƙungiyoyin ceto ba su yi nasarar kai wa ba…
Read More
Majalisar wakilai ta gabatar da ƙudurin wa’adin mulkin shekara shida ga Shugaban ƙasa da gwamnoni.

Majalisar wakilai ta gabatar da ƙudurin wa’adin mulkin shekara shida ga Shugaban ƙasa da gwamnoni.

Wata ƙungiyar 'yan majalisar wakilai 35 ta gabatar da ƙudurin wa'adin mulki na shekaru shida ga Shugaban ƙasar Najeriya da ma gwamnonin jihohi.'Yan majalisar sun kuma ya ce ya kamata a riƙa gudanar da zaɓukan muƙaman siyasa a rana guda, don kuɓutar da ƙasar daga kashe maƙudan kudaɗe wajen gudanar da zaɓe.Mai magana da yawun ƙungiyar, Hon., Ikenga Imo Ugochinyere, wanda ya jagoranci sauran mambobin ƙungiyar, ya bayyana shida daga cikin ƙudurin doka hamsin, wanda wasu daga cikinsu sun riga sun tsallake karatun farko, a yayin zantawa da manema labarai a Abuja a ranar Litinin.
Read More
Ƙungiyar wakilan kafafen yaɗa labarai ta ƙasa, ta ƙauracewa dukkanin wasu harkoki na gwamnatin Kano, nan take.

Ƙungiyar wakilan kafafen yaɗa labarai ta ƙasa, ta ƙauracewa dukkanin wasu harkoki na gwamnatin Kano, nan take.

Daga Ibrahim Hamisu, Kano Kungiyar wakilan kafafen yaɗa labarai ta ƙasa, ta ƙauracewa dukkanin wasu harkoki na gwamnatin Kano, nan take. Hakan na ƙunshe cikin sanarwar da shugaban ƙungiyar Aminu Ahmed Getso ya sanyawa hannu a litinin din nan. Getso ya bayyana kyara, cin mutunci da tsangwama da ya ce wakilan nasu na fuskanta daga gwamnati da wakilanta yayin gudanar da aiyukansu a fadin jihar. Kazalika ƙungiyar ta koka kan yadda ta ce, gwamnatin na amfani da waɗanda ba yan yaridu ba wajen ɗaukar harkokin gwamnati, maimakon barin yan jaridu su yi aikinsu bisa ƙwarewa. A saboda haka ne ƙungiyar…
Read More
Sarakunan gargajiya da aka tsige a tarihin Nijeriya

Sarakunan gargajiya da aka tsige a tarihin Nijeriya

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Mutane da dama suna tunanin cewa rikicin masarautar Kano ne karon farko da aka fara tsige sarkin gargajiya a tarihin Nijeriya, amma hakan ba gaskiya ba ne domin kuwa an sha tsige sarakuna a tarihi, wanda ya sa jaridar Blueprint Manhaja ta ga ya dace ya kawo tarihin tsige sarakuna a Nijeriya. Ooni na Ife – Ogboru: Ogboru shi ne aarni na 19 Ooni na Ife wanda sarakunan fadar Ife suka tsige daga gadon sarauta bisa zalunci wanda aka gaji da mulkinsa na shekaru 70. An yaudare shi da dabara ya fito daga wurinsa ya zo…
Read More
Yadda za a samu maslaha tsakanin surukai (2)

Yadda za a samu maslaha tsakanin surukai (2)

Barkanmu da jimirin karatun jaridarku mai farin jini ta Manhaja. Za mu ci gaba daga inda muka tsaya a kan dalilan da suke kawo lalacewar alaƙa tsakanin surukai. Kamar yadda muka faɗa a makon da ya gabata, surukuta a ƙasar Hausa ta zama kamar gaba a tsakaninsu. Kowa kishi da hassada yake wa ɗanuwansa. Ga rainin wayo, abin ba a magana.A makon da ya gabata mun fara kawo wasu daga cikin dalilan da suka sa hakan take faruwa domin masu karatu su yi alƙalanci su gano wai shin ma laifin wanene? To a yanzu za mu ci gaba da kwararo…
Read More