ukarofi

11627 Posts
Hattara masu zance a mota

Hattara masu zance a mota

Tare da MUSTAPHA IBRAHIM ABDULLAHI Ina masu yin tadi ko zance a cikin mota tare da kunna ‘air conditioner’ da zuge gilashi? To, ku matso ku ji. Yin hakan yana da haɗari. Haɗarin shi ne idan iskar carbon monoxide da ya kamata ta tafi silencer ta samu kafa take shigowa cikin motarka. Mene ne illar hakan? Ku biyo ni. A baya bayannan anan jihar Kano, an samu gawar wani mutum da wata mace a cikin mota sun mutu, sai da akayi dabaru wajen cire su daga motar saboda sun fara lalacewa. Abinda ya faru shi ne shi namijin ya kunna…
Read More
Idan ka zama sakarai

Idan ka zama sakarai

Daga ALI ABUBAKAR SADIƘ Idan ka zama sakarai, babu abinda ba za a yi ma ka ba. Sakamakon zama sakarkaru, saboda hassada da haɗama a arewacin Najeriya mu na ji muna gani an kassara mu ta ko'ina. An cuso ma na Boko Haram ta mummunar akidar addini ta rashin hakuri da juna (tolerance) wadda ya kassara Arewa maso Gabas. Da aka ga aƙidar Boko Haram ba za ta karɓu a Arewa maso Yamma ba sai aka fara far ma Fulani a ko'ina suke, ana kashewa da ƙone mutanensu da dabbobinsu, wanda ya haifar mana da banditry da kama mutane domin…
Read More
Me ya sa shahararrun mata ke wahalar auruwa?

Me ya sa shahararrun mata ke wahalar auruwa?

Daga MUHAMMAD TAJAJJINI DAN TIJJANI Abokina Sulaiman Badamasi ya yi tambaya a shafinsa na Fesbuk kamar haka: Me ya sa shahararrun mata ke wahalar auruwa? Mata da yawa a nan Social Media masu tarin mabiya, masu son addini, kyawawa, su na posting abubuwa masu amfani. Idan sun yi comment ko su ka sanya hoto, cikin ƙanƙanin lokaci za ka ga comments na yabo fiye da 1,000. Me ya sa duk da wannan yabon da maza suke yi musu, suke daɗewa babu aure? Me ya sa ba a auran su? Ga amsar da na ba shi: Ingiza Mai Kantu Ruwa ake…
Read More
Arewa Media Writers ta shawarci gwamnoni kan martaba sarakuna da tsaro

Arewa Media Writers ta shawarci gwamnoni kan martaba sarakuna da tsaro

Daga Abba Abubakar Yakubu A ƙarshen Babban taron Ƙungiyar Arewa Media Writers Association da ta gudanar a garin Kaduna, an shawarci gwamnonin Arewa su kaucewa zubar da darajar sarautun gargajiya, saboda bambancin ra'ayin siyasa abin da ƙungiyar ke ganin rashin kishin Arewa ne ke haifar da haka. Ƙungiyar ta bayyana haka ne cikin takardar jawabin bayan taron da ta yi da shugabannin ƙungiyar a matakin ƙasa da jihohi, ƙarƙashin jagorancin sabon shugaban ƙungiyar na ƙasa Kwamred Haidar Hasheem Kano, inda ta fitar da wasu muhimman ƙudirori goma sha ɗaya. Kungiyar ta yi kakkausan suka ga abin da ta ce, wasa…
Read More
Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi Allah wadai da harin ƙunar bakin wake a Gwoza

Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi Allah wadai da harin ƙunar bakin wake a Gwoza

Ko’odinetan Majalisar Ɗinkin Duniya a Nijeriya, Mohamed Malick Fall, ya fitar da wata sanarwa inda ya yi kakkausar suka kan harin ƙunar bakin wake da aka kai kan fararen hula a Ƙaramar Hukumar Gwoza da ke Jihar Borno. Hare-haren da suka auku a ranar Asabar, 29 ga watan Yuni, sun yi sanadin asarar rayuka da har yanzu ba a san adadinsu ba, inda rahotanni ke nuni da cewa an kashe mutane da dama tare da jikkata wasu da dama .“Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi kakkausar suka kan harin kunar bakin wake da aka kai kan fararen hula a Ƙaramar hukumar Gwoza…
Read More
Da ƊUMI-ƊUMI: Gwamna Raɗɗa ya rubuta takardar tuhuma ga Sarkin Katsina

Da ƊUMI-ƊUMI: Gwamna Raɗɗa ya rubuta takardar tuhuma ga Sarkin Katsina

Gwamnan Katsina, Dikko Raɗɗa ya rubuta takardar tuhuma ga Sarkin Katsina Abdulmumini Kabir Usman. Wannan al'amari ya jawo mutane da dama na tunanin kar abinda ya faru Jihar Kano da Sokoto ya maimaita kan shi a Jihar. Dalilin wannan tuhuma shine, rashin zuwa hawan Sallah da wasu masu anguwanni ba suyi ba sati biyu da ya wuce. Wannan a na ganinshi kamar rashin bin doka ne da kuma rashin ɗa'a ga martabar masarauta. Duk da haka wasu suna tunanin dalilin yafi wannan. Gwamna Raɗɗa na tunnain ƙarfin masarautun yayi yawa. Don haka dole ya rage masu ƙarfi ta hanyar yin…
Read More
Fitaccen likitan ido a Arewa, Umar Ɗanladi Kilishi ya rasu

Fitaccen likitan ido a Arewa, Umar Ɗanladi Kilishi ya rasu

Daga USMAN NASIR KAROFI a Abuja Alhaji Umar Ɗanladi Kilishi, ɗaya daga cikin ƙwararrun likitocin idanu daga arewacin Najeriya, ya rasu jiya Asabar a garin Kaiama da ke arewacin Jihar Kwara. Marigayi Alhaji Kilishi yi aiki a asibitoci daban-daban a Kano, New Bussa da Ilorin.Sanarwar rasuwarsa ta fito ne daga bakin babban ɗansa, Mallam Ismaila Umar. A lokutan da Arewacin Nijeriya ke fama da ƙarancin likitocin ido, Alhaji Umar Danladi Kilishi ya ziyarci asibitoci daban-daban a Nijeriya, domin yi wa masu ciwon ido aiki. Marigayi likitan ido Kilishi, wanda a turance ana kiran su ‘Ophthalmologist’, ya rasu ya bar ‘ya’ya…
Read More
 Tsaftar muhalli don kawar da cutar kwalara

 Tsaftar muhalli don kawar da cutar kwalara

Harkar lafiya a Nijeriya ta sake faɗawa cikin wani yanayi mai wuyar gaske, sakamakon ɓullar annobar kwalara, wacce aka fi kira da cutar amai da gudawa, a wasu jihohin ƙasar nan. A rahoton baya bayan nan da Hukumar Yaƙi da Cututtuka Masu Yaduwa ta Ƙasa (NCDC) ta fitar an bayyana cewa kawo yanzu jihohi 31 ne suka samu ɓullar wannan cuta a hukumance. Kusan za mu iya cewa, wannan annoba ta kama ƙasar nan bakiɗaya kenan. Saboda hatta a sauran jihohin da ba a ambata ba, ba yana nufin babu mai ɗauke da ciwon ba ne, sai dai ko hukuma…
Read More
Kotu ta sake ɗage sauraron ƙarar da ke neman a tsige Ganduje a matsayin shugaban APC

Kotu ta sake ɗage sauraron ƙarar da ke neman a tsige Ganduje a matsayin shugaban APC

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta sake ɗage sauraron ƙarar da ke neman a tsige Dr Abdullahi Ganduje a matsayin shugaban jam’iyyar APC na ƙasa har zuwa ranar 5 ga watan Yuli. Mai shari’a Inyang Ekwo, a ranar Laraba, ya ɗage ci gaba da sauraron ƙarar domin baiwa mai ƙara damar amsa sabuwar buƙatar da Ganduje ya shigar na ƙalubalantar cancantar ƙarar. Da aka ci gaba da sauraron ƙarar, lauyan mai ƙara, Benjamin Daɓou, ya shaida wa kotun cewa Sanusi Musa, SAN, wanda ke kare Ganduje, ya miƙa masa wata sabuwar buƙata.…
Read More