ukarofi

11626 Posts
Ƙungiyoyin tsofaffin ɗaliban Kwalejin Shari’a sun gudanar da taro a Kano

Ƙungiyoyin tsofaffin ɗaliban Kwalejin Shari’a sun gudanar da taro a Kano

Daga MUHAMMADU MUJJITABA a Kano Ƙungiyar tsofaffin Ɗalibai na Kwalejin Shari'a ta 'Aminu Kano College of Islam and Legal Studies' da aka fi sani da Legal sun gudanar babban taro a Kano. Tsofafun ɗaliban fannin shara'a aji na 2007 ƙarƙashin shugabancin Malam Munnir Ibrahim Bala ne suka gudanar da taron. Babban Mai Shara'a na ƙungiyar, Barista Saifulahi Alhassan Aliyu, ya bayyana a taron inda ya ce, su da suka kammala wannan makaranta a shekaru 17 da suka wuce sun yi taron ne don sada zumunci da taimakon juna musammam waɗanda Allah ya karɓi ransu a yi musu adu'a kuma a…
Read More
Ƙungiyar ’yan sintiri ta ja kunnen masu yi mata sojan-gona

Ƙungiyar ’yan sintiri ta ja kunnen masu yi mata sojan-gona

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Ƙungiyar 'Yan Sintiri ta 'Vigilante Group of Nigeria VGN' ta ƙasa ta ja kunnen masu amfanin da sunan ta, suna nuna kan su a matsayin mambobi, alhali su ba 'yan ƙungiyar ba ne, inda ta ce za ta ɗauki duk matakin da ya dace a kan wanda aka kama. Ƙungiyar ta ce, duk wanda ya san shi ba ɗan wannan ƙungiya ba ne, to ya daina amfani da suna, ko kaki, ko duk wani alami na wannan ƙungiya. Shugaban ƙungiyar na ƙasa ta ƁGN, Kaftin na sojan ruwa (mai ritaya), Abubakar Umar Bakori ne ya bayyana…
Read More
Kamar gwamnati ke ƙara ta’azzara matsalolin Nijeriya

Kamar gwamnati ke ƙara ta’azzara matsalolin Nijeriya

A ɓangare guda za mu iya cewa haƙiƙanin gaskiya Gwamnatin ƙasar mu ta Nijeriya suna ƙoƙari, suna kuma aiki don ganin an tabbatar da zaman lafiya da bunƙasa tattalin arziki. Amman duk da wannan ƙoƙarin har ila yau ita ce babbar matsalar ƙasar. Ta kowane ɓangare na matsalar ƙasar nan, za ku ga akwai gazawar ita gwamnatin. Musamman ɓangarorin tsaro, da kuma ita kanta matsalar tattalin arzikin ƙasar da kuma fannin ilimi. Bari mu fara da harkar tattalin arziki a wannan karon. Idan muka yi duba I zuwa harkar, zamu ga cewa, kuɗin da ƙasashen waje suke samu daga Nijeriya,…
Read More
Ina bahaushe ya kai kunyar da aka san shi da ita?

Ina bahaushe ya kai kunyar da aka san shi da ita?

Assalamu Alaikum, 'yan uwa Musulmi. Ina yi muku fatan alkhairi. Idan mai karatu na biye da mu a wasiƙunmu na baya mun yi magana ne akan matsayin kunya a al'adar Bahaushe sannan daga bisani kuma muka gangaro muka duba asalin waɗanda shi wanna al'adar tafi shafa a cikin al'umma. Yadda kunya ta kasance a rayuwar bahaushe jiya, ba haka ta ci gaba da kasancewa a yau ba, domin kuwa ta samu ’yan sauye-sauye, sakamakon mu’amalar wasu da wasu baƙin ƙabilu da suka shigo ƙasar Hausa, suka mamaye. Manyan al’umma da suka fi tasiri a kan rayuwar Bahaushe su ne Larabawa…
Read More
Davido da Chioma: Auren farko ko na biyu?

Davido da Chioma: Auren farko ko na biyu?

Daga AISHA ASAS  Duk wani da zai iya iƙirarin ya san muhimman abubuwa game da shahararren mawaƙi David Adeleke, wanda mutane suka fi sani da Davido, tabbas zai san ko wacce ce Chioma Avril Rowland a rayuwar mawaƙin, kasancewar irin soyayyar da yake bayyana wa duniya yana yi mata, ciki kuwa har da waƙa da ya yi da ke ɗauke da matsayin masoyiyar tasa Chioma.  Sai dai abinda da yawa daga cikin masoyan mawaƙin ba su sani ba shi ne, auren mawaƙin wanda ya gudana a ranar Talatar da ta gabata, bai zama ranar auren mawaƙin da masoyiyarsa na farko…
Read More
Bagudu ya jinjina wa ƙoƙarin hukumar finafinai ta Nijeriya

Bagudu ya jinjina wa ƙoƙarin hukumar finafinai ta Nijeriya

 Daga AISHA ASAS  Mai Girma Ministan Kasafin Kuɗi da Tsare- tsare, Sanata Abubakar Atiku Bagudu ya yi kira ga ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa da masu ruwa da tsaki da harkar finafinan Najeriya su tallafa wa domin bunƙasa tattalin arzikin ƙasar. Ministan ya bayyana hakan ne a lokacin da Babban Daraktan hukumar, Dakta Ali Nuhu da manyan jami’an hukumar suka kai masa ziyarar aiki a ma’aikatar a Abuja. Abubakar Bagudu ya yi nuni da cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya kafa ma’aikatar al’adu da ƙirƙira da masaniyar zamanta ɗaya daga cikin ma'aikatun da ke samarwa ƙasa kuɗin shiga da bunƙasa…
Read More
Hukumar finafinai ta Nijeriya na shirin shirya gagarumin bikin masu harkar fim da sinema 

Hukumar finafinai ta Nijeriya na shirin shirya gagarumin bikin masu harkar fim da sinema 

Daga AISHA ASAS  Hukumar Tace Finafinai ta Najeriya (NFVCB) tare da haɗin gwiwa da Babban Taron Finafinai da Sinema na Legas (LIFACC) suna farin cikin sanar da taron Baji Kolin Masu Shirya Finafinai na Najeriya da kuma Babban Majalisar Gudanarwar Sinema. Wannan taro dai an shirya shi ne domin ya zama wani gagarumin biki ga duk masu ruwa da tsaki a harkar finafinan Najeriya. Dokta Shaibu Husseini, Babban Darakta kuma Babban Jami'in NFƁCB, ya miƙa gayyatar ga dukkan masu ruwa da tsaki a masana'antu da suka jiɓinci sha'anin fim, inda yake fatan su halarci taron. Taron NFƁCB a cikin LIFACC…
Read More
Wakilin Majalisar Ɗinkin Duniya ya buƙaci ɗaukar matakan gaggawar dawo da Nijeriya turbar SDG

Wakilin Majalisar Ɗinkin Duniya ya buƙaci ɗaukar matakan gaggawar dawo da Nijeriya turbar SDG

 Ko’odinetan Majalisar Ɗinkin Duniya a Nijeriya, Mohammed Malick Fall, ya jaddada muhimmancin haɗakar Katsina Impact Convergence, dandali mai karfi da nufin ƙara kaimi don cimma ajandar Majalisar Ɗinkin Duniya ta 2030 da kuma muradun ci gaba mai ɗorewa (SDG) a jihar.  Fall ya bayyana haka ne a wani taron da aka yi a ranar Juma’a, 28 ga watan Yunin 2023, a cibiyar Shehu Musa Yar’adua da ke Abuja. “Ina mika sakon godiyata ga Gwamnan Jihar Katsina bisa ayyukan da yake yi na tabbatar da ci gaba da inganta rayuwar al’ummar Katsina, da ma ɗaukacin yankin Arewa maso Yamma a matsayinsa na Shugaban…
Read More
DA ƊUMI-ƊUMI: ‘Yar ƙunar baƙin wake ta halaka mutum shida da bom a Borno

DA ƊUMI-ƊUMI: ‘Yar ƙunar baƙin wake ta halaka mutum shida da bom a Borno

Wata da ake zargin yar ƙunar bakin wake ce, ta tashi bam a mararaban Gwoza da ke jihar Barno. Wanda hakan yayi sanadiyar aƙalla mutane shida da jikkata wasu da dama. Wadda tai ƙunar bakin waken, ance mace ce wadda bata wuce shekara 20 ba. Bayanan sirri sun tabbatar mafi yawan wanda abun ya rutsa dasu, farar hula ne. Kuma sun dawo ne daga wani biki. Ma'aikatan asibiti sun tabbatar da mutuwar mutum shida da kuma jikkatar mutum 15. Kwamishinan 'ƴan sandan jihar Barno Yusuf Lawal ya tabbatar da faruwar wannan al'amari.
Read More
’Yan majalisa 50 sun roƙi Tinubu ya saki Nnamdi Kanu

’Yan majalisa 50 sun roƙi Tinubu ya saki Nnamdi Kanu

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja ’Yan Majalisar Wakilai 50 sun aike wa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu wasiƙar neman ya saki shugaban ƙungiyar ta’addanci ta IPOB, Nnamdi Kanu. Honorabul Mohammed Jajere ya tabbatar wa Manhaja goyon bayansa ga buƙatar a saki Namadi Kanu, wanda ƙungiyarsa ta IPOB ke neman ɓallewa daga Nijeriya domin kafa ƙasar Biafra. A halin yanzu dai Gwamnatin Tarayya tana gurfanar da shi a kan laifukan ta’addanci da kuma cin amanar ƙasa. Mohammed Jajere ya bayyana cewa sakin Nnamdi Kanu zai sa samu wanzajjen zaman lafiya a yankin Kudu maso Gabas da ma Nijeriya baki ɗaya.…
Read More