ukarofi

11627 Posts
Har yanzu akwai masu kallon karatun mace a matsayin bariki – Asma’u Karofi

Har yanzu akwai masu kallon karatun mace a matsayin bariki – Asma’u Karofi

"Ina so in zama fitacciyar mai sharhin wasanni" Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU  Gimbiyarmu ta wannan mako ba kowa ba ce sai illa, Asma'u Hamza Karofi, fitacciyar 'yar jarida, mai sharhin wasannin ƙwallon ƙafa, kuma ɗaya daga cikin matan da ke gabatar da shirin 'Mata A Yau' a tashar Arewa 24. Gimbiyar tamu wacce ƙwararriya ce wajen gabatar da shirye-shiryen talabijin da sharhi kan abubuwan da suka shafi cigaban matan Arewa, ta shaidawa wakilin Blueprint Manhaja, Abba Abubakar Yakubu cewa burinta watarana ta kai kamar ƙwararriyar mai sharhin wasannin ƙwallon ƙafar turan nan Kate Abdo, ko ma ta zarce ta a…
Read More
MAKAMASHI: Zuƙi ta malle, tushen fitina

MAKAMASHI: Zuƙi ta malle, tushen fitina

Tare da BASHIR MUDI YAKASAI Makamashi, musamman na man fetur da gas da dukkan sauran dangoginsu da kuma mabiyansu, wato ma’adanai waɗanda sun doshi sama da 50, su ne ruhin Nijeriya ta fuskar tattalin arziki da siyasa da kuma zamantakewar al’umma cikin kwanciyar hankali da zaman lafiya da kuma walwala, amma idan babu wata magana tartibiya daga mahakunta, shugabanni, game da wannan ruhi na ƙasa, babu abinda zai haifar illa ruɗani. Kace-nace da ke faruwa dangane da tallafin man fetur tun daga ranar da Shugaban Ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya furta dakatar da bayar da wannan tallafi ga masu hada-hadar…
Read More
Wani otel ya rushe da mutane ciki a Abuja

Wani otel ya rushe da mutane ciki a Abuja

Mutane da dama ake tunanin suna cikin ginin lokacin da bene mai hawa huɗu ya rushe a Abuja. Benen wanda yake jingine da Westbrook Hotel, yana garki a babban birnin tarayya Abuja. Ana zargin shi otel ɗin Westbrook mallakin wani tsohon gwamna ne daga cikin jihohin Yammacin Najeriya. Wani shaidar gani da ido, ya shaida cewa, yace lamarin zai iya haddasa a jikkata sosai domin ya hangi an ciro mutum biyu an tafi dasu asibiti. Akwai yiyuwar akwai sauran mutane sosai inji shi. Sauran bayanai za su biyo baya.
Read More
A cikin gida ake samar da dukkan katin kiran waya – NCC

A cikin gida ake samar da dukkan katin kiran waya – NCC

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Hukumar Sadarwa ta Nijeriya, NCC, a ranar Lahadi ta ce kashi 100 na katin kira, SIM, da ake amfani da su a ƙasar ana yin su ne a cikin gida. Babagana Digima, Shugaban Sabbin Kafafan Yaɗa Labarai da Tsaron Watsa Labarai na NCC ne ya bayyana haka a wurin horar da shugabannin kafafen yaɗa labarai a Legas. Horon na kwanaki biyu yana da taken: "Haɓaka Ƙwararrun Masu Ruwa Da Tsaki Na Kafofin Watsa Labarai Akan Abubuwan Da Ke Faruwa A Harkar Sadarwa." Digima ya danganta hakan ne da jajircewar hukumar wajen ƙarfafa abubuwan cikin gida da…
Read More
Talauci ya fi illa ga dimukraɗiyya fiye da rarraunan tsari – Dogara

Talauci ya fi illa ga dimukraɗiyya fiye da rarraunan tsari – Dogara

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Tsohon Kakakin Majalisar Wakilai, Yakubu Dogara, ya gabatar da wani jawabi mai jan hankali inda ya jaddada cewa talauci ya fi yin barazana ga dimukraɗiyya fiye da rarraunan tsari a ƙasa. Taron, wanda aka gudanar a otel ɗin Marriott da ke Ikeja, Legas, wanda ƙungiyar Coɓenant Nation ta shirya, ya mayar da hankali kan taken “Dimokraɗiyya da Tattalin Arzikin”. A jawabinsa na buɗe taron, Dogara ya nuna jin daɗinsa ga waɗanda suka shirya taron, ya kuma yaba da taken da suka zaɓa, inda ya bayyana muhimmancinsa a ranar tunawa da dawowar Nijeriya kan turbar dimokuraɗiyya bayan…
Read More
Gwamnan Kano ya nuna damuwa kan ayyukan hukumomin KAROTA da REMASAB

Gwamnan Kano ya nuna damuwa kan ayyukan hukumomin KAROTA da REMASAB

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya nuna damuwarsa kan yadda ma’aikatun tsaftar muhalli da ta karota ke gudanar da ayyukansu a jihar. Cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran gwamnan Sanusi Bature Dawakin Tofa ya aikowa Blueprint Manhaja, gwamnan ya umarci ma’aikatun biyu su gabatar da cikakken bayanan kayayyakin aikinsu domin tabbatar da ingancinsu. Gwamnan ya bayar da umarnin ne bayan wata ziyarar ba-zata da ya kai hukumomin, inda ya tarar da gazawar ma’aikatun tare da jami’an hukumomin. Abba Kabir ya nuna damuwarsa kan yadda hukumomin ke gudanar da ayyukansu, duk da irin kuɗin…
Read More
Jirgi marar matuki ne ya faɗi a Kaduna, inji Rundunar Sojojin Sama

Jirgi marar matuki ne ya faɗi a Kaduna, inji Rundunar Sojojin Sama

Saɓanin rahotanni dake yawo a kafar sadarwa cewa jirgi mai saukar angulu ya faɗi a kaduna, rundunar sojojin Najeriya sunce jirgi marar matuƙi ne ya faɗi. Lamarin ya auku ne a wani ƙauye da ake kira Rumji wanda yake kilomita 12 daga sansanin sojojin. Don haka mutane su guji, yaɗa jita jita har sai sun tabbatar inji Edward Gabkwet, jami'in yaɗa labarai na rundunar. Yanzu haka an fara bincike a san dalilin faruwar wannan lamarin.
Read More
Yadda aka kama wasu ma’aikatan banki da laifin satar miliyoyin naira a asusun mamaci

Yadda aka kama wasu ma’aikatan banki da laifin satar miliyoyin naira a asusun mamaci

Jami’an Hukumar Yaƙi da Masu Yi Wa Tattalin Arziki Ƙasa Zagon Ƙasa, EFCC, reshen Makurdi sun kama wasu ma’aikatan banki bisa zargin satar Naira 4,199,500 mallakin wani kwastoma da ya mutu. An kama waɗanda ake zargi, Idah Ogoh da Agbo Okwute, a ranar Jumma’a, 21 ga Yuni, 2024 a garin Makurdi, Jihar Benuwai. Cafke su ya biyo bayan ƙorafin da bankin ya shigar a kansu bisa zargin cirar kuɗi daga asusun marigayin, Emmanuel Azer Agenna ba tare da izini ba. An gano wannan ɓarnar ne lokacin da iyalan marigayin suka je bankin domin neman ragowar kuɗin da ke cikin asusu.…
Read More
Mutane 25 sun mutu, 53 sun jikkata a haɗarin mota a Kano – FRSC

Mutane 25 sun mutu, 53 sun jikkata a haɗarin mota a Kano – FRSC

Daga Ibrahim Hamisu, Kano Hukumar kiyaye haddura ta ƙasa FRSC reshen jihar Kano ta tabbatar da mutuwar matafiya 25, yayin da wasu 53 suka samu raunuka a wani hatsarin mota da ya afku a safiyar yau Litinin. Lamarin ya faru ne a kasuwar duniya ta Dangwairo da ke wajen birnin Kano. An ce matafiyan sun yo lodin su ne a cikin wata tirela wadda ita ma take dauke da shanu ta nufi Kudancin Nijeriya daga Maiduguri. Sai dai Tirelar ta yi karo da wata motar kuma ta yi ta'adi so sai inda mutane da dama suka mutu. Kwamandan hukumar FRSC…
Read More
An cafke matashin da ya yi garkuwa da kansa

An cafke matashin da ya yi garkuwa da kansa

Rundunar 'yan sanda Jihar Legas ta ce ta kama wani matashi kan zargin ƙaryar garkuwa da kansa. Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar, Benjamin Hundeyin, ne ya bayyana haka a shafinsa na X, a lokacin da yake tsokaci kan wani saƙo da wani matashi da ke amfani da shafin mai suna @Flacko ya wallafa a shafin. FlackoT ya wallafa cewa an tsare shi a ofishin 'yan sanda na Ikeja kan zargin garkuwa da wani mutum da bai san komai game da shi ba. "Jama'a an tsare ni a ofishin 'yan sanda. Bani da isasshen lokaci, kuma ban san…
Read More