ukarofi

11627 Posts
Tinubu ya yi ta’aziyyar rasuwar ƙwararren ɗan jarida, Kabir Yusuf

Tinubu ya yi ta’aziyyar rasuwar ƙwararren ɗan jarida, Kabir Yusuf

Daga USMAN NASIR KAROFI a Abuja Shugaba Bola Tinubu ya miƙa ta'aziyyarsa ga iyalan Kabir Yusuf, wanda ya rasu ranar Talata. Bayanin hakan ya fito ne a cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun Kakakin Shugaban Ƙasa, Ajuri Ngelale, a yau Laraba. Sanarwa ta ce, “Yusuf ƙwararren ɗan jarida ne, wanda ya kasance manemin labarai na Birnin Tarayya na Jaridun The Triumph da kuma Radio France Internationale Hausa. “Ya yi wakilin Fadar Shugaban Ƙasa na jaridu da dama tsawon shekaru da dama har zuwa rasuwarsa. “Shugaba ya yi addu'ar Allah ya jikan sa, kuma ya ba iyalansa hakuri a…
Read More
Barau Jibrin ya miƙa ta’aziyyar rasuwar ɗan jarida, Kabiru Yusuf

Barau Jibrin ya miƙa ta’aziyyar rasuwar ɗan jarida, Kabiru Yusuf

Mataimakin shugaban majalisar dattijai, Barau Jibrin ya miƙa ta'aziyyar rasuwar ƙwararren ɗan jarida Kabiru Yusuf. Sanarwar ta fito daga bakin mai bashi shawara, Alhaji Ismail Mudashir. Ya jaddada cewa marigayin mutum ne mai jajircewa da nuna ƙwazo wajen aikinsa. Marigayin ya kasance tsohon wakilin gidan jarida na Triumph da RFI Hausa. Ya kasance wakilin gidan gwamnati na shekaru da dama. Daga karshe yayi wa mamacin Addu'a, Allah ya jiƙansa, yayi masa rahama.
Read More
Ambaliyar Legas: Ku kwantar da hankalinku – Gwamna Sanwo-Olu

Ambaliyar Legas: Ku kwantar da hankalinku – Gwamna Sanwo-Olu

Gwamnan Jihar Legas, Sanwo Olu yayi kira da mutane su kwantar da hankalin su a dalilin ruwan sama da aka samu kamar da bakin ƙwarya. Kwamishinan ruwa na Jihar shine yake faɗin haka a yayin wata sanarwa ranar Laraba. Ruwan saman ya fara ne wajen karfe biyu na dare, sai dai mutane suka tashi suka ga ruwa ya cika masu ko ina har da ambaliyar ruwa a wasu sassan jihar. Wurare kamar su, Surulere, Ijesha, Okokomaiko, Ibeju-Lekki, Greenland Estate in Mende, Gbagada, Oshodi, Isolo, Lekki, Ikoyi, Ogba, Ikeja, da Ajah duk abun ya shafesu. Har wasu tituna suma abun ya…
Read More
Ƙungiyar Ƙwadago ta soki gwamnoni bisa kawo cikas a lamarin ƙarancin albashi

Ƙungiyar Ƙwadago ta soki gwamnoni bisa kawo cikas a lamarin ƙarancin albashi

Ƙungiyar ƙwadago ta bayyana saka baki da gwamnoni ke yi a batun ƙarancin albashi baya cikin kundin tsarin mulki. Benson Ujah, shugaban yaɗa labari na ƙungiyar, shiya faɗi haka a yayin tattaunawar sa da gidan talabijin na Arise ranar litinin. Ujah ya jaddada ƙin amincewar su saka baki da gwamnoni sukeyi a kan lamarin ƙarancin albashin. Yayi bayani yace, hanyar da ake bi domin cimma matsaya a kan mafi ƙarancin albashi shine tattaunawa daga bangare uku, ɓangaren gwamnati, ɓangaren ƙwadago da ɓangaren ma'aikata. Fitar wani ɓangare a wannan gabar cin amana ne. Ya ƙara da cewa, Najeriya tai ta bin…
Read More
Ba ni da madubin kwaikwayo a marubuta – Asiya Muhammad 

Ba ni da madubin kwaikwayo a marubuta – Asiya Muhammad 

"Burina littafin da nake son bugawa ya samu karɓuwa" Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU  Asiya Muhammad wata jajirtacciyar marubuciyar onlayin ce daga Jihar Kebbi, tana cikin fitattun marubuta da ƙungiyar Lafazi Writers Association ke ji da su, saboda ƙwazonsu da yadda suke rubutu mai tsari da tsafta. Tun da ta fara rubutun labaran adabi a shekarar 2017, Asiya ta fitar da labarai masu yawan gaske, waɗanda take fitarwa a shafukan sada zumunta, kuma masoya littattafanta ke rige-rigen nema su karanta. A tattaunawarta da wakilin Blueprint Manhaja, Abba Abubakar Yakubu, marubuciyar ta bayyana shirinta na fitar da sabon littafinta da za a…
Read More
Gwamnatin tarayya ta yi nasara kan gwamnoni akan cin gashin kan ƙananan hukumomi

Gwamnatin tarayya ta yi nasara kan gwamnoni akan cin gashin kan ƙananan hukumomi

Gwamnatin Tarayya da kuma Hukumar Binciken Kuɗaɗen Najeriya (NFIU) sun yi nasara a shari'ar da suka shigar kan gwamnonin jihohi game da cin gashin kan ƙananan hukumomi. Alƙalin Kotun Tarayya Mai shari'a Inyang Ekwo ya ba da hukunci ranar Litinin, 24 ga watan Yuni 2024, inda yake bayyana nasarar gwamnatin tarayya a shari'ar. Ƙungiyar Gwamnonin Najeriya ta kai gwamnatin tarayya ƙara da NFIU saboda shiga cikin ikon gwamnatocin akan Ƙananan Hukumomi, suna nuna hujjoji daga kundin tsarin mulkin 1999. Sai dai NFIU sun fitar da sabbin ƙaidoji, wanda cikin su shine rage fitar yawan kuɗi daga asusun kananan hukumomi zuwa…
Read More
Matar mataimakin gwamnan Niger ta rasu

Matar mataimakin gwamnan Niger ta rasu

Matar mataimakin gwamnan Jihar Niger, Garba Yakubu ta rasu ranar Talata a garin Minna. Mai magana da yawun mataimakin gwamnan, Ummikaltumi Kuta ta tabbatar wa gidan talabijin na Channels cewa Hajiya Zainab ta rasu bayan fama da gajeruwar rashin lafiya. Gwamnan Jihar Niger,Umaru Bago ya nuna alhinin sa ga mutuwar. Inda ya bayyana cewa mutuwar Hajiya Zainab a matsayin rashi ga duk al'ummar Jihar Niger. Kamar yadda sanarwa mai ɗauke da sa hannun mai magana da yawunsa, Ibrahim Bologi ta bayyana.
Read More
Da ƊUMI-ƊUMI: Kotu ta ɗage sauraren ƙarar rikicin masarautar Kano zuwa jibi

Da ƊUMI-ƊUMI: Kotu ta ɗage sauraren ƙarar rikicin masarautar Kano zuwa jibi

A yayin da kotu ke cigaba da sauraren ƙarar rikicin masarautar Kano, yau babban kotun Jihar Kano ta ɗage sauraren ƙarar zuwa jibi, 4 ga watan Yuli. Ƙarar da aka shigar 27 ga watan Mayu, tana neman sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero, da Sarkin Bichi, Gaya, Karaye da kuma Rano da su daina yawo suna kiran kansu sarakuna. Waɗanda ake tuhuma, sun haɗa da Alhaji Aminu Ado Bayero, Alhaji Nasiru Ado Bayero, Alhaji Kabiru Muhammad Inuwa da kuma Alhaji Ibrahim Gaya. Saura sun haɗa da sufeton 'ƴan sanda, Darakta hukumar farin kaya, Sojoji da kuma Civil Defense. Bayan…
Read More
Ana cece-kuce kan ƙona makaman Naira biliyan huɗu da Hukumar Kwastom za ta yi

Ana cece-kuce kan ƙona makaman Naira biliyan huɗu da Hukumar Kwastom za ta yi

Yan Najeriya na cece kuce akan ƙona makaman biliyan goma da hukumar kwastom za tayi. Hukumar kwastom a yayin wani atisayen su, sun kama kwantena cike da bindigogi 844, da harsashai 112,500 a birnin fatakwal. Makaman an ɓoye su a cikin kayan katako irin su kofa, jakukuna, da kayan karfe. Kwantenar da aka kama, ta taso ne daga ƙasar turkiya, wanda harajin da aka biya mata ya kai adadin biliyan huɗu. Amma daga ciki cece kuce da ake wani ya bayyana a shafin sa na X cewa "kuna son ƙona makamai na biliyan huɗu bayan sojoji na kukan basu da…
Read More
Tsohon mijin Diezani ya roƙi kotu ta hana ta amfani da sunansa

Tsohon mijin Diezani ya roƙi kotu ta hana ta amfani da sunansa

Tsohon mijin tsohuwar ministan man fetur ta ƙasa, Diezani, ya shigar da ƙara kotu kan hana ta amfani da sunanshi bayan mutuwar auren su. Ya roƙi kotun ta umarci Diezani ta dawo da tsohon sunanta na Agama kafin suyi aure. Ya umarce ta sanya sanar da wannan sunan a jaridun Najeriya da Ingila. Ƙarar an shigar da ita ga babbar kotun Jihar Legas da ta daina amfani da sunan shi. Saboda yin haka na masa barazana sosai ga kasuwancin shi da mutuncin shi.
Read More