05
Jul
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Wasu malamai sun koka akan Gwamnatin Tarayya, domin sanya hannu akan yarjejeniyar nan mai cece-kuce ta Samoa, wacce ake zargin ta na ƙunshe da amincewa da tsarin auren jinsi. A cewarsu, yarjejeniyar tana ɗauke da wasu sharaɗai da suka ƙunshi cewa ƙasashe masu tasowa dole su yarda da ’yancin ’yan luwadi da ’yan maɗigo da kuma ’yancin yin auren jinsi ɗaya. Yarjejeniyar an samar da ita a tsibirin Samoa, inda aka sanya ma ta hannu a ranar 15 ga Nuwamba, 2023, amma tun lokacin yarjejeniyar ke samun suka daga addinai da dama, saboda hakan…
