ukarofi

11627 Posts
lllar gurɓata muhalli ga rayuwar al’umma

lllar gurɓata muhalli ga rayuwar al’umma

Rahotanni daga Hukumar kula da lafiya ta duniya (WHO) sun nuna cewa, aƙalla gurɓata muhalli na sanadiyyar salwantar rayukan kusan mutum miliyan goma a duniya a kowace shekara. Wani babban abin tashin hankalin shi ne Nijeriya na daga cikin ƙasashen Afirika da wannan matsala ta yi ƙamari a cikinta, kuma ita ce ta huɗu a cikin jerin ƙasashen duniya da ake fama da wannan matsala ta gurɓata muhalli. Domin kuwa ƙididdiga ta nuna cewa, duk cikin ’yan Nijeriya dubu ɗari, akwai mutum ɗari da hamsin da ke mutuwa sakamakon shaƙar gurɓatacciyar iska a kowace shekara. A ƙasar Afganistan mutum 406,…
Read More
Kwastom sun kama makaman biliyan N1.6 a filin jirgin Legas

Kwastom sun kama makaman biliyan N1.6 a filin jirgin Legas

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Hukumar Kwastom ta Nijeriya ta kama makamai da kudinsu ya haura Naira biliyan 1.6 a filin jirgin sama na Murtala Muhammad da ke Jihar Legas. Makaman da aka kama sun hada da jirage marasa matuka da kakin soji da ragunan sulke da hulunan kwano da na’urorin sadarwa na oba-oba da sauran kayan yaki. Kwanturola-Janar na Hukumar Kwastam na Kasa, Bashir Adewale Adeniyi, ya sanar cewa cikin makaman da aka kama akwai “bindigogi 55 masu sarrafa kansu kirar Jojef Magnum (Tomahawk) da kudinsu ya kai Naira miliyan 270.8. “Bincikenmu ya gano cewa wasu ’yan Nijeriya…
Read More
An kama ’yan bindiga biyar bayan gumurzu da ’yan sanda a Abuja

An kama ’yan bindiga biyar bayan gumurzu da ’yan sanda a Abuja

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja ’Yan sanda sun kama ’yan bindiga guda biyar bayan musayar wuta da su a yankin Babban Birnin Tarayya. An ƙwato bindigogi ƙirar AK-47 da wata kuma a hannun ’yan bindigar da aka kama a dajin da ke tsakanin yankin Gwagwa  Dei-Dei da ke wajen garin Abuja. Kwamishinan ’Yan Sandan Abuja, Benneth Igweh, ya sanar a safiyar Alhamis cewa ’yan bindigar sun shiga hannu ne a samamen kwana uku da rundunar ta gudanar a yankin. Ya ce bayan samun bayanai kan ayyukan ɓata-garin ne ’yan sanda suka yi dirar mikiya a maboyar ’yan bindigar, inda…
Read More
Makamai da ƙwayar biliyan N13.9 muka kama a Ribas – Kwastom

Makamai da ƙwayar biliyan N13.9 muka kama a Ribas – Kwastom

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Shugaban Hukumar Kwastom ta Nijeriya, Bashir Adeniyi Adewali ya ce kimar makamai da miyagun ƙwayoyi da suka kama a rana guda a Jihar Ribas ya kai Naira biliyan 13.9. Bashir Adewali ya bayyana cewa makaman biliyan N4.171 suka kama a Tashar Jiragen Ruwa ta Onne da ke Jihar Ribas a ranar Litinin. Makaman a cewarsa sun haɗa da bibdigo guda 844 da kuma harsasai masu rai guda 12,500, waɗanda aka ɓoye suba cikin kayan daki da aka shigo da su daga ƙasar Turkiyya. A tashar jiragen ruwan ne kuma jami’an hukumar kwastom suka kama…
Read More
Abin da ya sa ‘yan sandan Nijeriya ke shan wahala – Majalisar Dattijai

Abin da ya sa ‘yan sandan Nijeriya ke shan wahala – Majalisar Dattijai

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Majalisar Dattijan Nijeriya ta ce halin da aikin ‘yan sanda ke ciki a kasar na buƙatar a zauna a sake masa fasali. Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Mataimakin shugaban Majalisar, Sanata Barau Jibrin ya ce ba a gina hukumar ‘yan sandan Nijeriyar kan yadda za ta yi nasara ba. Sanata Ahmed Abdulhamid Malam-Madori wanda shi ne shugaban kwamitin aikin ‘yan sanda na Majalisar dattijan ƙasar, ya shaida wa BBC cewa tabbas batun haka yake, saboda yadda ake da ƙwararrun 'yansanda a ƙasar da za su iya fitar da ita a idon…
Read More
Gwamnatin Nijeriya na mantawa da Arewa maso Gabas a ayyukanta – Sanata Goje

Gwamnatin Nijeriya na mantawa da Arewa maso Gabas a ayyukanta – Sanata Goje

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Majalisar Dattijan Nijeriya ta ce gwamnatin kasar ta manta da yankin arewa maso gabas a wasu daga cikin manyan ayyukanta da take yi a fadin kasar. Sanata Muhammad Danjuma Goje daga jihar Gombe ne ya gabatar da kuduri kan wannan batu, wanda kuma ya samu goyon bayan majalisar baki daya. Sanata Goje ya ce Shugaba Tinubu ya dauki matakan gina manyan hanyoyi na zamani a sassa biyar na kasar, amma babu ko hanya daya da za ta ratsa yankin arewa maso gabas. Tinubu ya yi alƙawarin gina babbar hanya daga Legas zuwa birnin Kalaba,…
Read More
Rikicin masarautar Kano: NNPP ta nesanta kanta da Kwankwaso kan umarni ga ‘yan majalisa

Rikicin masarautar Kano: NNPP ta nesanta kanta da Kwankwaso kan umarni ga ‘yan majalisa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Shugabancin jam’iyyar adawa ta New Nigeria Peoples Party (NNPP) na ƙasa ya nesanta kansa da jagoranta na ƙasa, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, kan wasiƙar da ya rubuta wa ‘ya’yan jam’iyyar a majalisar dokokin ƙasar dangane da rikicin masarautar Kano da ke ci gaba. Jam’iyyar ta ce Kwankwaso ya rubuta wasiƙa ga ɗaukacin ‘yan majalisar tarayya da aka zaɓa a ƙarƙashin inuwar NNPP, wanda wani Dr. Ajuji Ahmed ya sanya wa hannu, inda ake zargin ya umurci ‘yan majalisar su fara sukar Shugaba Bola Tinubu da gwamnatin tarayya kan rikicin masarautar Kano. Amma, a cikin…
Read More
’Yan ƙwadago sun yi tir da sabon ƙarin kuɗin lantarki

’Yan ƙwadago sun yi tir da sabon ƙarin kuɗin lantarki

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Ƙungiyoyin Ƙwadagon Nijeriya NLC da TUC, da kuma ƙungiyoyi masu zaman kansu sun soki ƙarin kuɗin wutar lantarki ga kwastomomi masu layin Band A. Kamfanonin rarraba wutar lantarki da dama da suka haɗa da Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Ibadan, Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki ta Eko, da Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Kaduna, sun sanar da cewa farashin kwastomomi na layin Band A zai tashi daga Naira 206.80 a kowace kilowatt zuwa Naira 209.50. Wannan ƙarin da Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Nijeriya ta aiwatar, na da nasaba da faɗuwar darajar Naira a kan Dalar…
Read More
JAMB ta bankaɗo ɗalibai 3,000 da suka kammala karatun jami’a na bogi

JAMB ta bankaɗo ɗalibai 3,000 da suka kammala karatun jami’a na bogi

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Hukumar shirya jarrabawar shiga makarantun gaba da sakandire ta ƙasa (JAMB) a Nijeriya ta bankaɗo daliban da suka kammala karatun jamia na bogi 3,000 da kuma mallakar takardun shaidar kammala karatu ba bisa ƙaida ba a duk faɗin ƙasar. Magatakardar hukumar, Farfesa Ishaƙ Oloyede ne ya bayyana hakan kuma ya ce waɗannan mutane ba su taɓa zuwa jami’a ba, wanda hakan ya nuna irin cin hanci da rashawa da ake samu a harkar ilimi. Oloyede ya soki yadda wasu cibiyoyin karatu suke shigar da ɗalibai makarantu ba bisa ƙa’ida ba, yana mai cewa abin…
Read More
Gwamnatin Kano ba ta hana ’yan kasuwar IBB sana’arsu ba – Hon. Wise

Gwamnatin Kano ba ta hana ’yan kasuwar IBB sana’arsu ba – Hon. Wise

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano An bayyana Gwamnan Jihar Kan, .Alhaji Abba Kabir Yusuf da cewa mutum ne mai tausayi da imani duk lokacin da aka ce wata matsala ta shafi al;umma ba wai ;yan kasuwar kaɗai ba  zai zauna ya samu sukuni ba sai ya tabbatar ya warware matsalar. Hon. Alhaji Isa Wise, Babban Mataimaki na biyu ga Gwamnan Jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf kan harkokin kasuwanci ne ya shaida hakan ga yan jarida. Ya ce dalilin da ya sa aka cire teburan yan kasuwar a kewayen filin Idi shine don samar da sarari lokacin sallar idi domin…
Read More