ukarofi

11627 Posts
Buga ƙwallo da robar kariyar fuska babu daɗi – Mbappe

Buga ƙwallo da robar kariyar fuska babu daɗi – Mbappe

Ɗan wasan ƙasar Faransa, Kylian Mbappe ya ce ba daɗi buga ƙwallo da robar kariyar fuska, bayan Faransa ta fuskanci Belgium a karawar zagaye na biyu a Euro 2024 ranar Litinin ɗin da ta gabata. Mai shekara 25 ya ji rauni a karan hanci a wasan farko a cikin rukuni da Faransa ta ci Austria 1-0 a gasar ta cin kofin nahiyar Turai. Bai buga wasa na biyu ba da suka tashi ba ci da Netherlands, amma ya kara a fafatawa ta uku a cikin rukuni da suka tashi 1-1 da Poland. A karawar ce Mbappe ya buga da robar…
Read More
A Inter Miami zan ajiye ƙwallo – Messi

A Inter Miami zan ajiye ƙwallo – Messi

Shahararren ɗan wasan ƙasar Argentina, Lionel Messi ya yanke shawarar rataye takalmansa daga ƙwallon ƙafa a Inter Miami.  Ɗan wasan mai shekara 36, mai kyautar Ballon d’Or takwas, ya koma buga gasar ƙwallon ƙafa ta Amurka a kakar wasa ta 2022/23, bayan da kwantiraginsa ya ƙare a Paris St-Germain. Kyaftin ɗin na tawagar Argentina ya nuna kansa a ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barcelona, inda ya lashe gasar Kofin Zakarun Turai sau huɗu da La Liga 10 a ƙungiyar da ke Sifaniya. Wanda ya ɗauki kofin duniya a 2022 da Argentina a Katar a 2022, yana da sauran ƙunshin yarjejeniya da…
Read More
Brazil ta ƙaddamar da ‘Ranar Sarki Pele’

Brazil ta ƙaddamar da ‘Ranar Sarki Pele’

Za a karrama fitaccen ɗan wasan ƙwallon ƙafa na Brazil Pele a ƙasarsa tare da ƙaddamar da bikin “Ranar Sarki Pele”, inji jaridar gwamnatin ƙasar a ranar Talata. Kasancewarsa fitaccen ɗan wasan ƙwallon ƙafa a tarihi, Edson Arantes do Nascimento - wanda aka fi sani da Pele - ya lashe gasar kofin duniya sau uku tare da Brazil kuma ya zura ƙwallaye sama da 1,000 a tarihin rayuwarsa. Za a gudanar da "Ranar Sarki Pele" a ranar 19 ga Nuwamba - ranar da ɗan wasan ya ci ƙwallonsa ta 1,000 a wasan da kulob ɗinsa ta Santos ta doka a…
Read More
Wannan ne Euro na ta ƙarshe – Ronaldo

Wannan ne Euro na ta ƙarshe – Ronaldo

Kyaftin ɗin Portugal, Cristiano Ronaldo, ya bayyana cewa gasar Euro 2024 ce za ta zama Euro ɗinsa ta ƙarshe. Ronaldo ya bayyana hakan ne bayan da Portugal ta fitar da Sloɓenia a bugun fenariti a wasan da suka fafata a zagaye na 16 a daren Litinin. Ɗan wasan mai shekaru 39 ya ɓarar da bugun fenariti, to sai dai tsohon ɗan ƙwallon Manchester United da Real Madrida Juɓentus ya sharɓi kuka. Sai dai Ronaldo ya zura ƙwallo a bugun daga kai sai mai tsaron gida, yayin da Diogo Costa ya yi bugun daga kai sai mai tsaron gida. "Tabbas wannan…
Read More
Hada-hadar kasuwar ’yan wasan ƙwallon ƙafa

Hada-hadar kasuwar ’yan wasan ƙwallon ƙafa

Arsenal ta ɗauki zaɓin sayen mai tsaron gidanta Daɓid Raya da tauka aro daga Brentford kan kuɗi fan miliyan 27. Raya mai shekara 28 ya buga wasannin gasar firimiya 16 ba tare da an zura masa ƙwallo a raga ba. An zura masa ƙwallo 16 ne kacal a gasar firimiya sannan a ƙarshe ya lashe kyautar maitsaron ragar da ya fi kowanne ƙoƙari a kakar da ta gabata. Arsenal tana da mai tsaron ragarta Aaron Ramsadale, wanda ya buga mata wasanni 38 na kakar da aka yi ta 2022/23, ya buga wasanni 14 ba tare da an zura masa ƙwallo…
Read More
Hukumar tace fina finai za ta sanya ƙafar wando ɗaya da masu zanen ƙwarangwal a jikin Adaidaita

Hukumar tace fina finai za ta sanya ƙafar wando ɗaya da masu zanen ƙwarangwal a jikin Adaidaita

Daga USMAN KAROFI A yau ne, hukumar tace fina finai da ɗabi'a ta Jihar kano ta bada sanarwar cewa za ta sanya ƙafar wando ɗaya da masu zane dake yiwa matuƙa baburan adaidaita zanen banza. Wannan na fitowa a wata sanarwa daga jami'in hulɗa da jama'a na hukumar Abdullahi Sani Sulaiman, inda yace Shugaban hukumar Abba Elmustapha ya ɗau wannan alwashi ne a lokacin da ƙungiyar masu sana'ar zane suka kai mashi ziyara ƙarkashin jagorancin Malam Muhammad Kabir. Ya ƙara da cewa, duk wani mai zane da yake da hannu wajen yin zane na cin mutunci, ko ɓata tarbiya da…
Read More
Za a kara tsakanin Massoud Pezeshkian da Saïd Jalili a zaɓen shugabancin Iran

Za a kara tsakanin Massoud Pezeshkian da Saïd Jalili a zaɓen shugabancin Iran

A Ƙasar Iran kasancewa a zagayen farko na zaɓen shugaban ƙasa na 2024, wata ɗaya bayan mutuwar shugaba Ibrahim Raïssi, zagayen farko ya bayar da dama na zaɓen magajin Raissi ba, sai an je zagaye na biyu tsakanin ɗan takarar neman sauyi Massoud Pezeshkian wanda ya samu kashi 40% da ɗan takarar masu ra'ayin riƙau Saïd Jalili ya zo a matsayi na biyu da kashi 38.5% na ƙuri'un. Bincike ya bayyana cewa kashi 60% na Iraniyawa sun ƙi fitowa rumfunan zaɓe, alamar rashin gamsuwa da taɓarɓarewar tattalin arziki da kuma murƙushe masu zanga-zangar da suka biyo bayan mutuwar Mahsa Amini…
Read More
Sama da Indiyawa 100 sun mutu a wurin bikin addini

Sama da Indiyawa 100 sun mutu a wurin bikin addini

Hukumomin Indiya sun tabbatar da mutuwar mutane 116 sakamakon turmutsitsi a yayin wani dandazon taron addini a wannan Talatar. Mutanen sun rasa rayukansu bayan halatar taron addini na ƙabilar Hindu a Hathras da ke arewacin ƙasar, kuma galibinsu mata ne da ƙananan yara. Wata mai suna Shakuntala da ta ganewa idonta yadda lamarin ya faru ta ce duk jama’ar wurin sun fara tserewa ne bayan kammala taron addinin. Wani babban jami’in ɗan sanda, Shalbh Mathur ya ce adadin mutanen da suka je taron sun haura yawan waɗanda aka ba wa izinin zuwa. Babban Ministan jihar Uttar Pradesh Yogi Adityanath, wanda…
Read More
Babban ɗan Kwame Nkrumah ya rasu 

Babban ɗan Kwame Nkrumah ya rasu 

Dakta Francis Nkrumah, babban ɗan shugaban Ghana na farko, Osagyefo Dr. Kwame Nkrumah, ya rasu, yana da shekaru 89 a duniya. Mawallafin Indiya kuma editan Ɓijay Prashad ne ya tabbatar da mutuwarsa, wanda ya ba da labarin ta kafafen sada zumunta ranar Lahadi, 30 ga Yuni, 2023. “Dakta Francis Nkrumah (1935-2024) ya rasu, wanda ya kasance babban ɗan Kwame Nkrumah. Ya yi rayuwarsa a matsayin likitan yara, wanda majinyatansa ke matuƙar ƙaunarsa. Dakta Nkrumah ya ci gaba da zama a Ghana bayan juyin mulkin da aka yi wa mahaifinsa, kuma ya ci gaba da aiki a matsayin likita, kuma masanin…
Read More
Kenya za ta ƙara ciyo bashi  bayan janye dokar ƙarin haraji – Shugaban Ƙasa

Kenya za ta ƙara ciyo bashi  bayan janye dokar ƙarin haraji – Shugaban Ƙasa

Shugaban Ƙasar Kenya William Ruto ya ce, ƙasar za ta ƙara rance don ci gaba da tafiyar da gwamnatin ƙasar biyo bayan ƙin amincewa da sabuwar dokar ƙarin kuɗin haraji da ake fata ya zama hanyar ƙarin kuɗin shiga ga gwamnatin.  Shugaban ya ce, zai janye ƙudirin dokar da ke ƙunshe da ƙarin harajin da ya janyo mummunar zanga-zanga a ranar Larabar da ta gabata, wadda ta yi sanadin mutuwar mutane, inda aka ƙona majalisar dokokin ƙasar. Sai dai a ranar Lahadin da ta gabata ya bayyana cewa, watsi da ƙudirin ya mayar da ƙasar baya har na tsayin shekaru…
Read More