ukarofi

11668 Posts
Laifi ne sakin fim ko bidiyon kiɗa ba tare da shedar hukumar NFVCB ba – Gwamnatin Tarayya 

Laifi ne sakin fim ko bidiyon kiɗa ba tare da shedar hukumar NFVCB ba – Gwamnatin Tarayya 

Daga AISHA ASAS  A cewar Gwamnatin Tarayya, sakin waƙoƙi, ko finafinai, ko kuma bidiyon kiɗa ba tare da Hukumar Kula da Finafinai ta Ƙasa (NFVCB) ta bayyanar da gurbinsa ba zai iya zama wani nau'in cin zarafi. Rarraba finafinai ta hanyar saka shekarun da ya kamata akai kafin a kalla kan taimaka wurin tantance finafinan da suka dace da waɗanda ba su dace ba ga kallo. Baya ga haka, hanya ce da ke sawaƙa wa iyaye zaɓawa 'ya'yansu finafinai da suka dace da su, da kuma sanin waɗanda bai kamace su kalla tare da yaransu ba. A watan Mayu, hukumar…
Read More
Hukumar Tace Finafinai ta kafa kwamitin mutane bakwai da za su yi aikin tsaftace Kannywood 

Hukumar Tace Finafinai ta kafa kwamitin mutane bakwai da za su yi aikin tsaftace Kannywood 

Daga AISHA ASAS  Shugaban hukumar tace finafinai da ɗab'i ta Jihar Kano, Alhaji Abba El-mustapha ya kafa wani kwamiti na musamman da za su yi aikin tsaftace masana'antar finafinai ta Kannywood. A wata sanarwar wadda ta fito ta hannun Abdullahi Sani Sulaiman Jami’in Watsa Labarai na Hukumar Tace Finafinai, ta bayyana cewa, an kafa kwamitin ne don ganin an cimma ƙudurin sabunta rijista ga kowane ɗan masana'antar, matakin da ta ɗauka da muhimmanci. El-mustapha ya ce, manufar kafa kwamitin shi ne shiga lungu da saƙo na masana'antar domin tabbatar da kowa ya mallaki rijistar da ke nuna shaidar mutum cikakken…
Read More
Harin Gwoza: Da wane zunubi aka kashe su?

Harin Gwoza: Da wane zunubi aka kashe su?

Zubar da jini laifi ne, kuma Allah yana fushi da wanda ya zubar da jinin, wannan ga waɗanda suka yarda cewa akwai Ubangiji. Da wane laifi za ka kashe mutum bayan da cewa bai kamata a zubar da jinin ɗan Adam ba? Duk da cewa akan iya samu wasu basu yarda da akwai Allah ba, amman bana tunanin akwai wanda bai yarda da ɗan adamtaka ba. Mu a gari na alfarma (Gwoza), wanda mune na biyu a yawan jama'a a jihar Borno, tare da mutane masu daraja. Allah ya azurta mu da iyaye masu iliimi, da kuma ’ya’ya masu hazaka.…
Read More
’Ya’ya na kowa ne, a daina cin zarafin ’ya’yan riƙo

’Ya’ya na kowa ne, a daina cin zarafin ’ya’yan riƙo

Assalam alaikum. Ina miƙa saƙon gaisuwa da ban bajiya ga dukka ma'aikatan jaridar Blueprint Manhaja, Allah Ya albarkaci wannan jarida, Amin. Wata babbar matsala na tasowa da ta shafi yadda wasu mutane ke ɗaukar 'ya'yan da ba nasu ba na cikinsu, a wulakance, musamman ma dai 'ya'yan riƙo da suke ɗauko su daga ƙauye ko gidajen 'yan uwa, don su taimaka musu, ko kuma marayu ne da iyayen su suka rasu. Akwai kuma batun yaran aiki da ake ɗauko su daga ƙauye ko daga gaban iyayen su, don su yi aiki a gidajen masu kuɗi ko ma'aikata, don su taya…
Read More
Obasanjo ya musanta hannu a ƙudurin da gwamnonin yankin Kudu maso Gabas suka dauka kan Nnamdi Kanu

Obasanjo ya musanta hannu a ƙudurin da gwamnonin yankin Kudu maso Gabas suka dauka kan Nnamdi Kanu

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Tsohon Shugaban Ƙasa Olusegun Obasanjo ya ce ba a kan batun sakin Nnamdi Kanu suka tattauna ba a lokacin da ya gana da gwamnonin yankin Kudu maso Gabas a ranar Talata. Gwamnoni a ƙarƙashin Ƙungiyar Gwamnonin Kudu maso Gabas sun yanke shawarar ganawa da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu kan sakin Kanu, jagoran haramtacciyar ƙungiyar ƙasar Biafra (IPOB). Hope Uzodimma, gwamnan Imo kuma shugaban ƙungiyar, ya bayyana shirin "tattaunawa" da gwamnatin tarayya kan Kanu a matsayin ɗaya daga cikin ƙudurorin da aka cimma a taron Enugu. Obasanjo ya kuma kai ziyarar haɗin kai a taron…
Read More
Siyasa ke kawo tarnaƙi a yaƙi da ake da cin hanci da rashawa a Nijeriya – Ɗanpass

Siyasa ke kawo tarnaƙi a yaƙi da ake da cin hanci da rashawa a Nijeriya – Ɗanpass

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano  Ɗan Saran Kano, Alhaji Gambo Muhammad Ɗanpass ya bayyana cewa batun yaƙi da cin hanci da rashawa akwai siyasa a cikinsa. Ya ce domin irin abinda yake faruwa a ƙasar nan sai mutum ya kwashi dukiyar al'umma, amma duk da hukumomi na yaƙin da almundahana irin su EFCC da ICPC suna kamawa amma idan aka kai ga matakin shari'a  sai a bada belinsu shi kenan sai aji shiru. Ya ce in ana son gyara sai an tsaya an riƙe amana da gaskiya da tsoron Allah shine zai sa waɗannan  abubuwa za su tafi daidai a…
Read More
Mun gamsu da yadda Gwamna Abba ke gina ci gaban Jihar Kano a tsarin Kwankwasiyya – Musa Gambo Ɗanzaki 

Mun gamsu da yadda Gwamna Abba ke gina ci gaban Jihar Kano a tsarin Kwankwasiyya – Musa Gambo Ɗanzaki 

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano An bayyana shekara ɗaya da rantsar da Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf  irin ayyuka da ya gudanar a zahiri  sun fi na shekaru takwas da tsohon Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya yi. Shugaban Kwankwasiyya na Jihar Kano, Hon. Musa Gambo Hamisu Ɗanzaki ne ya bayyana hakan da yake zantawa da manema labarai. Ya ce sun gode wa Allah da jinjina ga jagoran Kwankwasiyya Dakta Rabiu Musa Kwankwaso bisa hangen nesa da ya yi na zaɓo musu jajirtacce, haziƙin Gwamna Abba Kabir Yusuf domin irin ayyuka da yake bijirowa dasu kwalliya ta na biyan…
Read More
‘Yan siyasar Arewa sun zama ‘yan amshin-Shata a gwamnatin Tinubu – Lukman

‘Yan siyasar Arewa sun zama ‘yan amshin-Shata a gwamnatin Tinubu – Lukman

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Tsohon Mataimakin Shugaban Jam’iyyar APC na Shiyyar Arewa maso Yamma, Salihu Lukman, ya ragargaji ‘yan siyasar Arewa da ke cikin gwamnatin Shugaban Ƙasa Bola Tinubu, cewa an sun yi sototo, su na kallo an maida su ‘yan-amshin-Shata. Lukman wanda kwanan nan ya fice daga APC, ya ce, “an maida ‘yan siyasar Arewa “an-amshin-Shata a gwamnatin Tinubu, waɗanda hatta shi kan sa amshin ba su iya ba. Ga shi kuma su na sane da cewa wanda suke wa amshi shi ma bai san makamar aikin sa ba.” Ya ce ‘yan Arewa sun samu cikakkiyar damar…
Read More
Shekaru bakwai da buɗe zauren marubuta a WhatsApp 

Shekaru bakwai da buɗe zauren marubuta a WhatsApp 

A ƙarshen makon da ya gabata na samu zarafin halartar wani babban taron marubuta da aka gudanar a Birnin Kano, ƙarƙashin Zauren Marubuta na manhajar WhatsApp, wanda ya kasance haɗakar marubuta littattafan Hausa, manazarta da 'yan jarida, malaman harshen Hausa da mawaƙa, da ma duk wani mai ruwa da tsaki a harkar adabin Hausa. Taron ya gudana ne ƙarƙashin jagorancin shugaban ƙungiyar masu shirya finafinan Hausa ta MOPPAN, kuma Sarkin Mawallafan Arewa, Alhaji Ado Ahmad Gidan Dabino MON, wanda bayan kasancewarsa jarumin finafinan Hausa kuma marubuci, ya kasance uba ga marubutan Hausa na Arewa. Daga cikin dalilan da suka sa…
Read More
CNG ta soki masu neman a saki Nnamdi Kanu

CNG ta soki masu neman a saki Nnamdi Kanu

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Gamayyar ƙungiyoyin farar hula na yankin Arewacin Nijeriya, CNG, sun jaddada cewa kotu ce kawai ke da hurumin yanke hukunci kan makomar jagoran haramtacciyar ƙungiyar Biyafara ta IPOB a yankin kudu maso gabashin ƙasar, Nnamdi Kanu ba Gwamnatin Tarayya ba. Wannan martani ya biyo bayan ƙoƙarin da wasu gwamnoni da 'yan majalisar dokokin tarayya na shiyyar kudu maso gabashin Nijeriya, wato yankin al'ummar Ibo ke yi na neman gwamnatin Nijeriya ta saki jagoran na IPOB, duk da kasancewar yana fuskantar shari'a a gaban kotu, bisa zarge-zargen aikata laifuka da suka shafi cin amanar ƙasa. Shugaban CNG, …
Read More