ukarofi

11668 Posts
Ciwon daji

Ciwon daji

Tare da MUSTAPHA IBRAHIM ABDULLAHI ’Yan uwa barkan mu da wannan lokaci, sannun mu da jimirin gudanar da al’amuran rayuwa. Ya mu ka ji da zafi? To Allah ya ba mu wucewa lafiya. In sha Allah yau za mu yi magana akan ciwon kansa ko daji ko kansa. Zan mayar da hankali wajen kawo abubuwa da ke jefa mutum cikin haɗarin kamuwa da cutar da kuma hanyoyin da za a bi wajen rage afkwawa cikin haɗarin  kamuwa da ita. Amma kafin mu fara, Ina son mu fahimci cewa, babu abu ɗaya tilo da ke jawo ciwon kansa; abubuwa ne da…
Read More
Tarihin shahararren marabucin Ƙasar Hausa, Alhaji Abubakar Imam

Tarihin shahararren marabucin Ƙasar Hausa, Alhaji Abubakar Imam

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Dangane da adabin Hausa da adabin Arewacin Nijeriya, Alhaji Abubakar Imam na ɗaya daga cikin manyan marubutan da rubuce-rubucensu suka yi nuni da al’adun Arewa. Sai dai ba abun mamaki ba ne yadda ya fito daga jihar Neja, wadda daman jiha ce mai daɗaɗɗen tarihi na marubuta masu hazaƙa. Ya rubuta litattafai da dama da suka rayu har bayan rasuwarsa. Don fahimtarsa, mutum na buƙatar karanta ko wane shafi masu ban sha'awa na littattafansa don gane wa kansa wane ne Alhaji Abubakar Imam. Malami ne, mai kishin ganin al'ummarsa sun sami ilimi. Har ila yau, ya…
Read More
An kama dagaci da kansila kan zargin satar taransifoma

An kama dagaci da kansila kan zargin satar taransifoma

Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya ya amince da dakatar da dagacin garin Majidadi da ke yankin ƙaramar hukumar Akko, Mohammed Majidadi bisa zargin hannu a sace wata taransifoma. Cikin wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar, Farfesa Ibrahim Abubakar Njodi, ya fitar, ya ce majalisar ƙaramar hukumar Akkon ta kuma dakatar da kansilan mazaɓar Kumo ta Gabas, Abdullahi M. Panda bisa wannan zargi. A baya-bayan nan ne dai rundunar 'yan sandan jihar ta yi baje kolin mutanen biyu da ta ce ta kama bisa zargin haɗa baki da ɓarayi wajen sayar da taransifomar lantarkin Garin Majidadi. Sanarwar ta ce, an…
Read More
Kwastom sun kama bindigogi 844 a tashar ruwan Ribas

Kwastom sun kama bindigogi 844 a tashar ruwan Ribas

Hukumar Kwastom a Nijeriya ta ce, ta kama makamai da harsasai da aka yi yunƙurin shiga da su ƙasar ta tashar ruwan Onne da ke Jihar Ribas. Da yake ba da sanarwar a yau Litinin yayin taron manema labarai, shugaban hukumar Adewale Adeniyi ya ce dakarun hukumar sun yi nasarar kama makaman ne tun ranar 21 ga watan Yuni. Ya ce bayan tattara bayanan sirri, dakarun sun lura da wata kwantena da ta fito daga ƙasar Turkiyya wadda ke ɗauke da bindiga 844 da kuma ƙunshin harsashi 112,500. "An ƙunshe su ne a cikin ƙofofi, da kayan ɗaki, da kayan…
Read More
Ta kashe mijinta kan ƙaramin siket

Ta kashe mijinta kan ƙaramin siket

Rikicin da ya ɓarke tsakanin wani mutum da matarsa ​​kan wata ƙaramin siket da matar ta saka ya yi sanadiyyar mutuwar mijin. Matsalar ta afku ne da daddare lokacin da mutumin mai suna Patrick John ya dawo gida daga mashaya, inda ya haɗu da matarsa ​​mai ciki sanye da ƙaramin siket, wanda a baya ya gargaɗe da ta daina sakawa. Ma'auratan na zaune ne a ƙauyen Faram Faram ne a ƙaramar hukumar Fufore da ke Yola a Jihar Adamawa. An tattaro cewa a ranar Litinin 13 ga watan Yuni, 2024, a wani rikici da ya ɓarke, mutumin ya ƙalubalanci matarsa…
Read More
Rai/ruhi da mutuwa

Rai/ruhi da mutuwa

Daga ALI ABUBAKAR SADIƘ Mene ne rai ko ruhi? Wannan tambaya ce da ta shige ma ɗan adam duhu tun farkon halittarsa. Ɗaiɗaikun mutane da addinai da dama sun yi iya ƙoƙarinsu wajen ganin sun gano bakin zaren wajen fahimtar rai. Amma babu wani addini da ya iya kawo cikakken bayani kafin zuwan Musulunci. Kafiran Makka, Yahudawa da Nasara na ƙalubalantar Annabi (SAW) da ya kawo musu mu'ujiza kamar yadda Allah ya ba mu labari cikin Suratul Ankabut Q29:50 "Kuma su ka ce "Don me ba a saukar masa da ayoyi (na mu'ujiza) daga ubangijinsa", sai Allah ya ba su…
Read More
Shugabannin Mali, Burkina Faso da Niger sun ƙulla sabuwar haɗaka bayan ficewa daga ECOWAS

Shugabannin Mali, Burkina Faso da Niger sun ƙulla sabuwar haɗaka bayan ficewa daga ECOWAS

Shugabannin soja na ƙasashen Niger,Mali da Burkina Faso sun ƙulla wata sabuwar haɗaka bayan ficewa daga tarayyar ECOWAS. Anyi wannan taron ne a babban birnin Niger, Niamey. Wannan haɗakar sun yi ta ne domin ƙarfafa alaƙa dake tsakanin kasashen ta ɓangaren tsaro da kuma tattalin arziki, wanda suka sanyawa suna "Alliance of Sahel State" (AES). Wannan taron shine ma farko da dukkanin shugabannin ƙasashen uku suka haɗu tun bayar hawan kowannen su ƙaragar mulki. Kuma yana zuwa watanni uku da ficewar su daga tarayyar ECOWAS. Tchiani, yayin magana a taron yace, ECOWAS ta zama barazana ga ƙasashen su, don haka…
Read More
An yi garkuwa da wakilan jaridun Blueprint da The Nation a Kaduna

An yi garkuwa da wakilan jaridun Blueprint da The Nation a Kaduna

A jiya ne muka samu rahoton garkuwa da wakilan Jaridar Blueprint da The Nation tare da iyalansu a gidajen su dake Danhono cikin garin kaduna. Ƙungiyar yan Jaridu ta ƙasa ita ta fitar da wannan sanarwa da sa hannun shugaban ta. Sun bayyana wannan hari a matsayin rashin imani tsantsa. Abdulraheem Aodu shine wakilin Jaridar Blueprint, yayin da Abdulgaffar Alabelewe shine wakilin The Nation. Sai dai masu garkuwar sun sako matar wakilin Blueprint saboda ba ta da lafiya sosai. Ƙungiyar ƴan jaridun reshen kaduna sun yi kira da gwamnati da jami'an tsaro da su hanzarta wanjen ganin an kuɓutar da…
Read More
Gwamnatin Tarayya ta ware Naira biliyan 1.5 ga furodusoshi don gudanar da ayyukan fim

Gwamnatin Tarayya ta ware Naira biliyan 1.5 ga furodusoshi don gudanar da ayyukan fim

Daga AISHA ASAS  A ƙarkashin tsarin 'Renewed Hope Agenda' na Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, Gwamnatin Tarayya ta raba wa masu shirya finafinai Naira biliyan ɗaya da rabi domin gudanar da ayyukansu. Wannan shiri wani ɓangare ne na Asusun Ƙirkira, mai kimanin Naira Biliyan 5, da aka ƙaddamar tare da haɗin gwiwa da Bankin Proɓidus a watan Disamba 2023. Tun daga farko dai an fara bayar da kuɗaɗen ne a watan Mayun shekarar 2024, kuma an ware Naira biliyan 1.5 ga ’yan wasa huɗu da furodusoshi. Fegho Umunubo, mataimaki na musamman ga shugaban ƙasa akan ƙirkirar zamani da ke ƙarƙashin…
Read More