ukarofi

11668 Posts
Shugaba Tinubu ya taya Sheikh Ɗahiru Bauchi murnar cika shekaru 100 a duniya

Shugaba Tinubu ya taya Sheikh Ɗahiru Bauchi murnar cika shekaru 100 a duniya

Shugaba Tinubu ya taya Sheik Ɗahiru Bauchi murnar cika shekaru 100 a duniya. Ya bayyana Sheik Ɗahiru Bauchi a matsayin mutum wanda ya sadaukar da rayuwar shi wajen bada ilmi da kuma haskaka rayuwar al'umma.. Sanarwar ta fito daga bakin mai bada shugaban ƙasa shawara bangaren kafafen sadarwa. Yace, Shehin malamin mutum ne daya sadaukar da rayuwar shi wajen bada ilmi da kuma zama jagora nagari wajen matasa masu tasowa.
Read More
Za mu ɗauki mummunan mataki kan duk wanda aka kama da laifin maɗigo da luwaɗi-Gwamnatin Kano

Za mu ɗauki mummunan mataki kan duk wanda aka kama da laifin maɗigo da luwaɗi-Gwamnatin Kano

Daga Rabiu Sanusi Gwamna Abba Kabir Yusuf na Jihar Kano ya bai wa hukumar Hisbah umarnin daukar mataki kan wa su kungiyoyi da ake zargin da koyar da Luwaɗi da Maɗigo a Jihar Kano. Umarnin na Gwamnan na zuwa ne bayan zargin ɓullar wasu ƙungiyoyi dake fakewa da tallafawa makarantu suna yaɗa mummunar dabi’ar auren jinsi a jihar. Kwamishinan yaɗa labarai na jihar Kano, Baba Halilu Dantiye ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ranar lahadin data gabata. Tun da farko dai kwamishinan ya ce gwamnatin jihar baza ta amince da auren jinsi ba…
Read More
Faɗuwa a siyasa ma nasara ce – Fatima Kadashi

Faɗuwa a siyasa ma nasara ce – Fatima Kadashi

Daga AISHA ASAS Sanannen abu ne mata a wannan zamani sun yunƙuro kan sha'anin siyasa, sun kuma nuna za su iya idan aka ba su dama ta ɓangaren riƙe madafun iko a ƙasar nan. Sai dai hakan ya zama wata barazana ga wasu mazan 'yan siyasa ganin cewa idan suka yi wasa hula za ta bi bayan ɗankwali ne a harkar siyasar Nijeriya. Wannan tunanin na su ne ya sa suke amfani da ƙarfin ikonsu wurin ganin sun hana mata kataɓus a fagen siyasa, ta hanyar danne su, su hana su motsi, har su gaji su gudu don ba inda…
Read More
MAKAMASHI: Babu inda ’yan tasha za su kai mu sai halaka

MAKAMASHI: Babu inda ’yan tasha za su kai mu sai halaka

Tare da BASHIR MUDI YAKASAI Najeriya da farkon fari, arzikin wannan ƙasa, musamman ma arewacin wannan ƙasa shine noman abinci da suka haɗa da dawa da gero da maiwa da rogo da makani (walihan) da doya, sannu a hankali alkama da sha’ir da shinkafa ’yar Hausa suka kankama suka zama ’yan gida duk da cewa farin wake da jan wake su na yi mu su dabaibayi. Sai da ta kai gidan kowa a duk kaka sai ka tarar da runbuna cike makil da abinci, babu abin da yake biyo baya illa bukukuwa na samari da ’yan mata da zawarawa har…
Read More
Gwamnatin Tarayya ta soke biyan haraji kan shinkafa,alkama da masara da aka shigo daga waje

Gwamnatin Tarayya ta soke biyan haraji kan shinkafa,alkama da masara da aka shigo daga waje

Gwamnatin Tarayya ta sanar da dakatar da haraji akan wasu nau'in abinci. Ministan Noma, Abubakar Kyari, ya bayyana wannan a lokacin taron manema labarai a cibiyar watsa labarai na Ƙasa, Abuja a ranar Litinin. Kyari ya bayyana cewa abincin sun haɗa da masara, alkama, shinkafa da wake. Gwamnati ta bada damar shigo da su ba tare da biyan haraji ba na tsawon kwanaki 150. Ya ƙara da cewa wannan mataki yana cikin Shirin gaggawa na Shugaban Ƙasa ya ɗauka domin rage hauhawar farashi da ke damun ƙasar. Ministan ya ce gwamnati ta na aiki tuƙuru don magance matsalar ƙaruwar farashin…
Read More
Kama sana’a ne mafita ga matasa- Pharm. Gali Sule

Kama sana’a ne mafita ga matasa- Pharm. Gali Sule

An yi kira ga matasa a Jihar Kano, musamman wanda suka kammala makaranta da ba su samu aiki ba, da su rungumi sana'o'i don kaucewa zaman kashe wando.Wannan kiran na zuwa ne daga bakin babban daraktan hukumar samar da magunguna da Kayan asibiti ta Jihar Kano. Famasist Gali Sule ne ya bayyana haka a lokacin da yake jawabi a gurin bikin cika shekara 10 da kammala makaranta da ƙungiyar tsofaffin ɗaliban makarantun sakandiren kimiyya da fassha ta Jihar Kano (KASSOSA) reshen makarantar kimiyya da ke garin Dawakin Kudu aji na shekarar 2014 (Class 2014) suka shirya a ranar lahadin nan.…
Read More
‘Ƴan bindiga sanye da hijabi sun yi garkuwa da mutane 25 a Katsina

‘Ƴan bindiga sanye da hijabi sun yi garkuwa da mutane 25 a Katsina

'Yan bindiga sanye da hijabi wanda aka fi sani da abaya sun sace mutane 26, mafi yawansu mata da yara,a wani hari da suka kai Runka da ke ƙaramar hukumar Safana ta Jihar Katsina. Al'ummar Runka tana 'yan kilomita kadan daga dajin Rugu wanda ya dade yana zaman mafakar 'yan ta'adda. Wani shaida ya sanar da Channels Television ta waya a ranar Litinin cewa 'yan bindigar sun kai hari a ranar Asabar da dare a wajen karfe 10:00 na dare. Ya ce 'yan bindigar suna ta harba wuta a ko'ina a cikin garin. Ya ce harin ya faru ne sakamakon…
Read More
A dawo da tallafin mai ko na kashe kaina, inji mutumin da ya haye ƙarfen sabis a Abuja

A dawo da tallafin mai ko na kashe kaina, inji mutumin da ya haye ƙarfen sabis a Abuja

Wani mutum da ba a san ko waye ba, ya haye ƙarfen sabis a Abuja, domin ya gaji da rayuwa saboda wahalar da ke ciki. Wani ɗan ƙaramin jawabi da ya ajiye, ya na cewa, a dawo da tallafin man fetur da kuma sauran matakan domin rage raɗaɗin ga yan Najeriya. Ya cigaba da cewa a shirye yake ya sadaukar da rayuwar shi in har waɗannan abubuwan basu samu ba. A cikin takardar ya cigaba da cewa, gwamnati ta ayyana dokar ta ɓaci a kan jihohin Katsina, Kaduna, Zamfara, Kebbi, Sokoto da Niger saboda rashin tsaro. Ya buƙaci gwamnati ta…
Read More
Gwamnan Zamfara ya sami kyautar Shugaban Ƙasa ta NEAPS

Gwamnan Zamfara ya sami kyautar Shugaban Ƙasa ta NEAPS

Daga USMAN KAROFI Gwamnan Zamfara Dauda Lawal ya sami kyautar NEAPS ta Shugaban ƙasa sabida ayyukan da gwamnatin shi ta assasa kuma ta kammala a cikin shekara guda Kyautar NEAPS wani sashi ne daga ofishin sakataren gwamnatin tarayya. Kamar yadda wata sanarwar ta fito daga bakin mai magana da yawun Gwamnan Sulaiman Bala Idris, ya shaida cewa an yi wannan bikin bada kyautar ne, ranar Asabar a babban ɗakin taro na fadar shugaban ƙasa. Sanarwar ta shaida Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima shi ya bada kyautar ga Gwamna Dauda Lawal a madadin Shugaba Tinubu. Sanarwar ta cigaba ta nuna cewa…
Read More
An yi garkuwa da tsohon Shugaban NLC na Ƙasa a ƙauyen Kaduna

An yi garkuwa da tsohon Shugaban NLC na Ƙasa a ƙauyen Kaduna

An yi garkuwa da tsohon shugaban NLC Takai Shamang a mahaifarsa Biniki da ke ƙaramar hukumar Kaura a Jihar Kaduna. Shamang, mai shekaru 78, ya kasance tsohon shugaban ƙungiyar ma'aikatan wutar lantarki da iskar gas ta ƙasa, a yanzu ƙungiyar ma'aikatan wutar lantarki ta ƙasa, tsakanin 1982 zuwa 1989. Da take tabbatar da hakan ga Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya, ɗiyarsa, Grace Abbin, ta ce an sace mahaifinta mai shekaru 78 a gidansa da ke Biniki, da misalin karfe 8:00 na daren ranar Juma’a. Shamang shi ne shugaba, kuma wanda ya kafa gidauniyar Gantys Aid for Widows, Orphans and Needy Foundation,…
Read More