ukarofi

11668 Posts
Majalisa na zargin Ministar Mata da kashe miliyan N75 wajen sayen ƙunzugun mata

Majalisa na zargin Ministar Mata da kashe miliyan N75 wajen sayen ƙunzugun mata

Ana zargin ministar harkokin mata ta Tinubu Uju Kennedy, da almundahana kuɗi kimanin naira miliyan 20 wajen sayen ƙunzugu na mata da kuma naira miliyan 45 wajen bikin sabuwar shekara. Wannan ya fito ne lokacin da aka gayyaceta majalisa domin tuhumar rashin biyan yan kwangila kuɗinsu, kimanin biliyan 1.5 bayan gwamnati ta biya wannan kuɗin. Amma minstar ta musanta zargin hakan, tace ya faru ne lokacin tsohuwar gwamnati. Tuhumar ta samo asali ne lokacin da ɗan kwangilar ya shigar da koke gaban majalisa. Akan ayyukan da yayi kuma an kasa biyanshi haƙƙinshi.
Read More
Gwamnatin Dauda za ta gina tashar mota ta zamani a Gusau

Gwamnatin Dauda za ta gina tashar mota ta zamani a Gusau

Gwamnan Jihar Zamfara ya amince da fara ginin sabuwar tashar mota na zamani a cikin Gusau, wanda takai kimanin N4,854,135,954.53. Aikin kwangilar a bada shi ga Fieldmark Construction ltd. Wannan na ɗaya daga cikin ayyukan raya birni wanda gwamnatin sa ke aiwatar wa. Wannan ya faru ne, a ranar Talata yayin zaman majalisar gudanarwa na gwamnatin, kamar yadda mai magana da yawun Gwamnan,Sulaiman Bala Idris ya shaida. Yace majalisar ta zanta akan abubuwa da dama wanda suka shafi cigaban mutanen Jihar Zamfara. Ma'aikatar ayyuka tare da Ma'aikatar Ƙananan Hukumomi su zasu ɗauki nauyin biyan wannan aiki. Sabuwar tashar za ta…
Read More
An kama ɗan shekara 80 da yin lalata da ‘yar shekara 10 a Bayelsa

An kama ɗan shekara 80 da yin lalata da ‘yar shekara 10 a Bayelsa

'Ƴan sanda a Jihar Bayelsa sun yi nasarar cafke wani dattijo mai shekaru 80 da zargin yin lalata da yar shekara 10. Lamarin ya faru a Otuakpoti dake ƙaramar hukumar Ogbia a Jihar Bayelsa. Mai magana da yawun yan sanda na Jihar, ASP Musa Muhammad ya tabbatar da faruwar lamarin, inda yace tuni an miƙa lamarin sashen binciken manyan laifuka domin cigaba da bincike. Bayanai sun nuna cewa, dattijon ya jima yana lalata da yarinyar har tsawon wata 12 kafin dubun shi ta cika. An sami nasarar cafke tsohon ne da taimakon wata ƙungiya mai rajin kare haƙƙin mata.
Read More
Sharhin littafin ‘Na Sake Ta’

Sharhin littafin ‘Na Sake Ta’

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU  SUNAN LITTAFI: Na Sake Ta!  MARUBUCI: Mustapha Abbas Rijiyar Lemo, Kano SHEKARAR WALLAFAWA: 2023  YAWAN KALMOMI: 2403 YAWAN SHAFI: 6 MAI SHARHI: Abba Abubakar Yakubu Littafin 'Na Sake Ta!' na Mustapha Abbas Rijiyar Lemo Kano, ƙaramin littafi ne da bai wuce shafi shida ba, da kalmomin da kaɗan suka haura dubu biyu da ɗari huɗu. Gajeren labari ne wanda marubucin ya nuna cewa ya faru da gaske, sai dai 'yan sauye-sauye na hikimar marubuci da aka yi, domin ɓatar da hankalin mai karatu daga sanin haƙiƙanin mutanen da abin ya faru da su.  Labarin wani mutum…
Read More
Arewa Media Writers ta shawarci gwamnoni kan martaba sarakuna da tsaro

Arewa Media Writers ta shawarci gwamnoni kan martaba sarakuna da tsaro

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU  A ƙarshen Babban Taron ƙungiyar Arewa Media Writers Association, da ta gudanar a garin Kaduna, an shawarci gwamnonin Arewa su kaucewa zubar da darajar sarautun gargajiya, saboda bambancin ra'ayin siyasa abin da ƙungiyar ke ganin rashin kishin Arewa ne ke haifar da haka. Ƙungiyar ta bayyana haka ne cikin takardar jawabin bayan taron da ta yi da shugabannin ƙungiyar a matakin ƙasa da jihohi, ƙarƙashin jagorancin sabon shugaban ƙungiyar na ƙasa Kwamred Haidar Hasheem Kano, inda ta fitar da wasu muhimman ƙudirori goma sha ɗaya. Ƙungiyar ta yi kakkausan suka ga abin da ta ce, wasa…
Read More
NPAN da NPC sun yi Allah wadai da garkuwa da wakilan Blueprint da The Nation a Kaduna

NPAN da NPC sun yi Allah wadai da garkuwa da wakilan Blueprint da The Nation a Kaduna

Ƙungiyar NPAN ta bayyana damuwarta kan lafiyar Abdulgafar Alabelewe da Mista AbdulRaheem Aodu, wakilan Jaridun The Nation da Blueprint na Jihar Kaduna. An sace su ne tare da iyalansu a Kaduna a daren ranar Asabar. Wata sanarwa da shugaban NPAN, Malam Kabiru A. Yusuf ya sanya wa hannu, ta ce: “Abin da ya fi daukar hankali shi ne shiru da aka ji daga masu garkuwa da mutanen da suka kama ‘yan jaridan tare da iyalansu da suka hada da mata da yara.” Malam Kabiru ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta tura jami’an tsaro domin ganin an ceto dan…
Read More
Tsohon ɗan wasan gaba na Liverpool, Firmino ya zama fasto

Tsohon ɗan wasan gaba na Liverpool, Firmino ya zama fasto

Tsohon ɗan wasan Liverpool Roberto Firmino ya sanar cewa ya zama limamin coci.Ɗan wasan na Brazil ya bayyana hakan ne a shafukansa na sada zumunta, inda ya bayyana wannan lamarin a mastayin gagarumin sauyi a rayuwarsa. Firmino, tare da matarsa, sun zama Fasto a cocin da suka kafa shekaru uku da suka wuce. An gudanar da bikin sadaukarwar ne a ranar Lahadin da ta gabata a garinsu na Maceio. A cikin saƙo mai ratsa zuciya, Firmino ya bayyana cewa zama fasto abu da ya sameshi bayan nazari mai zurfi cikin lamarin Yesu. “Tun lokacin da na fara nazari akan Yesu,…
Read More
Wasu ma’aikatanmu na  ba wa ‘yan bindiga bayanai – Shugaban Jami’ar Dutsinma

Wasu ma’aikatanmu na ba wa ‘yan bindiga bayanai – Shugaban Jami’ar Dutsinma

Shugaban Jami'ar Tarayya ta Dutsinma (FUDMA), Jihar Katsina, Farfesa Armaya'u Bichi, ya zargi cewa wasu daga cikin ma'aikatan jami'ar suna aiki a matsayin masu bayar da bayanai ga 'yan bindiga. Ya bayyana cewa 'yan bindiga sun yi ta kai hari a yankin, suna sace dalibai da ma'aikata na jami'ar da kuma 'yan'uwansu. Kwana bakwai da suka wuce, 'yan bindiga sun kai hari gidan Dr Tiri Gyan David, Shugaban Sashen Tattalin Arzikin Noma, faɗaɗa da bunkasar Karkara na jami'ar, suka kashe shi kuma suka sace 'ya'yansa. A ranar Talata, yayin wata ganawa da 'yan jarida, Bichi ya ce an ba da…
Read More
Kwamishinonin El-Rufai sun zargi Gwamna Sani da ƙoƙarin zubar ma sa da ƙima

Kwamishinonin El-Rufai sun zargi Gwamna Sani da ƙoƙarin zubar ma sa da ƙima

Tsohon Gwamnan Kaduna, Mal Nasiru Elrufa'i ya zargi Gwamna mai ci, Uba sani da ƙirƙirar ƙudin da babu, cewa an karkata su. Yace wannan bita da ƙulli ne kawai na siyasa. A wani taron manema labarai da tsofaffin Kwamishinonin Elrufa'i sun musanta zargin da ake ma Elrufa'i, sunce wannan kawai an faɗa ne amma babu gaskiya a cikin lamarin. Ana yin haka ne kawai domin cin mutunci. Kwamisshinonin wanda sukai aiki lokacin Elrufa'i sunce kuɗin da ake cewa an karkata babu su, sabida idan ka duba rahoton nasu, basu faɗi yadda suka samo su ba. Sun ƙara da cewa, idan…
Read More
An sako ‘ya’yan alƙalin da aka yi garkuwa da su a Kaduna

An sako ‘ya’yan alƙalin da aka yi garkuwa da su a Kaduna

Kwanaki 15 da yin garkuwa da ya'yan Alƙali Janet Galadima. Shugaban ƙungiyar lauyoyi ta Nijeriya, Barista Godwin Ochai ne ya sanar da haka. Sai dai mai magana da yawun 'yan sandan Jihar kaduna, ASP Mansir Hassan ya shaida cewa yan bindigar sun kashe cikin ya'yan mai shekara 14. Barista Ochai ya miƙa godiya ga Allah, da kuma addu'a Allah ba iyalan Alƙalin hakuri wannan iftilai.
Read More