ukarofi

11668 Posts
Tubabbun ’yan boko haram 560 sun fara koyon sana’o’i a Borno

Tubabbun ’yan boko haram 560 sun fara koyon sana’o’i a Borno

Daga SANI AHMAD GIWA a AbujaA ci gaba da ƙoƙarin dawo da tubabbun mayaƙan Boko Haram cikin jama’a, rukuni na 8 da ya ƙunshi mutane 560 sun fara karɓar horo a Maiduguri, Jihar Borno.Babban maƙasudin shirin shi ne baiwa tsofaffin ’yan ta’addan sana’a da ilimin da suka dace domin samun sake shiga cikin al’umma.Mashawarci na musamman kan harkokin tsaro a Jihar Borno, Birgediya-Janar Abdullah Ishaƙ (mai ritaya), ya ce za a koya wa tsofaffin ’yan Boko Haram ɗin sana’o’i daban-daban kafin a mayar da su yankunansu don sake haɗuwa da ’yan uwansu.A yayin horon, za su saurari laccoci daga ƙwararru…
Read More
Matsalar matsananciyar yunwa a Nijeriya

Matsalar matsananciyar yunwa a Nijeriya

An yi hasashen cewa 'yan Nijeriya miliyan 80 na iya fuskantar matsananciyar yunwa nan da shekarar 2030 idan ba a ɗauki matakan gaggawa ba don magance matsalar.  Hukumar Abinci da Aikin Gona ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce alƙaluma daga binciken shekara-shekara kan abinci sun nuna cewa nan da shekaru masu zuwa lamurra za su ta'azzara a ƙasar. Haka kuma MDD ta yi kira da gwamnatin ƙasar ta magance matsalar sauyin yanayi da matsalar ƙwari da sauran abubuwan da yi wa harkar noma barazana. A wurin wani taron kan haɓaka ayyukan noma a Abuja ne jami'in Majalisar, Taofiƙ Braimoh ya…
Read More
Tinubu ya yaba da hukuncin Kotun Ƙoli ’yancin ƙananan hukumomi

Tinubu ya yaba da hukuncin Kotun Ƙoli ’yancin ƙananan hukumomi

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya yaba da hukuncin da Kotun Ƙolin Nijeriya ta yanke a jiya, inda ta tabbatar da 'yancin ƙananan hukumomi. A sanarwar da fadar shugaban ta fitar bayan hukuncin a ranar Alhamis, shugaban ya ce hukuncin tamkar jaddada matsayin ƙaramar hukuma ne a kundin tsarin mulkin ƙasar. A hukuncinta na ranar Alhamis, Kotun Ƙolin Nijeriya ta ce iko da kuɗaɗen ƙananan hukumomi da gwamnoni ke yi ya saɓa wa kundin tsarin mulki. Alƙalin da ya jagoranci hukuncin Emmanuel Agim ya ce ƙananan hukumomi 774 na Nijeriya su ke da haƙƙin tafiyar da kuɗaɗensu da suke samu…
Read More
Shugaba Ruto na Kenya ya sallami ministocinsa

Shugaba Ruto na Kenya ya sallami ministocinsa

Shugaban ƙasar Kenya, Ruto ya sallami sukkan ministocinsa. Wannan na zuwa ne bayan shafe satuka da akai ana ta zanga zanga a ƙasar. Amma wannan sauyin bai shafi ofishin mataimakin shugaban ƙasa ba da sakataren ministocin. Ya cigaba da cewa, za suyi gana sosai da mutane da dama domin samun shawarwari ta yadda za a kafa gwamnati mai inganci. Wadda zasu shawo kan bashin da ke damun ƙasar, samar da ayyukan yi da yaƙi da cin hanci
Read More
An karɓe ikon Sarkin Musulmi kan hakimansa

An karɓe ikon Sarkin Musulmi kan hakimansa

Majalisar Sarkin Musulmi sun cire masa ikon naɗa hakimai a jihar, yayin da Gwamna Aliyu Ahmed ya sanya hannu a dokar da ta ba da ikon haka. Wannan dokar, ta cire wa sarkin Musulmin duk wani iko na naɗa hakimai da dagatai a faɗin Jihar Sokoto. Yayin bikin ƙaddamar da dokar, gwaman yace ba anyi dokar bane don muzantawa wani, sai dai domin ƙarfafa mulkin dimukraɗiya a faɗin Jihar. Ya cigaba da cewa, malamai da sarakunan gargajiya su daina bari yan siyasa suna amfani dasu wajen cin ma manufofinso na siyasa. A ranar dai ya sanya hannu ga dokar da…
Read More
Matsayin gara a mahangar magabata 

Matsayin gara a mahangar magabata 

(Ci gaba daga makon jiya) Daga AISHA ASAS  Mai karatu barkanmu da sake ganin zagayowar sati lafiya. Idan ba mu manta ba, kuma kuna biye da jaridar Manhaja, a makon da ya gabata, mun ɗauko bayani kan kayan da ake kai gidan miji da ke da suna gara a al'adance. Mun faro bayanin kan irin kallon da ma'anar da take da shi a tsakanin al'ummarmu, musamman ma a Ƙasar Hausa. Inda muka yi bayanin yadda muhimmancin ta ke rasiri a zamantakewar aure a wasu lokuta.  Mun yi bayanin yadda barin ta yafi zama alheri da wasu hujjojin da muka kawo,…
Read More
Shugaba Tinubu ya yi maraba da hukuncin Kotun Ƙoli kan cin gashin ƙananan hukumomi

Shugaba Tinubu ya yi maraba da hukuncin Kotun Ƙoli kan cin gashin ƙananan hukumomi

Shugaba Tinubu yayi maraba da hukuncin kotun ƙolin a kan cin gashin kan ƙananan hukumomi Shugaba Tinubu ya nuna murna ƙwarai dagaske a kan hukuncin da kotun ta yanke na ba ƙananan hukumomi damar cin gashin kansu. Wannan ya fito ne a wata sanarwa daga mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkar sadarwa, Ajuri Ngelale. Ya bayyana cewa wannan hukuncin ya bayyana irin ƙudurin da gwamnatin sa ke da shi wajen ganin mun bi doka a tsarin gyaran da muka zo dashi" Ya cigaba da cewa wannan ya zama dole saboda ƙananan ayyuka irin su saka fitilar titi, gyaran wasu…
Read More
An dakatar da shari’ar tsohon ministan Buhari bayan ya yanke jiki ya faɗi a harabar kotu

An dakatar da shari’ar tsohon ministan Buhari bayan ya yanke jiki ya faɗi a harabar kotu

An dakatar da shari'ar tsohon ministan wuta, Saleh Mamman a babbar koto dake Abuja saboda bashi da cikakkiyar lafiya. Tsohon ministan zai gurfana ne yau domin cigaba da shari'ar sa, amma ya yanke jiki ya faɗi. Wanda lauya mai kare shi, ya sanar Alƙalin halin da ake ciki lokacin da aka kira shari'ar. Tsohon ministan ya bayyana a gaban kotun ne, da kayan sa a jiƙe, wanda ya sanya alƙalin ya tambaye ko ruwa ake a waje. Mai shari'a Okong,ya tambayi tsohon ministan ko zai iya cigaba da tsayuwa, wanda yace zai iya. Ya faɗi ne saboda maganin da ya…
Read More
Sanata Kawu Sumaila ya gabatar da ƙudirin ƙirƙirar sabuwar Jiha daga Kano

Sanata Kawu Sumaila ya gabatar da ƙudirin ƙirƙirar sabuwar Jiha daga Kano

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Akwai yiwuwar samar da sabuwar jiha nan ba da jimawa ba, sakamakon yadda aka gabatar da ƙudirin kafa jihar Tiga daga Kano a majalisar dattawan Najeriya. Ƙudurin dokar wanda Sanatan Kano ta kudu Suleiman Abdurrahman Kawu Sumaila ya gabatar, wanda aka yi masa karatu na farko a ranar 10 ga Yuli, 2024. Ƙudirin doka mai taken “Constitution of the Federal Republic of Nigeria, 1999 (Alteration) Creation of Tiga State Bill, 2024 (SB.523)” na da nufin raba jihar Kano zuwa jihohi biyu, inda Tiga za ta zama sabuwar jihar da za a ƙirƙireta daga Jihar kano…
Read More