ukarofi

11668 Posts
Hisba da jami’an tsaro sun cafke mata da makaɗa 45 a kasuwar Tage da ke Jigawa

Hisba da jami’an tsaro sun cafke mata da makaɗa 45 a kasuwar Tage da ke Jigawa

Daga UMAR AkILU MAJERI Dutse A wani samamen haɗin gwiwa tsakanin dakarun hisba ‘yan sandan, jami’an civil defense da na ‘yan sandan farin kaya (DSS) da suka kai kasuwar ƙauyen Tage da ke Ƙaramar Hukumar Kafin Hausa a makon jiya sun sami nasarar damƙe mutane 45 da ake zargin su da fakewa da guzuma suna harbin karsana. Kwamandan Hisba na Shiyyar Kafin Hausa, Malam Abdulƙdir Zakari Kafin Hausa, shine ya tabbatar da faruwar hakan, inda ya ce, mutanen da suka kama ɗin sun haɗa da maza da mata da mawaƙan garaya da masu rawar bori da suke fakewa da sunan…
Read More
Ƙungiyar Hamas ta yi barazanar ficewa daga tattaunawar tsagaita wuta da Isra’ila

Ƙungiyar Hamas ta yi barazanar ficewa daga tattaunawar tsagaita wuta da Isra’ila

Jagoran ƙungiyar Hamas Isma’ila Haniyeh, ya ce farmakin da sojojin Isra’ila suka ƙaddamar kan tsakiyar birnin Gaza, ka iya rusa tattaunawar neman ƙulla yarjejeniyar tsagaita wuta da suke yi. Haniyeh ya yi gargaɗin ne bayan da dakarun Isra’ila cikin tankokin yaƙinsu suka kutsa cikin tsakar birnin yankin na Gaza a ranar Litinin, inda suka bai wa dubban Falasɗinawa umarnin barin garin, bayan da suka shafe daren Lahadi zuwa wayewar garin Litinin ɗin su na shan ruwan bama-bamai. Mazauna birnin na Gaza dai sun ce ruwan wutar da dakarun Isra’ila suka yi musu ta ƙasa da sama a baya bayan nan…
Read More
Barazanar da NATO ke fuskanta a daidai lokacin da ta cika shekaru 75

Barazanar da NATO ke fuskanta a daidai lokacin da ta cika shekaru 75

Shugaban Amurka Joe Biden ya fara karɓar baƙuncin takwarorinsa shugabannin ƙasashe manbobin Ƙungiyar Tsaro ta NATO, wadda ta cika shekaru 75 da kafuwa, a daidai lokacin da ƙungiyar ke ƙoƙarin daƙile barazanar yaƙin da Rasha ke yi a Ukraine, da kuma ƙarfin ikon da Chana ke gwadawa a yankin Asiya da Pasifik. Wani ƙarin ƙalubalen da shugabannin ƙasashen na NATO ke fuskanta yayin gudanar da wannan muhimmin taro shi ne rashin tabbas ɗin da ƙungiyar tsaron tasu ke fuskanta dangane da ɗorewarta. Duk da cewar yaƙin da Rasha ta ƙaddamar kan Ukraine shekaru biyu da suka gabata ya zaburar da…
Read More
Albashi: Yadda ta wakana tsakanin Tinubu da ƙungiyoyin ƙwadago

Albashi: Yadda ta wakana tsakanin Tinubu da ƙungiyoyin ƙwadago

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Shugaban Nijeriya Bola Tinubu a jiya Alhamis ya gana da shugabannin ƙungiyoyin ƙwadago na Nijeriya, NLC da kuma TUC kan batun sabon mafi ƙarancin albashin ma’aikata. To sai dai kuma tattaunawar ba ta kammalu ba, inda za a ci gaba da tattaunawa cikin sati mai zuwa kamar yadda rahotanni suka nuna. Zaman ganawar da Shugaba Tinubu ya kira, ya gudana ne a Ofishin Shugaban Ƙasa da ke fadar gwamnatin tarayya Abuja.  Da yake jawabi ga manema labarai bayan kammala taron da ya ɗauki tsawon sa’o’i biyu ana yi, ƙaramin minista a ma’aikatar ƙwadago da…
Read More
Shugaba Tinubu ya canza sunan Ɗakin Al’adu na Ƙasa zuwa Ɗakin Wole Soyinka

Shugaba Tinubu ya canza sunan Ɗakin Al’adu na Ƙasa zuwa Ɗakin Wole Soyinka

Shugaba Tinubu ya sauya sunan ɗakin al'adu na ƙasa zuwa zuwa Farfesa Wole soyinka. Shugaban yayi wannan sanarwa ne yayin saƙon taya murnar gwarzon bikin cika shekera 90. A wani sanarwa da Ajuri Ngelale ya sa wa hannu, ya ce " a yau na taya duniya da samun mutum mai zaburar da matasa. Da irin rawar da ya taka wajen yaƙar mulkin soja. Ya kara da cewa,hanyar su ta haɗu wajen gwagwarmaya neman dimukraɗiya. Sai daga ƙarshe shugaban ya taya gwarzon murna cika shekaru 90, tare da lafiya mai ɗorewa
Read More
Ba mu ce Gwamnatin Tarayya ta dakatar da ‘Yarjejeniyar Samoa’ ba – Majalisa ta yi amai ta lashe

Ba mu ce Gwamnatin Tarayya ta dakatar da ‘Yarjejeniyar Samoa’ ba – Majalisa ta yi amai ta lashe

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Majalisar wakilai ta yi watsi da rahotannin da ke cewa ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta dakatar da aiwatar da yarjejeniyar haɗin gwiwa ta Samoa. Kakakin majalisar, Akin Rotimi ne ya bayyana hakan a ranar Laraba. Rotimi, wanda ke wakiltar mazaɓar Ikole/Oye, jihar Ekiti, ya ce saɓanin yadda kafafen yaɗa labarai suka riƙa yaɗawa, ‘yan majalisar sun yanke shawarar yin bincike a kan wasu batutuwan da ke cike da cece-kuce a cikin yarjejeniyar don tabbatar da cewa ba su saɓa wa tanadin kundin tsarin mulkin 1999 (kamar yadda aka gyara). Ɗan majalisar…
Read More
IMF da Bankin Duniya ba za su hana mu kifar da kai ba a 2027 – Ɗan El-Rufai ya caccaki Tinubu

IMF da Bankin Duniya ba za su hana mu kifar da kai ba a 2027 – Ɗan El-Rufai ya caccaki Tinubu

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Bashir El-Rufai, ɗan tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya caccaki Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, yana mai cewa babu wata cibiya a cikin gida ko kuma na ƙasashen waje da za ta hana a kada shi a zaɓen 2027. Bashir ya ce babu wanda ya kai girman da jama'a za su zaɓe shi daga muƙaminsa, yana mai gargaɗin cewa hakan ba zai faru ba. Ya ƙara da cewa mutane su manta da duk wata barazana da ake ta shawagi sama da ƙasa, yana mai cewa su yi haƙuri. Ya ce, “Ba wanda ya…
Read More
Gine-gine da fentin makarantu ba shi ne zai warware matsalar ilimi ba – Farfesa Kamilu Sani

Gine-gine da fentin makarantu ba shi ne zai warware matsalar ilimi ba – Farfesa Kamilu Sani

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano Taron tattaunawa akan makomar ilimi da aka yi a Kano abu ne mai kyau, amma masu aiwatar da manufofi da aka cimma shi ne abin kokwanto, za a kawo takardu da shawarwari a bai wa gwamnati anan siyasa take shigowa inda za a ga any i biris da waɗannan sakamako da aka tsara za a aiwatar.Farfesa Kamilu Sani Fagge ɗaya daga cikin mahalarta taron da aka gudanar a Jami'ar Bayero ne ya bayyana hakan da yake zantawa da 'yan jarida a wajen taron.Ya ce waɗanda alhaki ke kansu na su ga an farfaɗo da ilimi…
Read More
Ba gudu ba ja da baya kan N250,000 mafi ƙarancin albashi – TUC

Ba gudu ba ja da baya kan N250,000 mafi ƙarancin albashi – TUC

Daga SANI AHMAD GIWA a AbujaHar yanzu ƙungiyar ƙwadago ta dage kan cewa N250,000 ta kasance mafi ƙarancin albashi ga ma’aikata a Nijeriya, in ji Shugaban Ƙungiyar Ƙwadago Festus Osifo a ranar Talata.Osifo ya kuma bayyana cewa TUC da ƙungiyar ƙwadago ta Nijeriya suna ganawa da jami’an gwamnatin tarayya domin cimma matsaya kan mafi ƙarancin albashi.Ya bayyana hakan ne a babban taron ƙungiyar mata da man fetur da iskar gas a Abuja, mai taken ‘The Dynamic Woman: Naɓigating Challenges in a Constantly Eɓolɓing World’.Tattaunawa kan sabon mafi ƙarancin albashin ma’aikata ya tsaya cik bayan shawarar da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu…
Read More
Tsadar rayuwa: Ina guje mana fushin talakawa – Sanata Lawan ya gargaɗi gwamnati

Tsadar rayuwa: Ina guje mana fushin talakawa – Sanata Lawan ya gargaɗi gwamnati

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Tsohon shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawan, ya gargaɗi gwamnatin tarayya da ta gaggauta magance matsalar ƙarancin abinci da kuma ƙarin kuɗin wutar lantarki domin kaucewa zanga-zangar talakawa da ka iya jefa ƙasar cikin ruɗani.Gargaɗin nasa na zuwa ne a daidai lokacin da al’amura ke ƙara taɓarɓarewa a Kenya, inda zanga-zangar adawa da matakin da gwamnati ta ɗauka na ƙara haraji ta rikiɗe zuwa neman ingantaccen shugabanci da kuma rajin cewa Shugaba William Ruto ya yi murabus.Sanata Lawan (APC/Yobe ta Arewa) ya bayyana hakan ne a yayin zaman majalisar na ranar Talata, yayin da…
Read More