14
Jul
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Muhammad ya shaida wa BBC cewa lambar yabon da wata gidauniya da haɗin gwiwar gwamnatin Nijeriya suka karramashi da ita, babbar nasara ce.Sanata Bala ya ce an ba shi lambar yabo ta ayyukan birane, sakamakon irin ayyukan da gwamnatinsa ke yi a jihar Bauchi, ya kuma ce a yanzu zai mayar da hankali kan ƙara inganta tsaro a jiharsa.''Tsaro na ɗaya daga cikin abin da zai kawo huɓɓasa wajen ci gaban garuruwa da biranen da ƙauyukanmu, idan ƙauyuka ba su zauna lafiya ba, to kuwa birane ba za su…
