ukarofi

11668 Posts
An saki wakilan Blueprint da The Nation da akai garkuwa da su

An saki wakilan Blueprint da The Nation da akai garkuwa da su

Alamu sun nuna cewa, wakilan Jaridar Blueprint da The Nation Abduraheem Aodu and Abdulgafar Alabelewe sun sami ƙuɓuta daga hannun wanda suka yi garkuwa dasu. Wannan ya fito ne daga bakin shugabar ƙungiyar yan jaridu na ƙasa reshen Jihar Kaduna, Asma'u Yawo Halilu. Ta bayyana wannan saƙon ne ta manhajar WhatsApp inda ta ce" ƙungiyar na miƙa sakon jinjina ga rundunar ƴan sanda reshen jihar kaduna da kuma sauran jama'a wanda suka taya mu addu'a wannan lokacin" Jaridar Blueprint ta gano cewa ƴan jaridun suna hanyar zuwa Abuja.
Read More
Me yake tunzura mata suke wa maza kisan gilla?

Me yake tunzura mata suke wa maza kisan gilla?

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Wasu rahotanni da suka mamaye kafafen watsa labarai a 'yan makwannin da suka gabata, na nuni da wani abu mai tsoratarwa na faruwa a gidajen aurenmu, kuma akwai haɗarin gaske idan aka bari ya cigaba ba tare da an ɗauki matakin da ya dace wajen kawo ƙarshensa ba. Kodayake ba sabon abu ba ne, amma yawaitarsa a wannan lokaci na bayyana cewa, jama'a sun fara kai wa maƙura.  Daga farkon wannan shekara kaɗai an samu rahotanni daban-daban dake bayyana yadda wasu matan aure suka yi sanadiyyar hallaka mazajensu na aure sakamakon dalilai mabambanta, wanda suka shafi…
Read More
MZOUGH U TIV ta ƙaryata zargin da ƙabilar Alago ta yi mata a Nasarawa

MZOUGH U TIV ta ƙaryata zargin da ƙabilar Alago ta yi mata a Nasarawa

  Daga JOHN D. WADA, a LAFIYA Ƙungiyar Cigaban Al’ummar Ƙabilar Tibi na Duniya, wadda da ake fi sani da MZOUGH U TIV, reshen jihar Nasarawa ta ƙaryata wani zargi da wata ƙungiyar ƙabilar Alago a jihar ta yi cewa 'yan ƙabilar ta Tibi suna kai hare-hare da yi wa al’ummarsu ta Alago kwantan ɓauna a yankunan Ƙaramar Hukumar Keana a jihar. Shugaban ƙungiyar ƙabilar Tibin na reshen jihar Nasarawa, Kwamared Philip Nongu ne ya bayyana haka a cikin wata takardar bayan taro wanda aka raba wa manema labarai a Lafiya fadar gwamnatin jihar ranar Laraba 10 ga watan Yulin…
Read More
NYCN ta nemi haɗin kan al’umma wajen daƙile shan miyagun ƙwayoyi a Nijeriya

NYCN ta nemi haɗin kan al’umma wajen daƙile shan miyagun ƙwayoyi a Nijeriya

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Dangane da muguwar yawaitar shaye-shayen miyagun ƙwayoyi a tsakanin matasa, Ƙungiyar Matasa ta Ƙasa (NYCN) da Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa NDLEA) na neman haɗin kan al’ummomi da ƙungiyoyi wajen yaƙi da miyagun ƙwayoyi a Nijeriya. Dangane da rahoton ƙwayoyi na duniya na 2021, wanda Ofishin Majalisar Ɗinkin Duniya kan Ƙwayoyi da Laifuka (UNODC) ya fitar, kusan mutane miliyan 275 ne ke amfani da ƙwayoyi a duk duniya, yayin da sama da mutane miliyan 36 ke fama da matsalar shan muggan ƙwayoyi. Wani bincike da aka gudanar a shekarar 2018 ya…
Read More
Mai shari’a Dije Aboki ta yaba wa Shugabar FIDA

Mai shari’a Dije Aboki ta yaba wa Shugabar FIDA

Daga MUHAMMADU MUJJITABA a Kano Babbar Mai Shara'a ta Jihar Kano, Hon Dije Aboki ta yaba wa shugabar Ƙungiyar Mata Lƙuyoyi ta Ƙasa, reshan Jihar Kano Baristar Hajiya Bilkisu Ibrahim Sulaiman, dangane da yadda ta ke ƙoƙari wajen tabbatar da samun haƙƙin marasa galihu da kuma ƙoƙarin bunƙasa ilimin mata lauyoyi da sauran al'amura na ciyar da al'umma. Ta ce,  a wannan lokaci na shugabancin Hajiya Bilkisu Ibrahim Sulaiman, shugabar ƙungiyar mata lauyoyi da ake kira FIDA babbar mai shara'a ta Jihar Kano Hon Dije Aboki, ta bayana haka ne a lokacin da ayyarin lauyoyi mata ƙarƙashin shugabancin shugaban FIDA…
Read More
Dole ne Atiku, Obi, Kwankwaso, Ameachi su haɗa kai domin kada Tinubu a 2027 – Lukman

Dole ne Atiku, Obi, Kwankwaso, Ameachi su haɗa kai domin kada Tinubu a 2027 – Lukman

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Tsohon Mataimakin Shugaban Jam’iyyar APC mai mulki a shiyyar Arewa maso Yamma, Salihu Lukman, ya koka da yadda al'ummar ƙasar nan ke ƙara shiga mawuyacin halin tsadar rayuwa, inda ya buƙaci wasu jiga-jigan ‘yan siyasa da su haɗa kai su fatattaki gwamnatin Shugaba Bola Tinubu. “Shugabannin siyasa a Nijeriya, musamman Alhaji Atiku Abubakar, Mista Peter Obi, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, Farfesa Yemi Osinbajo, Cif Rotimi Amaechi, Dr. Kayode Fayemi, Sanata Ibikunle Amosun, Malam Nasir El-Rufai, Ogbeni Rauf Aregbesola, da dai sauransu dole ne su amsa tambayar ko suna son su kyale ƙunƙun manufofinsu na…
Read More
Gwajin maganin cutar mantuwa

Gwajin maganin cutar mantuwa

Ƙwayar magani ta farko da take taimakawa wajen rage lalacewar ƙwaƙwalwa ta samu yabo a matsayin mai muhimmanci. Binciken ya kawo ƙarshen shekarun da aka shafe ba tare da nasara ba kuma ta ba da damar samun maganin cutar Alzheimer's - nau'i mafi shahara na cutar mantuwa. Sai dai ya zuwa yanzu tasirin maganin na lecanemab ba shi da yawa kuma ana ta tafka muhawara game da aikinsa a rayuwar mutane. Ƙwayar na aiki ne tun a farko-farkon cutar, saboda haka wasu da dama maganin ba zai musu amfani ba idan ba a yi sa'ar gano ta da wuri ba.…
Read More
Ma’aunin talauci na Nijeriya

Ma’aunin talauci na Nijeriya

Assalam alaikum. Ina yi wa jaridar Blueprint Manhaja fatan alheri. Wani sabon rahoto ya tabbatar da cewa aƙalla ’yan Nijeriya miliyan 133 ne ke fama da talauci. Wannan na ƙunshe ne a cikin sabuwar ƙididdigar Talauci ta Nijeriya da Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS) ta fitar kwanan nan a Abuja. Sabuwar alƙalumman talauci na wakiltar kusan kashi 63 cikin 100 na al'ummar ƙasar. An gudanar da binciken tsakanin Nuwamba 2021 da Fabrairu 2022. Ambaliyar ruwa ta baya-bayan nan a faɗin ƙasar, wacce ta lalata gidaje da rayuwa da kuma nitsewar filayen noma a jihohi da dama na tarayyar ƙasar, mai…
Read More
Abin da ya sa na ke yin waƙa da kayan kiɗan gargajiya – Alan Waƙa

Abin da ya sa na ke yin waƙa da kayan kiɗan gargajiya – Alan Waƙa

DAGA MUKHTAR YAKUBU Da alama dai mawaƙi Aminu Ladan Abubakar Ala ya zama mazari ba ka gaba a fagen waƙa ta yadda duk inda ya sa gaba sai yanayin ya dace da shi. Shi mawaƙin fada ne, mawaƙin siyasa ne mawaƙin 'yan kasuwa, baya ga kasancewar sa mawaƙin faɗakarwa. Wani salo da mawaƙin yake da shi wanda ya bambanta shi da sauran mawaƙa shi yanayin waƙar da yake yi da kowanne salo ba ki. Kamar yadda ya yi waƙa Kukuma, ya yi waƙa da tafi ya yi waƙa da Bandiri. Kuma a 'yan kwanakinnan aka ji shi ya fitar da…
Read More
Patience Ozokwor na bayyana kishiyar halinta na zahiri a finafinai – Kanayo O. Kanayo

Patience Ozokwor na bayyana kishiyar halinta na zahiri a finafinai – Kanayo O. Kanayo

Daga AISHA ASAS  Idan aka ambaci sunan jarumi Kanayo O.Kanayo, abu na farko da zai zowa mai saurare shi ne, tsafi da makamantansu, wanda har a 'yan baya-bayan nan an samu masu wasannin barkwanci suna amfani da sunansa don isar da saƙo. Kamar yadda na gani a kwanaki, wani matashi ya yi niyyar yaudarar wata yarinya, har ya fara gaya mata mai zafi, amma tana sanar da shi cewa, Kanayo O. Kanayo ne babanta sai ya fara kuka. Akwai kuma wani wanda ya je wurin mai nama, ya ce, a yanka masa na kuɗi kaza, bayan ya gama, sai mutumin…
Read More