ukarofi

11668 Posts
Jan da Els: Ma’auratan da soyayya ta sa suka yanke shawarar mutuwa tare

Jan da Els: Ma’auratan da soyayya ta sa suka yanke shawarar mutuwa tare

Jan da Els ma'aurata ne da suka kwashe kusan shekara 50 da aure. Sun mutu tare a farkon watan Yuni, da taimakon likitoci biyu da suka ba su maganin da ya taimaka masu suka mutu. Jan da Els sun haɗu ne a makaranta a ajin rainon yara a lokacin suna ƙananan yara, sun kwashe tsawon rayuwasu suna soyayya. A lokacin Jan yana matashi yana bugawa ƙungiyar ƙwallon hockey ta ƙasar Netherlands wasa. Inda daga bisani ya zama kocin ƙungiyar. Els malamar makarantar firamare ce. A ƙasar Netherlands, hakan ba laifi ba ne, ya halasta, sai dai hakan bai yi fice…
Read More
Muhimmancin yawan shan ruwa

Muhimmancin yawan shan ruwa

Tare da MUSTAPHA IBRAHIM ABDULLAHI A yawaita shan ruwa: Ruwa abokin aiki ne, musamma a duniyar da ke kewaye da mu da kuma duniyar cikin jikinmu, domin jikin ɗan adam wata duniya ce mai zaman kanta. Sama da kaso 60 na jikin ɗan adam duk ruwa ne. Alƙurani ya jaddada mana cewa kowanne abu mai rai yana ɗauke da ruwa. Abinda ya sa mu ke cewa kusha ruwa sosai sun haɗar da: 1. Saboda ku maye gurbin ruwan da kuka rasa lokacin gumi, magana, numfashi, bayangida, da kuma fitsari. 2. Saboda ku kaucewa afkawa cikin illolin karancin ruwan jiki (dehydration).…
Read More
Nijeriya ina mafita? – Daga Uncle Larabi

Nijeriya ina mafita? – Daga Uncle Larabi

Daga ABDULLAHI JIBRIL LARABI (UNCLE LARABI) Wallahil azim! Idan ba mu yi wasa ba zuwa ƙarshen shekarar nan (2024) komai zai sake yin tsada ne fiye da yadda yake tsada a yanzu. Idan kuma mu ka sake sakankancewa wallahi kafin Tinubu ya sauka daga mulki, wanda ya ke da rabon gani (Allah ya sa mu ma mu na da rabon ganin ƙarshen mulkin nasa da na wasu ma) za a sha wahala ba kaɗan ba ta hauhawar farashin kayan masarufi. A yanzu da na ke rubutun nan, ko kun san farashin Dala ɗaya ya haura Naira 1545. Farashin kayan masarufi…
Read More
Luwaɗi da maɗigo a rumfar mulhidanci – Nazarin Ali Abubakar Sadiƙ

Luwaɗi da maɗigo a rumfar mulhidanci – Nazarin Ali Abubakar Sadiƙ

Daga ALI ABUBAKAR SADIƘ A tarihin duniya, ba a taɓa samun guguwar wata aƙida da ta yaɗu cikin gaggawa irin ta ’yan luwaɗi da maɗigo ba (wadda ake wa laƙabi da LGBTƘ). Ba za a fahimci hakan ba sai an bibiyi tarihin wannan ƙungiya da ga kafuwarta zuwa yanzu a Amurka, wato Sodom (garin Annabi Ludu) na zamaninmu. A ƙarni na 19 kaf da kuma farkon ƙarni na 20, yin luwaɗi a Amurka babban laifi ne da ke da hukuncin ɗauri. Kuma har zuwa shekarun 1950 akwai ƙungiyar ƙyamatar luwaɗi da ake wa laƙabi da McCarthyism, waɗanda ke farautar ’yan…
Read More
Kotu ta tabbatar da Sanusi a matsayin Sarkin Kano

Kotu ta tabbatar da Sanusi a matsayin Sarkin Kano

Babbar Kotun Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Amina Adamu Aliyu ta tabbatar Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II a matsayin halastaccen Sarkin Kano, inda kotun ta tabbatar da halascin sabuwar Dokar Masarautar Kano, wacce Gwamna Abba Kabir Yusuf ya rattaɓa wa hannu. A yayin da ta ke yanke hukuncin, Alƙali Amina Aliyu ta kuma bayyana cewa, gazawar jami’an tsaro wajen tabbatar da an aiwatar da sabuwar dokar, shi ma saɓa wa dokokin ƙasa ne.Haka nan ta kuma yanke hukuncin cewa, waɗanda ake ƙara ba su da hurumin hana Majalisar Dokokin Jihar Kano kafa doka a jihar.
Read More
Spain ta yi nasarar lashe gasar Kofin Turai

Spain ta yi nasarar lashe gasar Kofin Turai

Spain tayi nasarar lashe gasar turai ta 2024. Mikel Oyarzabal shine yayi nasarar jefa ƙwallo cikin ragar Ingila a mintunan ƙarshe na wasan. Wasan dai ya ƙayatar sosai. Spain ita ta fara zura ƙwallo a ragar Ingila, yayin da ɗan wasan Chelsea cole palmer ya farke ma Ingila. Sai dai wasan an kai ruwa rana domin sai a mintuna na 86, Spain ta samu nasarar zura ƙwallo ta biyu. Wanda yasa aka tashi wasan 2-1. Ingila ta kasance har yanzu tana neman nasara a gasar turai. Amma abun yaci tura.
Read More
Da Ɗumi-Ɗumi: PDP ta lashe duka kujerun shugabannin ƙananan hukumomin Adamawa

Da Ɗumi-Ɗumi: PDP ta lashe duka kujerun shugabannin ƙananan hukumomin Adamawa

Jam'iyyar APC ta sha kashi a hannun Jam'iyyar PDP a zaɓen shugabannin ƙananan hukumomin Jihar Adamawa. Wannan ya fito ne bayan da hukumar zaɓe ta Jihar Adamawa ta bayyana sakamakon zaɓen. Ta bayyana cewa dukkanin kujerun Jam'iyyar PDP ce ta lashe tare da kansiloli. Sai dai Jam'iyyar NNPP tayi nasarar lashe kujerar kansila ɗaya. Hukumar ta tabbatar cikin jami'u 19, guda 12 ne kaɗai suka shiga zaɓe. Wannan zaɓen shine na farko da akayi bayan hukuncin kotun ƙoli a kan cin gashin kai na ƙananan hukumomi.
Read More
An kashe wanda ake zargi da yunƙurin kashe Trump

An kashe wanda ake zargi da yunƙurin kashe Trump

Jami'an hukumar FBI sun tabbatar da kashe wanda ake zargi da yunƙurin kashe tsohon Shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump. Sunce sunyi nasarar kashe Thomas Mathew crook, ɗan shekara 20 daga Pennsylvania. A farkon sanarwa da suka bayar, sun ƙi yadda su bayyana sunan wanda ake zargin. Saboda a cewar su lokacin suna ta bincike kuma basu shirya faɗan wanda ya aikata wannan laifin ba. Sai dai yan sandan Pennsylvania sun tabbatar da cewa yanzu, suna da tabbacin cewa babu wani abu mai ban tsoro irin wannan da sake faruwa.
Read More
Jihar Zamfara ta yi zarra a Arewa a jarrabawar NECO 2024

Jihar Zamfara ta yi zarra a Arewa a jarrabawar NECO 2024

Daga USMAN NASIR KAROFI a Abuja Jihar Zamfara ta shiga jerin jihohin Arewa da su ka yi abun a zo a gani a jarrabawar NECO lokacin da hukumar ta fitar da sakamakon jarrabawa na rukunin ɗalibai masu hazaƙa. Wannan ya fito ne a wata sanarwa da mai magana da yawun gwaman jihar, Sulaiman Bala Idris, ya yi. Ya bayyana cewa a faɗin kasar, Jihar Zamfara ita ce ta zo na biyu da ɗalibai 35, yayin da Jihar Anambra ta zo na farko. Ya bayyana cewa, a karo na farko Jihar Zamfara ta zo na biyu a wannan jarabawar wanda ɗalibai…
Read More
Hukumar FBI ta tabbatar da yunƙurin kashe Trump a yayin yaƙin neman zaɓe

Hukumar FBI ta tabbatar da yunƙurin kashe Trump a yayin yaƙin neman zaɓe

Hukumar FBI ta tabbatar da yunƙurin kashe tsohon Shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump a yayin yaƙin neman zaɓe a Butler, Pennsylvania. Wanda yayi yunƙurin yanzu haka ya mutu da wani mutum guda ɗaya. Sai kuma wasu jami'an tsaro da sun jikkata sosai, suna asibiti suna amsar kulawa. FBI ta fitar da sanarwa cewa " mun tabbatar da yunƙurin kashe tsohon shugan ƙasa Donald Trump a Pennsylvania." Sai dai hukumar baga bayyana sunan wanda ke da alhakin kai wannan mummunan harin ba.
Read More