20
Jun
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya ba da tabbacin cewa gwamnatin tarayya na ƙoƙarin haɗa kai da sarakuna domin domin ɗabbaƙa zaman lafiya da tsaro da haɗin kan ƙasa da cigaba mai ɗorewa a faɗin Nijeriya. A yayin da yake wakiltarsa a yayin zaman kwamitin majalisar sarakuna (NTRC) karo na 8 a Dutsen jihar Jigawa a ranar Litinin, ministan yaɗa labarai da wayar da kan al’umma Mohammed Idris, ya miƙa saƙon shugaban ƙasa ga sarakunan da suka haɗu daga yankin Arewa. “Gwamnatin Shugaba Tinubu tana sane da irin rawar da kuke takawa kuma a shirye…
