20
Jun
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya sake jaddada cewa jihar na ci gaba da samar da yanayi mai kyau ga harkokin kasuwanci da zuba jari, ta hanyar daidaita manufofinta da ajandar sauye-sauyen Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu. Gwamnan ya ce, tsawon shekaru jihar ta aiwatar da wasu muhimman gyare-gyare da suka haɗa da ƙara gaskiya a harkokin gwamnati, ƙarfafa cibiyoyi, sauƙaƙa hanyoyin gudanarwa, ƙarfafa zuba jari da kuma inganta ayyukan hidima ga jama'a. Uba Sani ya bayyana hakan ne a zaman fasaha na taron Majalisar Shugaban ƙasa Kan Samar da Sauƙin Gudanar da…
