10
Jun
Daga IBRAHIM MUHAMMAD Asalin su Fulani ne da suka fito daga yankin Ningi ta Jihar Bauchi da zummar za su kai caffa a wajen Mujaddadi Shehu Usman ɗanfodiyo Tagammadahullahu birahamatihi a Sakkwato domin shiga dumu-dumu a cikin jihadin jaddada addinin Musulunci wanda Mujaddadi Shehu Usman ɗanfodiyo ya jagoranta. Sun zauna a wurare da dama kamar ƙiru da Gwarzo (da ke Jihar Kano ta yau) da Matazu da Fawwa ( dake Jihar Katsina a halin yanzu) da kuma Wonaka da ke Jihar Zamfara ta yanzu, kafin daga bisani Malam Muhammadu Sambo ya jagorance su ya zuwa inda suke a halin yanzu.…
