ukarofi

12553 Posts
Shin yunƙurin mayar da Nijeriya mai jam’iyya ɗaya zai yiwu kuwa?

Shin yunƙurin mayar da Nijeriya mai jam’iyya ɗaya zai yiwu kuwa?

A cikin ’yan watannin nan, muhawara ta sake ɗaukar zafi a fagen siyasar Nijeriya kan yiwuwar ƙasar ta koma ƙarƙashin tsarin da jam’iyya guda ɗaya ke mamaye siyasa. Wannan muhawara ta samo asali ne sakamakon yawaitar sauya sheƙa da wasu manyan ’yan siyasa ke yi daga jam’iyyun adawa zuwa jam’iyyar da ke mulki, lamarin da ya sa wasu masu sharhi ke gargaɗin cewa dimokuraɗiyyar Nijeriya na iya fuskantar barazana idan ba a samu ƙarfi da daidaito tsakanin jam’iyyun siyasa ba. Sai dai tambayar da ake yi ita ce: Shin da gaske Nijeriya na daf da zama ƙasar jam’iyya ɗaya? Kuma…
Read More
Akan satar ‘yan makaranta: Ina aka kwana?

Akan satar ‘yan makaranta: Ina aka kwana?

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Zuciyata na cike da ƙunci da takaici dangane da halin da ƙasar mu ke ciki na jimamin satar yara ’yan makaranta da malamai a Jihar Oyo, bayan garkuwa da aka yi da wasu 'yan makaranta da har yanzu suke hannun ’yan ta'adda a wata makaranta a Jihar Borno. Ga wanda bai sani ba ko ba shi da cikakken labarin abin da ya faru. A wata ranar Jumma'a ta 15 ga watan Mayu ne dai wasu ’yan bindiga suka sace ɗalibai ’yan firamare 39 ciki har da ɗan shekara biyu da haihuwa da malamansu guda 7 daga…
Read More
Gamji Uban Fita Kunya!

Gamji Uban Fita Kunya!

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA Kai tsaye a wannan kafa na kawo bayanan jami’i a gidan rediyon Biyafara Chinasa Nworu ya faɗi burinsu kan Arewa na wargaza yankin da maida shi ‘yan garuruwa ƙarƙashin mulkin ƙabilu. Nworu ya fito da hoton ‘yan karyar Hausa zalla da dama ba su da wata alaƙa da Hausawa ya jinjina mu su. Yanzu haka wasu daga gaggan ‘yan kwangilar karya ta Hausa zalla sun koma aiki kai tsaye da ‘yan IPOB kuma hakan ta tabbata a shafin Anyamuri Madu lion AJaja da ke Teɗas a Amurka. Tun watannin baya IPOB ke kashe dala 60,000 wato…
Read More
‘Yan bindiga sun sace dattawa 50 da suka je tattaunawar sulhu a Zamfara

‘Yan bindiga sun sace dattawa 50 da suka je tattaunawar sulhu a Zamfara

Daga USMAN KAROFI Aƙalla dattawa 50 daga ƙauyen Magamin Diddi da ke yankin Magami/Faru a ƙaramar hukumar Maradun ta jihar Zamfara sun faɗa hannun 'yan bindiga yayin da suka je wata tattaunawar sulhu da shugaban 'yan bindiga da aka fi sani da Jammo. Shugaban ƙaramar hukumar Maradun, Bello Dosara, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana cewa mutanen sun je ganawa da shugaban 'yan bindigar ba tare da amincewar gwamnati ba. Ya ce gwamnatin jihar Zamfara ƙarƙashin Gwamna Dauda Lawal ba ta goyon bayan yin sulhu da 'yan bindiga, amma al'ummar yankin sun yanke shawarar yin hakan da kansu.…
Read More
Fusatattun matasa sun kori sojojin da aka tura Zurmi a Zamfara

Fusatattun matasa sun kori sojojin da aka tura Zurmi a Zamfara

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau A cigaba da samun hare-haren 'yan ta'adda a wasu yankuna a Jihar Zamfara, wasu fusatattun matasa sun kori jami'an tsaron da aka tura masu a garin Zurmi da ke Jihar Zamfara. Matasan sun tare hanyar shigowa garin ne suna masu nuna alhinin yadda matsalar tsaro ke ƙara ƙaruwa a yankin. Sunyi ta jifar sojojin yayin da lamarin ya sanya sojojin suka tsere nan take . "Matasan sun yi ta cewar bama so, bama yi, azzalumai ne, a cikin kalaman su. Lamarin ya jefa yankin a cikin damuwa yayin da a halin yanzu babu wani jami'in…
Read More
Saudiyya ta jinkirta dawowar alhazan Jihar Katsina

Saudiyya ta jinkirta dawowar alhazan Jihar Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a katsina An samu sauyi a jadawalin jigilar dawowar alhazan Jihar Katsina daga ƙasar Saudiyya bayan da hukumomin kula da zirga-zirgar jiragen sama na Saudiyya suka yi gyara a tsarin rabon lokutan tashi da saukar jirage. Sauyin ya haifar da jinkirin fara jigilar alhazan jihar zuwa Nijeriya, lamarin da ya jawo damuwa a tsakanin wasu daga cikin mahajjatan da ke ci gaba da zaman su a birnin Makkah. Sakamakon haka, Amirul Hajj na Jihar Katsina a aikin hajjin shekarar 2026, Barista Ahmad Usman El-Marzuq, ya tabbatar wa alhazan jihar cewa an tanadi duk wasu muhimman tsare-tsare na…
Read More
Sai mun canza kiɗanmu za mu samu rawar da ta bambanta a siyasar Nijeriya – Khadija Iya

Sai mun canza kiɗanmu za mu samu rawar da ta bambanta a siyasar Nijeriya – Khadija Iya

"Mata za su iya kawar da matsalolin ƙasar nan idan suka samu dama" Daga AISHA ASAS  An daɗe ana kiran sunan mata da babbar murya kan neman na kai da gujewa zaman kashe wando, daɗaɗen jan kunne ne da ya fi gyemu tsufa, sai dai har yau wasu matan masu kunnen ƙashi sun sanya ƙafa sun shure wannan shawara ta gyara kayanka, duk da taurin kai na waɗannan mata, bai hana wasu jajirtattun mata ƙara tuna masu ba, kasancewar an ce hannunka ba ya ruɓewa ka yanke ka yar. Hajiya Khadija Iya Abdullahi na ɗaya daga cikin mata masu kishin…
Read More
Kotu ta haramta biliyan N110 na alawus da siyan motocin ‘yan Majalisar Dokokin Ƙasa

Kotu ta haramta biliyan N110 na alawus da siyan motocin ‘yan Majalisar Dokokin Ƙasa

Babbar Kotun Tarayya da ke Legas, ta ayyana kashe Naira biliyan 110 da Majalisar Dokokin Ƙasa ta yi wajen sayen motoci da kuma biyan alawus ga sabbin ‘yan majalisa a matsayin abin da ya saɓa wa doka. A hukuncin da Mai Shari’a Yellim Bogoro ta yanke, kotun ta ce kashe Naira biliyan 40 wajen sayen motoci 465 ga ‘yan majalisa da kuma Naira biliyan 70 a matsayin tallafin alawus ga sabbin mambobin majalisar ya karya dokokin saye da sayarwa na gwamnati, kundin tsarin mulki da kuma amanar da jama’a suka ɗora wa masu mulki. Shari’ar dai ƙungiyar kare haƙƙin tattalin…
Read More
Hukumar KSCHMA za ta tallafa wa ‘yan Kannywood marasa lafiya a Kano – MOPPAN

Hukumar KSCHMA za ta tallafa wa ‘yan Kannywood marasa lafiya a Kano – MOPPAN

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Hukumar Kula da Harkokin Bada Tallafin Lafiya ta Jihar Kano (KSCHMA) ta ci alwashin tallafa wa wasu daga cikin jaruman masana'antar Kannywood da ke fama da rashin lafiya na musamman, a wani yunƙuri na kula da lamuransu. Babbar Sakatariyar KSCHMA, Hajiya Rahina ta bayyana haka a wani taro da ya haɗa da wakilan Kannywood, hukumar tace finafinai ta jihar da wasu ɓangarori a ofishinta. A wata sanarwa da Shugaban Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Ƙasa (MOPPAN), Shehu Hassan Kano ya fitar a ranar Juma'a, ya ce an yi haka ne bisa la'akari da taimako…
Read More
An yi kira ga attajiran Katsina su yi koyi da Lado Ɗanmarke wajen tallafa wa ilimi

An yi kira ga attajiran Katsina su yi koyi da Lado Ɗanmarke wajen tallafa wa ilimi

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Ɗaliban manyan makarantun Jihar Katsina da na wasu a jihohin Kano da Kaduna sun yi kira ga attajirai da manyan kamfanoni da su yi koyi da Sanata Yakubu Lado Danmarke wajen tallafa wa ilimi a Jihar Katsina. Sanata Ɗanmarke ya kafa gidauniyar ta tallafin karatu da ta daɗe yana tallafa wa karatun ɗaliban Jihar Katsina masu karatu a manyan makarantu da jami'o'in ƙasar nan. Ya zuwa yanzu ɗalibai 31,711 suka ci gajiyar fiye da Naira miliyan 700 a matsayin tallafin karatu a manyan makarantu da suka haɗa da ABU Zaria,BUK Kano,UMYUK Katsina, FCE Kano,FCE Zaria,UDUS…
Read More