ukarofi

12553 Posts
Dan ga-ni-kashe-nin Arsenal ya mutu yayin kallon wasan ƙarshe na gasar Zakarun Turai a Anambara

Dan ga-ni-kashe-nin Arsenal ya mutu yayin kallon wasan ƙarshe na gasar Zakarun Turai a Anambara

An gudanar da jana’izar wani ɗan Nijeriya kuma babban masoyin ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Arsenal, bayan da rahotanni suka bayyana cewa ya rasu yayin da yake kallon wasan ƙarshe na Gasar Zakarun Turai ta UEFA tsakanin Arsenal da Paris Saint-Germain (PSG). Marigayin mai suna Chibuzor Nzediegwu, ɗan garin Uga da ke ƙaramar Hukumar Aguata a Jihar Anambra, an ce ya faɗi sumamme ne yayin da wasan ke gudana bayan PSG ta farke ƙwallon da Arsenal ta ci, lamarin da ya ƙara zafafa fafatawar tare da matsa lamba ga magoya bayan Arsenal. Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya faru ne a…
Read More
Ya shirya jana’izarsa yana raye domin gane masu ƙaunarsa

Ya shirya jana’izarsa yana raye domin gane masu ƙaunarsa

Wani lamari mai ban mamaki ya faru a ƙasar Indiya bayan wani tsohon jami'in soji mai ritaya ya shirya jana'izarsa alhali yana raye, domin ya gano mutanen da za su halarci jana'izarsa idan ya mutu.  Rahotanni sun bayyana cewa mutumin mai shekaru 74, mai suna Mohan Lal, ya shirya dukkan al'adun jana'iza a ƙauyensu da ke jihar Bihar. An gudanar da addu'o'i, taron makoki da sauran shirye-shiryen jana'iza kamar yadda ake yi ga mamaci na gaske.  Daruruwan mutane sun halarci taron ba tare da sun san cewa wanda ake yi wa jana'izar yana raye ba. Wasu daga cikin mahalarta taron…
Read More
Yadda ƙarancin kuɗin Babban Masallacin Ilorin ke jan hankalin duniya

Yadda ƙarancin kuɗin Babban Masallacin Ilorin ke jan hankalin duniya

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Yayin da Babban Masallacin Juma’a ta birnin Ilorin mai darajar miliyoyin Naira ke ci gaba da zama ɗaya daga cikin wuraren da suka fi jan hankalin masu yawon buɗe ido daga sassa daban-daban na duniya, batun yadda za a ci gaba da kula da wannan gagarumin gini ya fara zama abin damuwa ga masu ruwa da tsaki. A cikin makonni biyu da suka gabata, shugabannin da ke kula da masallacin sun bayyana damuwarsu kan ƙarancin kuɗaɗen da ake samu domin kula da ginin, wanda ake kallon sa a matsayin ɗaya daga cikin mafiya kyau a Nijeriya…
Read More
Yadda tsadar haya ke tilasta dubban ma’aikatan Legas koma wa yankin Ogun

Yadda tsadar haya ke tilasta dubban ma’aikatan Legas koma wa yankin Ogun

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Matsalar tsadar rayuwa da ke ƙara tsananta a Nijeriya ta fara sauya tsarin zaman jama'a a Jihar Legas, inda dubban mazauna birnin ke ci gaba da barin tsakiyar gari zuwa unguwanni marasa tsada da kuma garuruwan da ke kewaye da Legas domin samun gidajen haya masu sauƙin biya. Rahotanni sun nuna cewa hauhawar farashin kayayyaki, tashin kuɗin sufuri da kuma ƙarin kuɗin abinci sun jefa iyalai da dama cikin mawuyacin hali, lamarin da ya sa samun gida mai kyau a Legas ya zama tamkar abin alatu ga masu ƙarami da matsakaicin ƙarfi. Masana harkokin gidaje sun…
Read More
CBN ya ƙara wa’adin aiwatar da tsarin bibiyar POS zuwa Agustan 2026

CBN ya ƙara wa’adin aiwatar da tsarin bibiyar POS zuwa Agustan 2026

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya sanar da ƙara wa’adin fara aiwatar da dokar da ta wajabta sanya tsarin tantance wurin aiki (Geo-Fencing) ga na’urorin biyan kuɗi na POS zuwa 1 ga Agusta, 2026. Matakin, wanda bankin ya bayyana a wata sanarwa mai ɗauke da kwanan watan 29 ga Mayu, 2026, na da nufin bai wa cibiyoyin kuɗi da masu samar da ayyukan biyan kuɗi ƙarin lokaci domin kammala shirye-shiryen da suka dace da sabon tsarin dokokin da aka shimfiɗa. Sanarwar ta samu sa hannun Daraktar Sashen Kula da Tsarin Biyan Kuɗi na CBN, Dakta Rakiya Yusuf,…
Read More
Cire tallafin mai ne ya fara daidaita tattalin arzikin Nijeriya – CPPE

Cire tallafin mai ne ya fara daidaita tattalin arzikin Nijeriya – CPPE

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Cibiyar Bunƙasa Masana’antu Masu Zaman Kansu (CPPE) ta bayyana cewa cire tallafin man fetur da kuma haɗa tsarin farashin musayar kuɗaɗen ƙasashen waje su ne manyan sauye-sauyen tattalin arziki da suka taka muhimmiyar rawa wajen farfaɗo da tattalin arzikin Nijeriya a ƙarƙashin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu. A cikin wata sanarwa mai taken “Shekaru Uku Na Gwamnatin Tinubu: Daga Daidaita Tattalin Arziki Zuwa Wadata Ga Kowa”, Darakta kuma Babban Jami’in Gudanarwa na CPPE, Muda Yusuf, ya ce waɗannan tsare-tsare sun taimaka wajen fitar da tattalin arzikin ƙasar daga mawuyacin halin rashin daidaito tare da shimfiɗa harsashin…
Read More
Kiwo: Gwamnatin Tarayya za ta tallafa wa mata da matasa 37,000

Kiwo: Gwamnatin Tarayya za ta tallafa wa mata da matasa 37,000

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta bayyana shirinta na ƙarfafa mata da matasa 37,000 ta hanyar wani sabon shiri a ɓangaren kiwo, domin bunƙasa masana'antar madara ta ƙasa da kuma ƙara yawan samar da madara a cikin gida. Ministan Raya Harkokin Dabbobi, Alhaji Idi Mukhtar Maiha, ne ya bayyana hakan yayin taron manema labarai na Ranar Madara ta Duniya ta 2026 da aka gudanar bayan wani gangamin wayar da kai a Abuja. Ministan, wanda Babban Mataimakinsa na Musamman, Farfesa Eustace Iyayi ya wakilta, ya ce gwamnati na ƙara ƙarfafa manufofin da ke bai wa mata dama tare da…
Read More
Rasuwar Tauraruwa Wasila ta kawo jimami da muhawara kan rayuwar aurenta da Jarumi Ciroma

Rasuwar Tauraruwa Wasila ta kawo jimami da muhawara kan rayuwar aurenta da Jarumi Ciroma

Daga AISHA ASAS  Masu hikima kan ce, “Allah Ya raba mu da ranar yabo.” Ba wai yabo ba ne ake gudu, illa dai saboda galibi ranar da mutum ya fi samun yabo ita ce ranar da ya riga ya bar duniya ko kuma ya bar wajen da maganar tasa ta taso. A lokacin da mutum yake raye, mutane kan yi saurin ganin kuskurensa, su yi masa hukunci, su zarge shi, ko ma su ɗora masa laifukan da ba a tabbatar da su ba. Amma da zarar mutuwa ta auku, zuciyoyi kan fara narkewa, harsuna su fara sassautawa, mutane kuma su…
Read More
An buƙaci gwamnati ta tallafa wa fannin kiɗa don bunƙasa tattalin arziki

An buƙaci gwamnati ta tallafa wa fannin kiɗa don bunƙasa tattalin arziki

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD An buƙaci Gwamnatin Tarayyar Nijeriya da ta ƙara zuba jari a fannin ƙirƙire-ƙirƙire da fasaha irin na kaɗe-kaɗe, domin ta iya bunƙasa tattalin arzikin ƙasar tare da samar da damar haɓaka baiwar matasa da suke tasowa. Daraktan Kiɗa na Rundunar Sojin Sama ta Nijeriya (NAF), Kyaftin na Runduna Oludare Ayanbode, ne ya yi wannan kira yayin da yake ɗaya daga cikin alƙalan da suka jagoranci gasar kiɗa ta ƙasa a Abuja karo na takwas, wato Abuja National Music Competition (ANMC). A cewarsa, har yanzu akwai buƙatar gwamnati ta ƙara ƙoƙari wajen gano baiwar yara tun suna…
Read More
Nijeriya na da damar mamaye kasuwar manja a duniya nan da 2050 – NPPAN

Nijeriya na da damar mamaye kasuwar manja a duniya nan da 2050 – NPPAN

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Kungiyar Masu Sarrafa Kwakwan Manja ta ƙasa (NPPAN), ta bayyana cewa Nijeriya na da burin kaiwa ga cikakkiyar wadatar manja tare da samun gagarumar kason kasuwar duniya nan da shekarar 2050. Shugaban ƙungiyar na ƙasa, Alphonsus Inyang, ya bayyana hakan ne a wata hira da kamfanin dillancin labarai na ƙasa (NANS) a gefen taron tantance Tsarin Bunƙasa Noman Kwakwan Manja na ƙasa da aka gudanar a Abuja. Ya ce wannan buri zai tabbata ne ta hanyar aiwatar da Tsarin Bunƙasa Noman Kwakwan Manja na ƙasa yadda ya kamata, wanda zai taimaka wajen ƙara yawan amfanin da…
Read More