07
Jun
Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Shekaru uku bayan gwamnatin tarayya ta yi alƙawarin samar da asusun tallafi na Naira biliyan 200 domin rage tasirin sauye-sauyen tattalin arziki ga masana’antu da ƙananan ’yan kasuwa, masu ruwa da tsaki sun bayyana cewa har yanzu yawancin waɗanda aka yi niyyar tallafawa ba su amfana da shirin ba. A lokaci guda kuma, miliyoyin ƙananan kasuwanci sun durƙushe tare da rufe ƙofofinsu. Kungiyar Masu ƙananan Kasuwanci ta Nijeriya (ASBON) ta ce kusan ƙananan kasuwanci miliyan biyu ne suka rufe tsakanin shekarun farko uku na gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, sakamakon cire tallafin man fetur, sauye-sauyen tsarin…
