ukarofi

12553 Posts
Rancen bankunan sana’o’i ya haura tiriliyan N4.43 a 2025

Rancen bankunan sana’o’i ya haura tiriliyan N4.43 a 2025

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Bankunan ba da rance na bankunan ƙanana da matsakaitan sana’o’i (MFB) a Nijeriya sun samu gagarumar nasara a shekarar 2025, inda jimillar kuɗaɗen rancen da suka bayar ta ƙaru da kashi 92.8 cikin 100, daga Naira tiriliyan 2.30 zuwa Naira tiriliyan 4.43 a ƙarshen shekarar. Sabbin alƙaluman da ke cikin Rahoton ƙididdiga na Babban Bankin Nieriya (CBN) sun nuna cewa ƙaruwar buƙatar rance daga ƙananan da matsakaitan 'yan kasuwa, masu sana'o'in hannu da masu ƙaramin ƙarfi ta fuskar kuɗi ce ta haifar da wannan ci gaba. Rahoton ya bayyana cewa adadin rancen da bankunan suka bayar…
Read More
Kasuwar hannayen jari ta ƙara Naira tiriliyan 131.66 a shekaru uku na mulkin Tinubu

Kasuwar hannayen jari ta ƙara Naira tiriliyan 131.66 a shekaru uku na mulkin Tinubu

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Kasuwar hannayen jari ta Nijeriya ta samu gagarumin ci gaba a cikin shekaru uku na gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, inda darajar kasuwar ta ƙaru da sama da Naira tiriliyan 131, lamarin da ya sanya wannan lokaci ya zama ɗaya daga cikin mafi nasara a tarihin kasuwar. Bayanan da aka fitar sun nuna cewa darajar kamfanonin da aka jera a Kasuwar Musayar Hannayen Jari ta Nijeriya (NGɗ) ta tashi daga Naira tiriliyan 28.845 a watan Mayun 2023 zuwa Naira tiriliyan 160.509 a ranar 29 ga Mayun 2026. Wannan na nufin kasuwar ta samu ƙarin Naira tiriliyan…
Read More
Duk da haramcin NAFDAC, barasar leda ta ci gaba da mamaye kasuwanni

Duk da haramcin NAFDAC, barasar leda ta ci gaba da mamaye kasuwanni

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Watanni bakwai bayan da Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta ƙasa (NAFDAC) ta fara aiwatar da haramcin sayar da barasar leda da kuma kwalaben roba masu ƙasa da mililita 200, har yanzu ana samun ci gaba da sayar da kayayyakin a cikin kasuwanni da kan tituna a sassa daban-daban na Nijeriya. Binciken da wata jarida ta gudanar ya nuna cewa maimakon kayayyakin su ɓace daga kasuwa, har yanzu suna yawo a wurare da dama, yayin da kuma farashinsu ya yi tashin gwauron zabo tun bayan fara aiwatar da dokar. A halin yanzu, barasar leda…
Read More
Ina goyon bayan Tinubu ne don ba na fatan Nijeriya ta inganta – Keji Giwa

Ina goyon bayan Tinubu ne don ba na fatan Nijeriya ta inganta – Keji Giwa

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Wani fitaccen attajirin ɗan kasuwa a Nijeriya, Keji Giwa, ya jawo cece-kuce a kafafen sada zumunta bayan wasu kalamai masu jan hankali da ya yi kan siyasa, kasuwanci da shugabanci a ƙasar. A cikin wani bidiyo da ya bazu a shafukan sada zumunta, Giwa ya kare goyon bayan da yake bai wa Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, yana mai cewa siyasa na taka muhimmiyar rawa wajen nasarar kasuwanci a Nijeriya. Attajirin, wanda ya yi fice a harkar gine-ginen gidaje da filaye, ya bayyana cewa duk ɗan kasuwar da bai fahimci alaƙar da ke tsakanin siyasa da…
Read More
Cardoso ya sauya wa dukkan mataimakan gwamnan CBN sassa

Cardoso ya sauya wa dukkan mataimakan gwamnan CBN sassa

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya sanar da sauya wa dukkan mataimakan gwamnan bankin guda huɗu wuraren aikinsu, a wani mataki da ke cikin sauye-sauyen da Gwamnan Babban Bankin Nijeriya, Olayemi Cardoso, ke aiwatarwa domin ƙarfafa sa ido kan harkokin kuɗi da inganta gudanar da manufofin tattalin arziki. Sabon tsarin, wanda ya fara aiki daga ranar 1 ga Yunin 2026, ya haɗa da sake rabon jagorancin manyan sassan bankin da suka haɗa da sashen manufofin tattalin arziki, ayyuka, hidimomin gudanarwa da kuma sashen tabbatar da daidaiton tsarin kuɗi. A wata sanarwa da bankin ya wallafa a shafinsa…
Read More
Cire harajin kashi 15 kan motocin tokunbo zai sauƙaƙa wa ’yan Nijeriya – Farinto

Cire harajin kashi 15 kan motocin tokunbo zai sauƙaƙa wa ’yan Nijeriya – Farinto

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Tsohon Muƙaddashin Shugaban ƙungiyar Dillalan Kwastom Masu Lasisi ta Nijeriya (ANLCA), Dakta Kayode Farinto, ya buƙaci Gwamnatin Tarayya da ta soke harajin ƙarin kashi 15 da ake karɓa kan motocin da aka shigo da su daga ƙasashen waje (Tokunbo), yana mai cewa wannan tsari yana ƙara wa ’yan Nijeriya nauyin rayuwa a daidai lokacin da ake fama da matsin tattalin arziki. Farinto ya bayyana hakan ne yayin da yake tsokaci kan tasirin sauye-sauyen tattalin arzikin da Gwamnatin Tarayya ke aiwatarwa. Ya ce, duk da cewa manufofin gwamnati sun taimaka wajen ƙara kuɗaɗen shiga da kuma inganta…
Read More
Borno: Yadda annobar Kwalara ta kashe mutum 40, fiye da 3,000 ke asibiti

Borno: Yadda annobar Kwalara ta kashe mutum 40, fiye da 3,000 ke asibiti

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Cutar Kwalara ta yi ajalin aƙalla muutm 40 a yayin da wasu sama da mutum 3,000 suke fama da ita a cikin wata guda a wasu kananan hukumomi bakwai a Jihar Bonor. Manhaja ta ruwaito cewa al’ummomi 139 ne aka samu bullar cutar a kananan hukumomin Borno, Jere, Mafa, Konduga, Monguno, Ngala da Magumeri daga ranar 1 zuwa 28 ga watan Mayu, 2026. A ranar Asabar, 30 ga watan Mayun ne dai Gwamnatin Jihar Borno ta sanar cewa cutar kwalara ta kashe mutum 37, a yayin da wasu 3,000 ke ci gaba da fama…
Read More
Hukumar REMASAB ta ƙaryata zargin rashin biyan ’yan shara albashinsu a Kano 

Hukumar REMASAB ta ƙaryata zargin rashin biyan ’yan shara albashinsu a Kano 

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Hukumar Kula da tsaftar muhalli da kwashe shara ta Jihar Kano (REMASAB) ta ƙaryata rahotannin da ke ikirarin cewa ba ta biyan ma’aikatanta albashi, tare da zargin cewa wasu ma’aikatan na karɓar Naira 10,000 kacal a kowane wata. A cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, Abubakar Ahmad, ya fitar ranar 2 ga Yuni, 2026, REMASAB ta ce zarge-zargen da aka wallafa a wani flyer na shafin Facebook na gidan rediyon Dala FM ƙarya ne kuma ba su da alaƙa da ainihin halin da ake ciki a hukumar. Hukumar ta bayyana…
Read More
Tinubu ya ƙaddamar da manyan ayyukan CNG a faɗin Nijeriya

Tinubu ya ƙaddamar da manyan ayyukan CNG a faɗin Nijeriya

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya ƙaddamar da manyan ayyukan samar da ababen more rayuwa na iskar gas ta CNG guda huɗu a jihohin Legas, Abuja da Imo, a wani mataki da Gwamnatin Tarayya ta ce zai taimaka wajen rage kuɗin sufuri da kuma bunƙasa amfani da makamashi mai tsafta a ƙasar nan. Ayyukan, waɗanda aka aiwatar ta hannun Asusun Bunƙasa Ababen More Rayuwa na Iskar Gas (MDGIF), na daga cikin matakan da gwamnatin tarayya ke ɗauka bayan cire tallafin man fetur, domin rage nauyin da ke kan jama'a tare da ƙarfafa amfani da iskar gas…
Read More
Muna ƙoƙarin taimaka wa sanatocin da suka faɗi zaɓen fidda gwani su samu tikitin takara – Akpabio

Muna ƙoƙarin taimaka wa sanatocin da suka faɗi zaɓen fidda gwani su samu tikitin takara – Akpabio

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya bayyana cewa Majalisar Dattawa na kokarin ganin an samar da mafita ga wasu sanatocin da suka kasa samun tikitin tsayawa takara a zaɓukan fidda gwani domin babban zaɓen shekarar 2027. Jaridar Blueprint Manhaja ta ruwaito cewa sama da sanatoci 40 daga jam’iyyun APC, PDP, NDC da sauran jam’iyyu sun rasa tikitin komawa takara bayan kammala zaɓukan fidda gwani. Da yake jawabi bayan dawowar Majalisar Dattawa daga hutun makonni huɗu, Akpabio ya taya waɗanda suka samu tikitin takara murna, sannan ya nuna damuwa kan yawan sanatocin da suka…
Read More