ukarofi

12553 Posts
Zargin zambar biliyan N2.8: Kotu ta jinkirta yanke hukunci kan buƙatar dakatar da shari’ar Hadi Sirika

Zargin zambar biliyan N2.8: Kotu ta jinkirta yanke hukunci kan buƙatar dakatar da shari’ar Hadi Sirika

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Wata Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Maitama, Abuja, ta jinkirta yanke hukunci kan bukatar da aka gabatar na dakatar da shari’ar tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, Hadi Sirika, da ake zargi da hannu a damfarar kwangiloli ta kusan Naira biliyan 2.83. Mai shari’a S.C. Oriji ne ya bayyana hakan yayin zaman kotu ranar Talata, a shari’ar da Hukumar Yaƙi da Masu Yi wa Tattalin Arzikin ƙasa Ta’annati (EFCC) ta shigar kan Sirika, diyarsa Fatima Hadi Sirika, da surukinsa Hamma Jalal Sule. EFCC na tuhumar wadanda ake kara da laifuka shida da suka…
Read More
Gwamnatin Tarayya ta soke hutun wata uku kafin ritaya ga ma’aikatan gwamnati

Gwamnatin Tarayya ta soke hutun wata uku kafin ritaya ga ma’aikatan gwamnati

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Gwamnatin Tarayya ta umarci dukkan Ma’aikatu, Hukumomi da Cibiyoyin Gwamnati (MDAs) da su daina aiwatar da tsarin da ake kira hutun watanni uku kafin ritaya ga ma’aikatan gwamnati, tana mai bayyana cewa babu irin wannan tanadi a cikin Dokokin Aikin Gwamnati (Public Service Rules). Umarnin na kunshe ne cikin wata takarda da Shugabar Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya, Didi Walson-Jack, ta fitar zuwa ga ministoci, sakatarorin dindindin, shugabannin hukumomi da sauran manyan jami’an gwamnati. A cikin takardar mai taken “Ingantacciyar Fassarar Dokar Aikin Gwamnati ta 120243 Kan Shirye-shiryen Ritaya”, Walson-Jack ta bayyana cewa wasu hukumomi sun…
Read More
An kama jagoran ’yan bindiga da mataimakansa a Zamfara

An kama jagoran ’yan bindiga da mataimakansa a Zamfara

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  ’Yan sanda sun kama wani fitaccen jagoran ’yan bindiga Ali Bahago Danakulu, tare da mukarrabansa a ƙaramar Hukumar Kaura Namoda ta Jihar Zamfara. Kakakin ’yan sanda na jihar, DSP Yazid Abubakar, ya sanar cewa an bindiga ɗaya daga cikin ’yan binrigar har lahira a yayin samamen. Ya ce ’yan ta’addan da aka kama sun daɗe rundunar tana neman su, bisa zargin hannu a fashi da makami, ayyukan ’yan bindiga da sauran munanan laifuka a yankin. Waɗanda aka kama sun haɗa da Ali Bahago Danakulu na Kasuwan Daji da Hassan Dan Kure, shi ma mazaunin…
Read More
DSS ta kama mutum biyar kan sace ɗalibai 300 a Neja

DSS ta kama mutum biyar kan sace ɗalibai 300 a Neja

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Wasu mutane biyar da ake zargi da hannu a yin garkuwa da ɗalibai kimanin 300 a makarantar Katolika ta St. Mary Papiri da ke Jihar Neja, sun shiga hannu. Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta bayyana cewa ta kama mutanen ne a yayin da suke safarar wasu bindigogi kirar ƙirar AK-47 guda 15 da harsasai 1,434 a cikin wata mota a kan hanyar Kaduna zuwa Zariya. Daga cikin mutanen har da mutum biyu ’yan kasar Jamhuriyar Nijar da wani dan kungiyar Boko Haram da hukumar take nema mai suna Yusuf Mohammed wanda aka…
Read More
Mahara sun kashe ’yan yawon sallah bakwai a Sakkwato

Mahara sun kashe ’yan yawon sallah bakwai a Sakkwato

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Aƙalla mutum 17 ne, ciki har da masu yawon Sallah bakwai, suka rasa rayukansu bayan wani mummunan hari da ’yan bindiga suka kai ƙauyen Dangulbi da ke ƙaramar Hukumar Tureta ta Jihar Sakkwato. Mazauna yankin sun shaida wa Aminiya cewa maharan, waɗanda suka zo kan babura kimanin 150 ɗauke da makamai, sun mamaye kauyen da safiyar Lahadi, inda suka riƙa harbe-harbe kan mai uwa da wabi tare da kwashe kayayyaki daga shaguna. Wani mazaunin yankin da ya buƙaci a sakaya sunansa ya ce maharan sun shiga garin tsakanin ƙarfe 10 zuwa 11 na safe,…
Read More
Sojoji sun halaka ‘yan bindiga 10, sun ceto mutane 31 a Zamfara da Katsina

Sojoji sun halaka ‘yan bindiga 10, sun ceto mutane 31 a Zamfara da Katsina

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Rundunar Sojoji a ƙarƙashin Atisayen FANSAN YAMMA, ta yi nasarar ceto mutane 31 da aka yi garkuwa da su, tare da halaka ’yan ta’adda guda biyar yayin wasu atisaye a Jihar Zamfara da Katsina. Haka kuma, sun ceto mutane 31 a yankin Bagega zuwa Kawaye da ke ƙaramar Hukumar Anka ta Zamfara bayan harbin bom daga jiragen yaƙi a maɓoyar ’yan ta’addan a Dajin Bagega. Rahotanni sun bayyana cewa, waɗanda aka ceton, sun shafe tsawon makonni da dama a tsare kuma ’yan asalin ƙananan hukumomin Maga, Gummi, Zuru, Wasugu, Bukuyyum, da Anka ne da…
Read More
Amarya ta kashe uwargida kan rikicin rabon naman Sallah a Zariya

Amarya ta kashe uwargida kan rikicin rabon naman Sallah a Zariya

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna ta tabbatar da kama wata mata da ake zargi da kashe uwargidan mijinsu bayan ta soka mata wuƙa har lahira a unguwar Gwargwaje da ke Zariya. Kakakin rundunar, DSP Mansir Hassan, ya ce lamarin ya faru ne a Unguwar Madachi B da ke yankin Gwargwaje, inda ake zargin wata mata mai suna Amina ta kai wa uwargidanta, Amina Maharazu, hari da wuƙa. Ya ce bayan samun rahoton faruwar lamarin daga mai unguwa, jami’an ’yan sanda sun garzaya wurin, inda suka tarar da matar kwance cikin jini tana cikin mawuyacin…
Read More
’Yan bindiga sun sake kashe mutum 20 a ƙauyen Sakkwato

’Yan bindiga sun sake kashe mutum 20 a ƙauyen Sakkwato

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Ana fargabar cewa ’yan bindiga sun kashe aƙalla mutum 20 a wani sabon hari da suka kai ƙauyen ɗan Gulbi da ke ƙaramar Hukumar Tureta a Jihar Sakkwato. Wannan ibtila’in na zuwa ne kwanaki biyu kacal bayan wani hari makamancinsa da ya yi sanadin mutuwar mutum 17. Mazauna yankin sun ce maharan sun mamaye ƙauyen da safiyar Talata da misalin ƙarfe 8:00, inda suka riƙa harbe-harbe kan mai uwa da wabi, lamarin da ya tilasta wa jama’a tserewa domin neman mafaka. Wata majiya daga yankin ta shaida wa Aminiya cewa maharan sun shafe sa’o’i…
Read More
Boko Haram na shirin yin ‘bikin kammala karatun Alƙur’ani’ ga mata da yara sama da 100 da suka sace a Kwara

Boko Haram na shirin yin ‘bikin kammala karatun Alƙur’ani’ ga mata da yara sama da 100 da suka sace a Kwara

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Iyalan wasu mutanen da aka sace daga ƙauyen Woro da ke ƙaramar hukumar Kaiama a jihar Kwara sun bayyana cewa wasu ‘yan ta’adda da ake zargin Boko Haram ne na shirin gudanar da bikin kammala karatun Alƙur’ani ga mata da yara sama da 100 da ke hannunsu. Iyalan sun ce sun samu wannan bayanin ne ta hanyar tattaunawar waya da ‘yan ta’addan suka yi da su kwanan nan. Waɗanda aka sace ɗin an yi garkuwa da su ne watanni da suka gabata, bayan harin da ‘yan ta’adda suka kai ƙauyen Woro, inda suka kashe…
Read More
Isaac Fayose ya caccaki ɗan uwansa Ayo Fayose kan kalaman da ya yi game da sace ɗalibai a Oyo

Isaac Fayose ya caccaki ɗan uwansa Ayo Fayose kan kalaman da ya yi game da sace ɗalibai a Oyo

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Dan kasuwa kuma mai sharhi kan al’amuran yau da kullum, Isaac Fayose, ya soki ɗan’uwansa kuma tsohon gwamnan Jihar Ekiti, Ayo Fayose, kan kalaman da ya yi dangane da sace ɗalibai da malamansu a Jihar Oyo. A wata hira da ya yi a gidan talabijin ranar Talata, Ayo Fayose ya yi zargin cewa sace ɗalibai 46 da malamansu a Oyo na iya kasancewa wani shiri ne da gwamnatin jihar ta ƙulla domin kunyata Shugaba Bola Ahmed Tinubu. Tsohon gwamnan ya kuma yi tambaya kan yadda gwamnatocin jihohi ke amfani da kuɗaɗen tsaro da suke…
Read More