ukarofi

12553 Posts
NUT ta gudanar da zanga-zanga a jihohi da dama kan malamai da ɗaliban da aka sace

NUT ta gudanar da zanga-zanga a jihohi da dama kan malamai da ɗaliban da aka sace

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Kungiyar Malaman Makarantu ta Nijeriya (NUT) ta gudanar da zanga-zangar lumana a jihohi da dama na ƙasar nan domin nuna damuwa kan ci gaba da tsare malamai da ɗaliban da aka sace a Jihar Oyo. Rahotanni sun nuna cewa zanga-zangar ta biyo bayan irin wadda ƙungiyoyin farar hula suka gudanar a Ibadan, babban birnin Jihar Oyo, inda suka buƙaci a gaggauta ceto waɗanda aka yi garkuwa da su. A Ibadan, malamai sun taru a harabar ofishin Kungiyar Kwadago ta Nijeriya (NLC) da ke yankin American ƙuarter, inda shugabannin ƙungiyar suka yi musu bayani kan…
Read More
FIFA ta tabbatar da sabbin dokokin Gasar Kofin Duniya ta 2026

FIFA ta tabbatar da sabbin dokokin Gasar Kofin Duniya ta 2026

Hukumar ƙwallon ƙafa ta Duniya (FIFA) ta tabbatar da wasu sabbin dokoki da za su fara aiki a Gasar Kofin Duniya ta 2026, matakin da ake sa ran zai taimaka wajen rage ɓata lokaci, ƙara gaskiya a yanke hukunci da kuma inganta tafiyar da wasa. Daga cikin manyan sauye-sauyen da aka amince da su akwai sanya iyaka ga lokacin da ‘yan wasa za su ɗauka wajen dawo da ƙwallo cikin wasa, canje-canjen ‘yan wasa, da kuma ƙarin amfani da fasahar Bidiyon Taimaka wa Alƙali (VAR). Sabuwar dokar jefa ƙwallo daga gefe ta tanadi cewa idan ɗan wasa ya yi gangancin…
Read More
Konate ya yi bankwana da Liverpool bayan shekara biyar a Anfield

Konate ya yi bankwana da Liverpool bayan shekara biyar a Anfield

Kungiyar ƙwallon ƙafa ta Liverpool ta tabbatar da cewa ɗan wasan baya na ƙasar Faransa, Ibrahima Konate, zai raba gari da ƙungiyar a ƙarshen wannan kakar wasa bayan tattaunawar sabunta kwantiraginsa ta ci tura. Konate mai shekaru 26 a duniya, wanda ya koma Liverpool daga ƙungiyar RB Leipzig ta Jamus a shekarar 2021, bai cimma matsaya da mahukuntan ƙungiyar ba kan sabon kwantiragi. Hakan na nufin zai bar filin Anfield kyauta da zarar yarjejeniyarsa ta kare a ƙarshen watan Yuni, bayan ya shafe shekaru biyar yana taka leda a Merseyside. A cikin wata sanarwa da Liverpool ta wallafa a shafinta…
Read More
Vinicius zai iya barin Real Madrid idan ya so – Perez

Vinicius zai iya barin Real Madrid idan ya so – Perez

Shugaban ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Real Madrid, Florentino Perez, ya bayyana cewa ba zai hana tauraron ɗan wasan gaba na ƙungiyar, Vinicius Junior, barin ƙungiyar ba idan har ya yanke shawarar komawa wata ƙungiya. Kalaman na Perez sun zo ne a daidai lokacin da ake ci gaba da tattaunawa kan sabunta kwantiragin ɗan wasan na Brazil, tattaunawar da har yanzu ba a kai ga cimma matsaya ba. Da yake magana kan raɗe-raɗin da ke yawo game da makomar Vinicius, shugaban na Real Madrid ya bayyana cewa yana da burin ganin ɗan wasan ya ci gaba da zama a ƙungiyar har…
Read More
Rikicin shugabancin Real Madrid: Mahaifin Haaland ya ƙ aryata iƙirarin ɗan takara kan sayen ɗansa

Rikicin shugabancin Real Madrid: Mahaifin Haaland ya ƙ aryata iƙirarin ɗan takara kan sayen ɗansa

Zaɓen neman shugabancin ƙungiyar Real Madrid ya rikiɗe zuwa cece-kuce mai zafi bayan da ɗan takarar shugabancin kulab ɗin, Enrique Riquelme, ya yi iƙirarin cewa, ya ƙulla yarjejeniyar sayen taurarin ƙwallon ƙafa Erling Haaland da Rodri idan ya lashe zaɓen. Riquelme, ɗan kasuwa mai harkar makamashi, ya bayyana hakan ne a shirin talabijin na El Hormiguero, inda ya nuna rigar Real Madrid mai ɗauke da sunan Haaland, yana mai cewa ɗan wasan yana da sha’awar komawa Santiago Bernabeu. Sai dai wannan iƙirari ya jawo gaggawar martani daga ɓangaren ɗan wasan, inda wakilinsa Rafaela Pimenta tare da mahaifinsa Alfie Haaland suka…
Read More
An fara raba magunguna a asibitocin Bindawa da gwamnatin Katsina ta samar

An fara raba magunguna a asibitocin Bindawa da gwamnatin Katsina ta samar

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a katsina Shugaban ƙaramar hukumar Bindawa, Hon. Badaru Musa Giremawa, ya ƙaddamar da rabon magungunan da gwamnatin jihar ta samar domin asibitocin ƙaramar hukumar Bindawa, a wani mataki na inganta harkokin kiwon lafiya da tabbatar da samun ingantattun magunguna ga al'umma. Jami'in yaɗa labarai na ƙaramar hukumar Abubakar Hamisu Doro wanda ya fitar da sanarwa ya ce shugaban,ya hori malaman kiwon lafiya da su guji karkatar da magungunan da kawo domin al'ummar inda yayi gargaɗin cewa duk wanda aka samu da hannu wajen satar magungunan to ya kuka da kansa. Gwamnatin katsina ta samar tare da rarraba…
Read More
NCDC na cigaba da shirin kariya daga Ebola yayin da barazanar cutar ke ci gaba da ƙaruwa

NCDC na cigaba da shirin kariya daga Ebola yayin da barazanar cutar ke ci gaba da ƙaruwa

Daga USMAN KAROFI Hukumar yaƙi da cututtuka masu yaɗuwa Najeriya (NCDC) ta bayyana cewa har yanzu akwai babban haɗarin shigowar nau’in cutar Ebola na Bundibugyo zuwa Najeriya, sakamakon ci gaba da yaɗuwar cutar a wasu ƙasashen Gabashin Afirka, yawaitar zirga-zirgar jama’a tsakanin ƙasashe da kuma iyakokin da ba su da cikakken tsaro. Darakta janar na NCDC, Dakta Jide Idris, ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai a Legas, inda ya ce hukumar ta gudanar da wani nazari na musamman domin tantance haɗarin da Najeriya ke fuskanta. Ya ce duk da cewa ba a samu wani tabbataccen mutum da…
Read More
Rashin lantarki ya sa ɗalibai rubuta WAEC da cocilan

Rashin lantarki ya sa ɗalibai rubuta WAEC da cocilan

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Jarrabawar ɗalibai masu kammala karatun sakandare ta WASSCE ta fuskanci tsaiko a cibiyoyi da dama a jihohin Kaduna, Katisna, Delta, Imo, Oyo, Legas, Ogun da Osun, inda aka tilasta musu rubutawa acikin duhu sakamakon jinkirin kawo kayayyakin jarrabawar a wuraren da aka ɗauke wutar lantarki. Rahotanni sun bayyana cewa, al'amarin, wanda ya ɗauki tsawon kwanaki, ya jefa ɗalibai da dama cikin mawuyacin hali a cibiyoyin na sa'o'i, inda a wasu lokutan ake tilasta musu rubutawa a yanayin lantarki mara inganci. Waɗansu rahotanni sun nuna cewa an fara fuskantar ƙalubalen ne tun a ranar Litinin,…
Read More
Ranar muhalli: JEI ta yi kira ga ɗaukar matakan gaggawa kan sauyin yanayi

Ranar muhalli: JEI ta yi kira ga ɗaukar matakan gaggawa kan sauyin yanayi

Daga ABUBAKAR A BOLARI GOMBE Ƙungiyar Jewel Environmental Initiative (JEI) ta buƙaci gwamnatoci da al’ummomi a faɗin Najeriya da su ƙara ƙaimi wajen ɗaukar matakan kare muhalli da daƙile matsalolin da sauyin yanayi ke haifarwa. Kiran ya fito ne daga babban daraktan ƙungiyar, Mista Ismail Bima, yayin da ake gudanar da bukukuwan ranar muhalli ta duniya ta 2026 a Gombe ranar Juma’a. Bima ya bayyana cewa taken ranar ta bana, “Wahayi daga yanayi: Domin sauyin yanayi, saboda makomarmu,” na nuna muhimmancin amfani da hanyoyin da suka dace da muhalli wajen tinkarar ƙalubalen sauyin yanayi da kuma tabbatar da ci gaba…
Read More
Gwamnatin Tarayya na shirin gaggauta samar da gidaje yayin da Minista Darma ya ziyarci Kano

Gwamnatin Tarayya na shirin gaggauta samar da gidaje yayin da Minista Darma ya ziyarci Kano

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Gwamnatin Tarayya ta sake jaddada aniyarta na hanzarta samar da gidaje ga al’ummar Nijeriya, yayin da Ministan Gidaje da Raya Birane, Injiniya Muttagha Rabe Darma, ya kai ziyarar duba aikin Kano Renewed Hope City Housing Project, inda ya bayyana aikin a matsayin abin koyi wajen samar da gidaje masu araha ta hanyar haɗin gwiwar gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu. Darma ya ce aikin na nuna yadda kyakkyawar haɗin gwiwa tsakanin gwamnati da masu zuba jari masu zaman kansu zai taimaka wajen rage gibin gidaje da ake fuskanta a Nijeriya, tare da bunƙasa harkokin…
Read More