26
May
Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Wata mummunar gobara da ta tashi a kasuwar Katsina ta kawo asarar shaguna 10 tare da asarar ɗimbin dukiya. Ana zargin inverter mai amfani da hasken rana da haddasa gobara a babbar kasuwar Katsina Rahotanni sun bayyana cewar gobarar ta tashi ne da misalin ƙarfe 6:35 na safiya, inda hukumar kashe gobara ta jihar Katsina ta ce ta samu kiran gaggawa kafin jami’anta su isa wurin domin shawo kan lamarin. A cewar hukumar, gobarar ta shafi shaguna 10 da suka haɗa da na kayan masarufi, abubuwan sha, labule da yadudduka. Sai dai jami’an kashe gobara…
