23
May
Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Yayin da farashin shanu da nama ke ci gaba da tashi a faɗin Nijeriya sakamakon matsin tattalin arziki da hauhawar farashi, iyalai masu ƙaramin ƙarfi na ƙara cire nama daga cikin abincinsu na yau da kullum, lamarin da masana ke gargaɗin cewa na iya ƙara jefa miliyoyin mutane cikin matsalar rashin abinci mai gina jiki. Rahoton da jaridar PUNCH Healthwise ta wallafa ya nuna yadda talauci da raguwar ƙarfin saye suka sa iyalai da dama ba sa iya sayen nama, kifi, kaji, talo-talo ko sauran abincin da ke ɗauke da sinadarin furotin. A kasuwar Kara da…
