24
May
Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Hukumar Sadarwa ta Nijeriya (NCC) ta bayyana cewa kamfanonin sadarwa sun zuba sama da dala biliyan ɗaya wajen faɗaɗa hanyoyin sadarwa da inganta ayyukan intanet a faɗin ƙasar nan cikin shekarar 2025 kaɗai. Shugaban Hukumar NCC kuma Babban Daraktan Gudanarwa, Dakta Aminu Maida, ne ya bayyana hakan a birnin Legas yayin wani taro da Hukumar NCC ta shirya tare da Cibiyar Horas da Alƙalai ta ƙasa domin horas da alƙalai kan harkokin sadarwa da fasahar zamani. A cewarsa, kamfanonin sadarwar sun ƙara dubban sabbin cibiyoyin sadarwa domin faɗaɗa kewayon intanet da kuma inganta ingancin ayyukan sadarwa…
