07
Oct
Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Jam'iyyar National Democratic Congress (NDC), reshen Jihar Zamfara, ta yi Allah wadai da harin da aka kai a kwanan nan a garin Bindin da ke ƙaramar hukumar Maru a Jihar Zamfara, wanda ya yi sanadiyyar kashe jami'an tsaro da fararen hula da kuma ɓarnata dukiyoyi. Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da aka fitar, wadda sakataren yaɗa labarai na jam'iyyar, Kassim Almustapha Kayatawa ya sanya wa hannu, kuma aka baiwa manema labarai a Gusau yau Laraba. Jam'iyyar ƙarƙashin jagorancin Alhaji Surajo Garba Maikatako, ta miƙa saƙon ta'aziyya ga al'ummar Bindin, tana addu'ar Allah…
